Yadda Rasha ta sayar wa Amurka jihar Alaska kan dala miliyan 7.2

Asalin hoton, Hulton Archive/Getty Images
Tattaunawar da Amurka za ta yi da Rasha a jihar Alaska ranar Juma'a domin ganin an kawo karshen yaƙin Ukraine, zai kasance ɗaya daga cikin tattaunawar diflomasiyya mafi muhimmanci a cikin shekaru.
Jihar Alaska wato wurin da za a yi tattaunawar yana da muhimmanci a tarihi.
Shugaba Donald Trump da Vladimir Putin za su gana a Anchorage, birni mafi girma a jihar Alaska.
Sai dai idan da an gudanar da tattaunawar a wurin shekaru 50 da suka wuce, wurin zai kasance cikin yankin Rasha.
Saboda Alaska - da ta kasance jiha mafi girma a Amurka, kashi ɗaya cikin biyar na ɗaukacin yankin ƙasar - Rasha ce ta mallake shi a baya.
'Abu ne mai kyau tattaunawa a Alaska'
Alaska ta kasance a yankin arewacin Amurka, kuma mashigar Bering ce ta raba su da Rasha - wadda ke da nisan mil 50.
Lokacin da shugaba Trump ya sanar da cewa za a yi tattaunawar a Alaska, maitaimaka wa shugaban Rasha Yuri Ushakov ya ce "abu ne mai kyau" ga tawagar Rasha "ta yi balaguro ta kan mashigar Bering don zuwa tattaunawar mai muhimmanci tsakanin shugabannin ƙasashen biyu da za a yi a Alaska".
Sai dai dangantaka tsakanin Rasha da Alaska wadda ta faro tun shekarun 1700, tana da daɗɗen tarihi - lokacin da al'ummar yankin Siberia suka fara ruwaito batun wannan yankin da ke gabashi.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike da wani ɗan ƙasar Denmark, Vitus Bering, ya yi ya gano cewa sabon yankin bai haɗu da asalin ƙasar Rasha ba.
Amma sakamakon yawan dutsar ƙanƙara, aka gaza samun nasara kan binciken.
A shekarar 1741, wani binciken da Bering ya sake jagoranta, ya samu yin nasara kuma an tura mutane domin zuwa su gani.
Daga wasu bincike-bincike kan kasuwanci da dama sun biyo, lokacin da aka mayar da wasu dabbobin ruwa zuwa Rasha - lamarin ya buɗe hanyar kasuwanci mai girma tsakanin Turai da Asiya da kuma tekun Pacific da ke yankin Arewacin Amurka.
Sai dai, a ƙarni na 19, ƴan kasuwa daga Birtaniya da Amrka sun zama masu gasa da Rasha a ɓangaren kasuwancin dabbobin ruwa.
Yayin da aka kawo ƙarshen gasar a 1824 - lokacin da Rasha ta sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi daban tsakaninta da Amurka da Birtaniya.
Batun karewar dabbobin ruwan a doron ƙasa da kuma tasirin yaƙin Crimea (a 1853-1856) ya sanya Rasha duba batun sayar da Alaska ga Amurka.
Sayan Alaska tamkar 'kasada ce'
Sakataren harkokin wajen Amurka a wancan lokaci, William Seward, ya jagoranci tattaunawar sayan Alaska da kuma ƙulla yarjejeniya da Rasha.
Bayan samun gagarumar adawa, majalisar dokokin Amurka ta amince da buƙatar da Sewar ya gabatar na sayan Alaska kan kuɗi dala miliyan 7.2.
Kuma a ranar 18 ga watan Oktoban 1867, aka ɗaga tutar Amurka a babban birnin jihar Alaska na wancan lokaci, Sitka.
Tun da farko, masu sukar Seward sun kwatanta sayan jihar Alaska da cewa ba shi da ma'ana ko kuma tamkar kasada - inda suka ce yankin ba shi da wani alfanu.
Idan aka yi duba a ɓangaren hauhawar farashi, dala miliyan 7.2 ɗin da Amurka ta yi amfani da shi wajen sayan Alaska, zai kai dala miliyan 100 a yau - wanda ƙanƙanin kuɗi ne ga jihar da ta fi girma a Amurka a yanzu.
Daga ƙarni na 19, an fara gano zinare da mai da kuma iskar gas a jihar Alaska - wanda ya sanya aka fara samun kuɗaɗen shiga.
Matakin Seward ya kasance mai amfani, kuma a 1959, Alaska ta kasance jihar Amurka ta 49 a hukumance.

Asalin hoton, Hasan Akbas/Anadolu via Getty Images
Jihar na da ɗimbin albarkatun ƙasa, inda a yau take da koguna 12,000 da kuma tafkoki da dama.
Babban birnin jihar, Juneau, shi ne wuri ɗaya tilo a Amurka da za a iya zuwa kaɗai ta hanyar jirgin ruwa ko kuma jirgin sama.
Yayin da tafkin Hood a yankin Anchorage ya kasance wuri mafi zirga-zirgar jiragen ruwa, inda jirage kusan 200 ke tashi a kowace rana.
Shugaba Trump da Putin za su gana a ginin soji na Elmendorf-Richardson - wanda ya kasance wurin soji mafi girma a jihar.
Wurin ya kasance yana da girman eka 64,000
Wannan ba shi ne karon farko da Alaska ke karɓar bakuncin tattaunawar diflomasiyya ba.
A watan Maris ɗin 2021, Joe Biden sabbin tawagar tsaro na shugaban a lokacin, suka gana da takwarorinsu na China a birnin Anchorage.
Babu wani bayani daga hukumomi kan taron, sai dai fadar White House ta ce Alaska za ta kasance "wurin tsaurara tsaro".
Ga shugaba Trump kuma zai ba shi "damar sanin yadda zai kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine".
Lokacin da ya sanar da batun taron a makon da ya gabata, Trump ya nuna farin ciki cewa ganawar za ta haifar da sakamako mai kyau na samun zaman lafiya.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sha bayyana cewa duk wata yarjejeniya ba tare da saka Kyiv a ciki ba, zai zama tamkar "matakai na iska" waɗanda ba za su haifar da ɗa mai ido ba.











