An gaza cimma matsaya kan kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
An kammala tattaunawar fiye da sa'oi biyu da rabi tsakanin Donald Trump da Vladimir Putin ba tare da cimma matsaya ba a kan yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Shugabannin biyu sun ya jawabi ga manem alabarai a ƙarshen taron, inda suka yi kalaman mutumta juna da kuma yaba yadda ganawar tasu ta kasance.
A jawabansu daban-daban, daga shugaban Amurkan har na Rasha, babu wanda ya ambaci batun tsagaita wuta a Ukraine.
Haka nan kuma, daga cikin su babu wanda ya amsa tambaya daga ƴan jarida, bayan kammala jawabansu.
Mr Putin ne ya fara gabatar da jawabi, inda ya ce yana sha'awar ganin an kawo ƙarshen yaƙin, amma fa yana so a fara magance damuwar da Rasha ke da ita a kan batun kafin duk wani abu da zai iya biyo baya.
Da ya fara nasa jawabin, Mr Trump ya yi waiwaye kan irin kyakkyawar alaƙa da ke tsakaninsa da shugaba Putin.
Ya ce zai kira shugabannin ƙungiyar tsaro ta NATO domin shaida masu yadda tattaunawar ta kasance.
Ya ce ''An amince da buƙatu da dama, akwai dai ƴan kaɗan da ba a cimma matsaya ba, wasu daga ciki kuma ba su da muhimmanci sosai...ana iya cewa ɗaya ne kaɗai mai muhimmanci a ciki. ba mu kai ga nasara ba, amma akwai yaƙinin kaiwa gare ta.''
Kafin yanzu dai an samu kyakkyawar fata game da wannan ganawa, wadda shugaba Trump ya riƙa kambawa, har ma aka riƙa jin shi yana barazanar ɗaukar tsauraran matakai a kan shugaba Putin, idan har bai kawo ƙarshen yaƙin da Ukraine ba.
Amma daga bayanan shugabannin biyu, ana iya cewa akwai sauran Rina a Kaba, game da alwashin da Trump ya sha ɗauka game da yaƙin.










