Abin da muka sani kan maganin maleriya na farko da zai warkar da jarirai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Dominic Hughes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 3
An amince da rigakafin maleriya na farko da za a iya yi wa jarirai da ƙananan yara.
Ana sa ran rigakafin ya fara aiki a ƙasashen Afirka nan da makonni.
Kafin wannan lokaci babu wani takamaiman maganin zazzaɓin cizon sauro da aka amince a riƙa amfani da shi ga jarirai.
Ana amfani ne da magungunan da ake yi saboda yaran da suka ɗan girma wanda hakan ke haifar da barazanar basu maganin da ya wuce kima.
Mutuwar mutane rabin miliyan a 2023
A 2023 - shekarar da kusan za a ce ana da tabatattun alkaluma - ana cewa zazzabin cizo sauro na malaria ya yi ajalin kusan mutane 597,000.
Kuma wannan adadi kusan dukka a Afirka ne, kashi 3 cikin hudu na adadin yara ne 'yan kasa da shekara biyar.
Akwai magungunan malaria da ake yi wa yara, sai dai babu wani magani na musamman da ake yi sabbin jarirai da kananan yara, wanda nauyinsu ba ya wuce kilogram 4.5 zuwa 10.
Ana mu su magani ne da magunguna da aka samar domin yara manya.
Hakan na da illa, saboda galibin magunguna na tattare da illar da za su iya yiwa jarirai, wanda hunhunsu ke soma aiki kuma jikinsu na kokarin karɓan sabbin magunguna daban-daban.
Kwararru sun ce wannan ba karimin giɓi ya ke haifarwa ba wajen samun saukinsu.
Yanzu sabon magani, wanda kamfanin haɗa magunguna na Novartis ya samar, hukumomi a Switzerland sun amince da shi, kuma ana sa ran nan da makonni kadan za a kai shi ƙasashe makwabta da sauran nahiyoyi da ƙasashe da malaria ya fi yiwa illa.
Novartis na da tsarin ganin cewa maganin bai kasance abin da za a ɗaura buri ko riba ba.
Mafi kankanta kuma mafi inganci
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban kamfanin, Vas Narasimhan, ya ce wannan lokaci ne mai muhimmanci.
"Sama da shekara 30, mun dage wajen yaƙi da cutar malaria, muna aiki tukuru domin cimma nasarar kimiya a inda ake bukata.
"Tare da abokan huldarmu, muna alfaharin ganin mun yi nasara wajen samar da maganin ga jarirai da kananan yara, da tabbatar da cewa duk kankantan jariri da kwanakinsa a duniya zai samu magani mai inganci da jikinsa ke bukata."
Maganin, wanda aka sani da Coartem Baby ko Riamet Baby a wasu ƙasashen, kamfanin Novartis ne ya samar da shi da haɗin-gwiwar cibiyar haɗa magunguna Malarai ta 'Medicines for Malaria Venture (MMV), a Switzerland, ƙungiya ce mai zaman kanta da ke samun taimako daga gwamnatocin Burtaniya da Switzerland da Netherlands, da kuma bankin duniya da gidauniyar Rockefeller.
Ƙasashen Afirka takwas na cikin waɗanda suka shiga wannan shiri da kuma soma aiwatar da gwajin maganin a kansu, kuma suna cikin rukuni na farko da za a soma kai wa maganin.
Shugaban cibiyar MMV, Martin Fitchet, ya ce wannan wannan cigaba ne mai muhimmanci a kokarin kawo karshen malaria da kisan da take yi.
"Malaria na ɗaya daga cikin cututtuka masu haɗarin gaske da ke kisa a duniya, musamman a tsakanin yara. Amma kuma ta hanyar bin hanyoyin da suka dace da mayar da hankali, ana iya kawar da ita.
"Amincewa da Coartem baby na nufin samar da maganin da ake bukata, mafi dacewa da za a yi amfani da shi a bisa kaida, wajen warkar da jarirai wanda a baya ake ganinsu a matsayin wani rukunni na al'umma da aka ware ko rashin mayar da hankali wajen ganin an sama musu magani mafi dacewa."
Dakta Marvelle Brown, da ke shirin zama Farfesa a Jami'ar Hertfordshire, ya ce wannan gagarumin cigaba ne na ceton rayuwar jarirai da kananan yara.
"Mutuwar da ake dangatawa da Malaria, musamman a ƙasashen kudu da hamadar Sahara ya kai mataki na kololuwa - sama da kashi 76 cikin 100 na mace-macen da ake samu sakamakon malariar, yara ne 'yan kasa da shekara biyar.
"Karuwar mutuwa sakamakon malaria ya fi muni a yaran da ake haifa da ciwon sikila, saboda rashin garkuwan jiki mai karfi.
"Kwararru a fannin lafiyar al'umma na ganin, kasance Novartis ya taimaka wajen ganin maganin bai kasance wanda za a daura riba ba, hakan zai taimaka wajen daidaita matsalar da ake fuskanta wajen samun kulawar lafiya."











