Me Putin da Trump ke son cimmawa a ganawar da za su yi a Alaska?

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin na gaisawa, yayain da suke kallon juna, hannun Putin da agago ga kuma wata fulwa a bayansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin na shirin ganawa a Anchorage ranar Jumaʼa
    • Marubuci, Anthony Zurcher and Steve Rosenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Alaska
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin za su tafi ganawarsu a yau Jumaʼa da za su yi a jihar Alaska da muhimman abubuwan da suke son cimmawa yayin da suke shirin tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙin Rasha a Ukraine.

Putin ya sha maimaita aniyarsa ta mamaye dukkanin Ukraine, yayin da Trump bai ɓoye aniyarsa ta zama jakadan wanzar da zaman lafiya a duniya.

Amma mutanen biyu ka iya samun wasu damarmakin na daban, kamar gyara wa Putin hulɗar diflomasiyya da sauran ƙasashen duniya.

Kintacen abubuwan da Trump ke son cimmawa yayin tattaunawar ya fi wahala, duba da maganganu masu cin karo da juna dangane da Putin a baya-bayan nan.

Ga cikakken nazari game da abubuwan da shugabannin ka iya nema daga ganawar.

Putin na neman yardar ƙasashen duniya... da sauran abubuwa

Daga Editan Rasha Steve Rosenberg

Abu na farko da Putin ke neman daga ganawar abu ne da ya riga ya samu, wato amincewa.

Amincewa daga ƙasa mafi ƙarfi a duniya, Amurka na nufin shirin ƙasashen Yamma na mayar da Rasha saniyar ware ya lalace.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma wannan tattaunawar mai muhimmanci manuniya ce cewa an samu hakan.

Fadar Kremlin za ta iya iƙirarin cewa Rasha ta dawo ganiyarta a siyasar duniya.

Ba ma tattaunawar ba ce kaɗai nasarar da Putin ya samu ba, har da wurin da za a yi ganawar. Alaska ta zamto wata garkuwa ga Kremlin.

Da farko, tsaro. Alaska na da nisan kilomita 90 daga garin Chukotka na Rasha.

Vladmir Putin zai iya kai wa nan ba tare da jirginsa ya bi ta saman ƙasashen da ba "ƙawayen" Rasha ba.

Abu na biyu, jihar na da nisa mai yawa daga Ukraine da Turai. Hakan ya dace da aniyar Kremlin na ajiye Kyiv da ƙawayen Ukraine da ke Turai a gefe, tare da tattaunawa kai tsaye da Amurka.

Akwai kuma shaidar tarihi ma.

Kasancewar Rasha ta sayar wa Amurka da Alaska a ƙarni na 19 ya zama wata hujja ga Moscow a ƙoƙarin da take na sauya iyakokin ƙasarta ta ƙarfi a ƙarni na 21.

Amma Putin ba wai amincewar ƙasashen duniya kawai yake nema ba, har da nasara yake nema.

Putin ya dage sai Rasha ta riƙe dukkanin wuraren da ta karɓe a yankunan Ukraine huɗu (Donetsk, Luhansk, Zaporizhzhia da Kherson) kuma Kyiv ta janye daga dukkanin wuraren da take da iko da su a waɗanann yankuna.

Ga Ukraine hakan ba mai yiwuwa ba ne. "Yan Ukraine ba za su saki ƙasarsu ga masu mamaya ba," a cewar shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky.

Kremlin ta san da hakan,amma idan ta samu goyon bayan Trump a abubuwan da take nema a nan, lissafin shi ne rashin amincewa da hakan daga Ukraine zai iya nufin Trump ya janye goyon baya ga Kyiv gaba ɗaya.

Bayan hakan, Rasha da Amurka za su bunƙasa alaƙarsu tare da ci gaban ƙawancen tattalin arziƙi.

Amma akwai wani abin da zai iya faruwa.

Tattalin arziƙin Rasha na fuskantar matsi. Giɓi a kasafin kuɗi na ƙaruwa kuma kuɗin da take samu daga fitar da mai da iskar gas na raguwa.

Idan matsalolin tattalin arziƙi za su iya tursasa Putin ya kawo ƙarshen yaƙin, Kremlin ka iya saduda.

A yanzu dai babu alamun hakan - kuma jamiʼan Rasha sun dage cewa ƙasar na samun nasara a filin daga.

Trump na fatan iƙirarin alfahari da zaman lafiya

Daga wakilin BBC a Arewacin Amurka Anthony Zurcher

Trump ya taɓa yin alƙawari yayin yaƙin neman zaɓensa a 2024 cewa kawo ƙarshen yaƙin Ukraine abu ne mai sauƙi kuma zai iya yin hakan cikin ƴan kwanaki.

Wannan alƙawarin ya tsaya wa Trump a ƙoƙarin da yake na kawo ƙarshen yaƙin, yayin da ya ɓata da ƴan Ukraine da Rasha tun bayan dawowa White House a Janairu.

Ya caccaki Zelensky yayin wata ganawa mai cike da ban mamaki a White House a watan Fabrairu, kuma daga baya ya dakatar da ba da agajin soji da na bayanan sirri ga Ukraine na wucin-gadi.

A ƴankwanakin nan ya fi caccakar Putin saboda jan ƙafar da yake yi da kuma yadda yake kai hari kan fararen hula.

Ya sha sa ranar sanya sabbin takunkumai, na baya-bayan nan shi ne ranar Jumaʼa da ta gabata, amma bai iya cika iƙirarin nasa ba.

Yanzu kuma zai karɓi baƙuncin shugaban Rasha a Amurka, kuma Ukraine na tsoron zai yarda da cefanar da wasu ɓangarorin ƙasar don samun zaman lafiya.

Saboda haka, duk wata tattaunawa game da abin da Trump yake so yayin ganawar ranar Jumaʼa za ta zama cike da maganganun shugaban ƙasar masu cin karo da juna da ya yi.

Wannan makon, Trump ya yi ƙoƙarin rage abubuwan da ake tsammani daga ganawar - wataƙila saboda akan yarda ne da matuƙar wahalar samun wani ci gaba daga tattaunawar da za a yi da ɓangare guda cikin rikicin.

A ranar Litinin, Trump ya ce ganawar za ta kasance "ta zubar da abin da ke zuci". Ya ce zai so ya san ko zai iya cimma wata yarjejeniya da shugaban na Rasha "cikin minti biyu na farkon ganawar".

"Zan iya tafiya na ce, shikenan, ba na ji za mu iya sulhunta lamarin nan."

A ranar Talata, Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House Karoline Leavitt ta jadda hakan.

A duk lamarin da ya shafi Trump, ya fi kyau a tsammaci abin da ake gani na da wahalar faruwar.

Kuma Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai sun tattauna da shi ranar Laraba a wani yunƙuri na tabbatar da bai cimma wata yarjejeniya da Putin da ba za ta yi wa Ukraine daɗi ba.

Abu ɗaya da aka sani shi ne Trump zai so duk wata dama ta kasancewa mutumin ya kawo ƙarshen yaƙin.

Ba ɓoyayyen abu ba ne cewa yana son samun shaidar zaman lafiya ta Nobel Peace.

Putin kuma mutum ne da ya iya tattaunawa, kuma zai iya barin Trump ya samu hakan, amma da amincewar Rasha.