Muhimman abubuwa biyar da suka faru a ganawar Trump da Putin a Alaska

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Laura Gozzi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Taron wanda aka daɗe ana hanƙoro tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin an yi tunanin shi ne zai buɗe kofar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine.
Amma ganin yadda ta kaya, sai ya zama taron shugabannin biyu na kusan awa biyu ya bar baya da ƙura ne maimakon samar da maslaha da amsar tambayoyin da jama'a ke yi.
Wannan ya sa muka kalato wasu muhimman abubuwa biyar da suka wakana a taron na Alaska.
Irin tarbar da Putin ya samu
A lokacin da Vladimir Putin ya isa wajen taron a ranar Juma'a, ya riski shugaban Amurka Donald Trump yana jiransa, sannan an shimfiɗa masa jar shimfiɗa ta girmama a filin jirgin sama na Elmendorf-Richardson.
Da Putin ya fito, sai Trump ya fara tafi, sannan suka gaisa cikin girmamawa, kafin suka yi murmushi.
Wannan lamari ne babba ga Putin wanda shugabannin ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa takunkumai tun bayan da ƙasarsa ta ƙaddamar da yaƙi a Ukraine a 2022. Tun lokacin sai ya zama tafiye-tafiyensa sun fi yawa zuwa ƙasashen da ke ƙawance da Rasha, musamman Koriya ta Arewa da Belarus.
Wannan ya sa wasu suke ganin Putin ya samu nasara, musamman ganin kasancewarsa wanda ƙasashen yamma a baya suka tsana, amma a yanzu har ya samu irin wannan tarbar ta girmamawa a cikin Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Ganawar Putin da baƙin ƴanjarida
A tsawon shekara da 25 da ya yi yana mulki, Putin ya kasance mai ƙarfin iko a kan kafofin sadarwa, inda yake take haƙƙin ƴanjarida da kuma musanya labarai da farfagandar da yake so. A Rasha bai cika fuskantar tambayoyin da bai yi tsammani ba daga ƴanjarida.
Amma isarsa Alaska ke da wuya, wani ɗanjarida ya jefa masa tambayar, "za ka daina kashe fararen hula?" ko da kuwa bai ji daɗin tambayar ba, bai nuna alama ba.
Haka kuma ƴanjarida sun yi ta jefa masa tambayoyi, ciki har ko a shirye yake ya gana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da sauran su.
Gaggawar gama ganawar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƴanjarida na duniya sun taru domin yadda ganawar ta kaya, amma sai shugabannin biyu suka yi jawabi ba tare da amsa tambayoyi ba.
Putin ne ya fara magana, inda ya yaba da irin tarbar da aka masa ta girmamawa, sannan ya bayyana yadda a baya yankin Alaska ya kasance a ƙarƙashin Rasha.
A lokacin da Putin yake magana, Trump ya yi shiru yana sauraro, inda sai daga baya ne ya ambaci abin da ke faruwa a Ukraine, wanda maganar ce asalin maƙasudin taron. Da kuma ya yi maganar, sai ya ce duk da an fara tattaunawa kan tsagaita wuta, "dole sai an warware asalin ƙullin da ya jawo rikicin kafin a samu maslaha."
Wannan maganar za ta jefa firgici a Ukraine da ma masu bibiyar lamarin, domin tun farkon yaƙin ne Putin yake bayyana wasu buruku da yake so dole ya cika kafin a dakata da yaƙin.
Daga ciki akwai ƙwace yankunan Crimea da Donetsk da Luhansk da Zaporizhzhia da Kherson waɗanda duka na Ukraine ne, domin su koma Rasha da sauran su.
Wannan ya sa ake ganin lallai maganar tsagaita wuta da sauran magana a gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Abubuwan da ba a faɗa ba
Ganin muhimmancin taron, sai aka yi mamakin yadda da Trump ya fara jawabi, bai ma ambaci Ukraine ba, ko kuma batun tsagaita wuta.
Inda ya ɗan yi kusa da batun shi ne inda ya ce, "ana kashe mutum dubu biyar zuwa shida ko bakwai a duk mako," sannan ya ce shi ma Putin na so a kawo ƙarshen zubar da jinin.
Amma bai bayyana wasu bayanai da za su nuna matakan da za a ɗauka ba domin samar da maslaha.
Haka kuma bai bayyana wani mataki da za a ɗauka ba mai tsauri a kan Moscow idan ƙasar ba ta tsagaita ba.
Amma ya ce za a samu nasara.
'Sake haɗuwa a Moscow'
Duk da cewa taron bai haifar da sakamako mai kyau ba game da yaƙin Ukraine, amma lallai ya yi amfani wajen ɗan sassauta saɓanin da ke tsakanin Rasha da Ukraine.
An ga hotunan shugabannin biyu suna gaisawa suna murmushi, da kuma yadda jami'an tsaron Amurka suka girmama Putin tun daga saukarsa daga jirgin sama.
Sannan kafin ya kammala jawabinsa, Putin ya nanata abin da shugaban Amurka Trump ya daɗe yana fada cewa da a ce shi ne shugaban Amurka a lokacin, da ba a ma fara yaƙin ba.
A ƙarshe kuma sai Putin ya kalla Trump, inda ya ce masa, "watarana a Moscow."
Sai Trump ya amsa da cewa, "zan yi kokarin ganin faruwar haka."










