Mece ce alaƙar ƙwayar halittar jini da kamuwa da cutar malaria?

Asalin hoton, Getty Images
Wataƙila kun taɓa jin cewa cutar zazzaɓin cizon sauro da aka fi sani da maleria ta fi kama masu ƙwayar halaittar jinin AA, inda masu AS suke da garkuwa daga cutar.
To sai dai kuma masu ƙwayar jinin SS waɗanda ake kira sikila na da garkuwa mai karfi daga cutar duk da cewa idan ta kama su ba ta yi musu ta daɗi.
Shin mene ne gaskiyar wannan tunani da jama'a ke yawan ji? Sannan kuma waɗanne irin matakai ya kamata kowane aji na ƙwayar halittar jinin ya kamata su dauka domin kariya?
Yadda cutar zauro ke shiga jikin mutum

Asalin hoton, Getty Images
BBC ta tattauna da Dakta Umar Sani Ibrahim, wanda likita ne mai neman ƙwarewa a ɓangaren Lafiyar Al'umma a asibitin koyarwa na KASU, wato Barau Dikko a Kaduna.
"Gaskiya ne akwai alaka ta kusa da ta nesa, saboda shi "genotype" ne yake bayyana kalar jinin mutum kuma akwai AA da AS da SS, akwai wasu kamar SC da sauransu.
Ita kuma maleriya ba ta yaduwa sai ta kwayar halittar jini ta ja wato RBS na jikin mutum. Idan sauro ya ciji mutum, sai ya saka kwayar cutar a jinin mutum, sai kwayar ta wuce zuwa hantar mutum.
A nan akwai wani mataki na girma da cutar ke kai wa sai cutar ta fita daga hantar ta fada cikin jini, a hanyar jinin ne take kara rubanya ta kara yawa, sai daga nan ta kara girma ta fashe ta shiga wata hanyar jinin daban.
Illar Malaria ga AA da AS da SS

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Umar ya ce sai bayan cutar da sauron ya zuba a jikin ɗan'adam ne ta fita daga hantarsa za a gane irin illar da take yi wa kwayar halittar jinin na mutane wato "genotype".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Idan ta shiga jinin AA, masu AA jininsu ba shi da ƙwari sosai, sai ta shiga ta kara rubanya sosai ta kara yawa fiya da yadda ta fito daga hanta. Sai ka ga mutum ya kamu da cutar.
Likitan ya ƙara da cewa su masu ƙwayar halittar jini ta AS da SS ba wai ba sa kamuwa da zazzaɓin cizon sauro ba ne, a'a jininsu ne bai barin ƙwayar cutar ta yi tasirin azo-a-gani.
"Amma su masu AS da SS, idan kwayar cutar ta shige su, jinin bai barin kwayar cutar ta rubanya sai ya mokade ya fashe. Ta wannan hanya sai ka ga ba wai ba sa kamuwa ba ne, suna kamuwa amma kwayar cutar ba ta rubanya ba sosai kafin ta fashe ya yadu kamar na AA."
"Shi ya sa ba wai ba a samun masu cutar ba ne, ba ta wahalar da su ne ta yi yawa sosai kamar na AA. Su masu SS jininsu a mokade, amma ba duka ba ne, akwai mai kyau, idan cutar ta shiga, sai ta shiga cikin wadanda ba mokadaddu ba, sai ya cigaba da mokadewa suna fashewa, sai su kamu da cutar ta hanyar zazzabi." In ji Dakta Umar.
Hanyoyin kare kai
Hanyoyin kariya manya su ne gujewa wuri mai datti da shara da tarin ruwa.Sannan amfani da safa a lokacin zama a wuraren da ya kamata a guji zamansu wato masu sauro.
Sai dai kuma hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bada shawarwarin kariya daga kamuwa da cutar da dabarun da take ganin su ne mafita.
Hanyoyin kariyar sun kasu gida biyu - akwai amfani da gidan sauro da kuma feshin maganin sauro - wanda akasari aka fi yi a lokuta da dama.
- Bacci da gidan sauro na rage damar da sauro ke da ita na cizon mutum.
- Feshin maganin kwari a gidaje da gine-gine, akalla sau daya ko biyu a shekara na taimako sosai.
- Sannan kuma ana iya kare kai daga Malaria ta hanyar shan magungunan rigakafi da ake kira anti-malarial drugs ga matafiya, mata masu juna-biyu da kananan yara.











