Putin na rikirkita yunƙurin dakatar da yaƙi a Ukraine - Zelensky

Vladimir Putin (hagu) da Volodymyr Zelensky

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce bisa ga dukkan alamu Rasha ba ta son a kawo karshen yakin da take yi da kasarsa.

Zelensky ya yi wannan zargi ne saboda kin amincewa da Rasha ta yi da yarjejeniyar dakatar da bude a ganawar da Shugaba Trump ya yi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a jihar Alaska ta Amurkar, ranar Juma'a.

A wani sako da ya sanya a shafinsa na X Mista Zelensky ya ce yadda Rasha ta yi watsi da kiraye-kirayen dakatar da bude wuta ta nuna cewa ba ta yanke shawara kan lokacin da za ta daina kisan da take yi ba.

Shugaban na Ukraine ya yi nuni da zilliyar da Shugaba Putin yake yi tare da kin yarda da duk kiran da ake yi na kawo karshen yakin – musamman a yayin ganawar ta Putin da Trump.

Mista Zelensky ya nuna yadda Rashar ke kauciya duk ta inda aka bullo mata – hakan ya nuna ba ta shirya kawo karshen abin da ya kira kisan al'ummar kasarsa da take yi ba kawo yanzu.

Shugaban na Ukraine ya fitar da wanan sanarwa ne yayin da zai tafi Washington a gobe Litinin inda zai gana da Shugaba Trump, na Amurka – Trump din dai ya ce zai bukaci Zelensky da ya amince da yarjejeniyar zaman lafiya.

Trump yana son kaucewa maganar dakatar da bude wuta a Ukraine – maimakon haka zai yi sabi-zarce ne kai tsaye zuwa ga maganar zaman lafiya na dindindin – bayan ganawarsa ta Alaska da Shugaba Putin.

A wani mataki da ake ganin ya sauya matsaya – shugaban na Amurka ya sanya a shafinsa na sada zumunta bayan ganawarsa da Putin – cewa hanyar da ta fi dacewa kenan wajen kawo karshen wannan yaki tsakanin Rasha da Ukraine – yana mai karin bayani da cewa galibi dakatar da bude wuta kawai ba kasafai take dorewa ba.

Bayan taron kolin na Trump da Putin ne wanda Trump bai gayyaci Zelensky ba – sai Zelenskyn ya kira Trump ta waya inda ya yi kira da samar da aman lafiya na gaske ba na je-ka-na-yi-ka ba ko bigi-bagiro ba – ya kuma nuna cewa dole ne a dakatar da bude wuta da tsayar da kisan haka.

A wani sakon da ya sanya daga baya kuma a shafin sada zumunta Mista Zelensky ya zayyana bukatun da yake son ganin an cimma kafin a kai ga zaman lafiya mai dorewa da Rasha – ciki har da bayar da tabbacin tsaron kasarsa na gaske da mayar da yaran da ya ce Rasha ta sace daga yankunan da ta mamaye.

A nasa bangaren shi kuwa Shugaban Rasha an ce ya gabatar wa Putin bukatunsa na cimma zaman lafiya da Ukraine da suka hada da janyewar Ukraine din daga yankin Donetsk da bai wa sallama wa Rashar wasu yankunanta, daga nan Rashar za ta dakatar da yakin a fagen dagar Zaporizhzhia da Kherson.