Shugabannin Turai na fargabar Trump zai tursasa wa Zelensky kan Rasha

Zelensky da Trump da JD Vance
Lokacin karatu: Minti 4

Shugabannin Turai za su rufa wa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky baya a ganawar da zai yi da Shugaba Trump a fadar gwamnatin Amurka, Litinin din nan, inda jagororin ke nuna damuwa kan Trump ka iya tilasta wa jagoran na Ukraine amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya a yakinsa da Rasha.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky zai iya kawo karshen yakin da Rasha ke yi da Ukraine din nan take idan har Mista Zelenskyn na son haka.

Haka kuma kuma Trump ya ce babu maganar Ukraine din ta shiga kungiyar tsaro ta Nato da kuma maganar mayar wa Ukraine din yankinta na Crimea da Rasha ta mamaye, duka a matsayin sharudan tattaunawar zaman lafiya.

Trump ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara kafin ganawar da zai yi da shugaban na Ukraine da kuma kawayen Ukraine din na Turai a Washington a yau Litinin.

Shugaban na Amurka ya bayyana wadannan sharuda ne ‚yan sa'o'i kafin ganawar ta musamman da Shugaba Volodymyr Zelensky da sauran abokan Ukraine din na Turai a fadar Amurka -White House.

Za su yi wannan ganawa ne bayan wadda shi Trump din ya yi ranar Juma'a da Shugaba Putin na Rasha a jihar Alaska ta Amnurkar.

Somawa da iyawa Mista Trump ya zayyana wadannan sharuda ne wadanda wasu na daga cikin manyan ginshikan Ukraine a alakarta ko yakinta da Rasha – batun shigar Ukraine din kungiyar Nato da kuma mayar mata da ikon yankin Crimea wanda Rasha ta mamaye a 2014, shekara takwas kafin ta kaddamar da yaki dungurungum a kann makwabciyar tata.

Bayan ganawar ta Alaska ce Shugaba Trump ya ce shi yanzu ba ma maganar dakatar da bude wuta yake yi a yankin na Rasha da Ukarine ba – yana neman a yi yarjejeniya ne ta dindindin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rasha dai ta kafe kai da fata da adawa da burin Ukraine na shiga kungiyar tsaro ta Nato.

Kafin komawar Trump mulki a watan Janairu, kasashen Nato sun amince cewa ba maganar shigar Ukraine kungiyarsu abu ne da tamkar ya riga ma ya tabbata – ba komawa baya a kansa.

Sai kuma a yanzu Trump ya bayyana wannan sanarwa ta sauya wannan magana kuma a matsayin sharuddan da yake gindaya wa Ukraine na kawo karshen yaki da Rasha.

Babban sakataren kungiyar ta Nato Mark Rutte, tare da shugabannin Turai da suka hada da Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer, za su rufa wa Shugaba Zelensky baya a tattaunawar ta Litinin kan makomar Ukraine din.

Haka kuma a tawagar akwai Shuagaban Faransa Emmanuel Macron, da Firaministar Italiya Giorgia Meloni, da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, da shugaban Finland Alexander Stubb da kuma shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Sai dai ba a san su nawa ne za su shiga fadar gwamnatin Amurkar ba domin halartar wannan ganawa da mai masaukinsu Donald Trump wanda ya ce ya zaku da ganin wannan babban taro.

Trump yace ba a taba samun shugabannin Turai da yawa haka a lokaci daya ba a fadar – yana mai cewa babban abin alfahari ne a gare shi ya karbi bakuncinsu.

Wasu kafofin diflomasiyya sun ce jami'an Turai na nuna damuwa cewa Trump zai iya neman ya tursasa wa Zelensky kan ya yarda da sharudda, bayan da aka ware shugaban na Ukraine a ganawar da Trump din ya yi da Putin ranar Juma'a.

To amma kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya gaya wa kafar yada labarai ta CBS da ke Amurka mai kawance da BBC, cewa maganar wai kila Trump ya tilasata wa Zelensky amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya – zancen kawai ne na 'yan jarida.

Shugabannin Nato na fatan ganin an kauce wa maimaicin abin da ya faru a fadar gwamnatin Amurka a watan Fabarairu lokacin da shugaban na Ukraine ya je fadar inda Trump da mataimakinsa JD Vance suka titsiye shugaban na Ukraine – inda Trump ya zargi Zelensky da neman janyo Yakin Duniya na Uku – ganawar da ta sukurkuta alakar Amurka da Ukraine.

Sai dai a wani taro da ya yi ranar Lahadi ta bidiyo da shugabannin Nato, Shugaba Zelensky ya jadda cewa kundin tsarin mulkin Ukraine ba zai bari kasar ta sallama wani yanki nata ba.

Kuma ya ce wannan magana ce da taron koli na shi da Putin na Rasha da kuma shugaban Amurka za su yi.