Abu biyar da suka kamata ku sani kan rayuwar sauro

Asalin hoton, PA Media
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Kusan kowane mai rai a duniya - musamman a Afirka - ya taɓa fuskantar cizon sauro.
Sai dai ba kowa ne ya taɓa kamuwa da cuta daga cizon ba saboda ba kowane sauro ne ke yaɗa cuta ba.
Akasarin mutane da zarar sun ji "wuuuuuu" na rundunar sauro sai su ji a ransu cewa "ga maleriya nan ta tunkaro", alhalin kuma akwai aƙalla cutuka shida bayan maleriya da zai iya saka musu.
Hasali ma, macen sauro da ake kira Anopheles ce kaɗai ke cizon mutane da dabbobi. Muna iya cewa namijin ba shi da mugunta sosai.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cizon ƙwari, ciki har da sauro, su ne ke haddasa kashi 17 cikin 100 na mace-mace 700,000 duk shekara a duniya saboda cutuka masu yaɗuwa.
Albarkacin Ranar Yaƙi da Sauro ta Duniya da akan yi duk ranar 20 ga watan Agusta, mun duba abubuwa biyar da suka kamata ku sani game da halittar sauro.
Ta yaya ake halittar sauro kuma nawa ne adadin tsawon ransa?
Masana halittar sauro sun ce akwai nau'i na sauro kusan 3,000 da ke rayuwa a duniyar nan, a cewar shafin ma'aikatar muhalli ta ƙasar Canada.
A Amurka kaɗai akwai kusan nau'i 200, a cewar hukumar kiyaye yaɗuwar cutuka ta Amurka. A Canada kuma akwai kusan 80.
Halittar sauro kan fara ne kamar haka:
- Balagaggiyar macen sauro wato Anopheles kan dasa ƙwai a kan ruwan da ba ya tafiya
- Ƙwan zai rikiɗe zuwa ɗantayi da ake kira larvae a Turance kuma ya koma rayuwa a kan ruwa
- Sai ya shiga matakin pupae
- Daga nan kuma sai ya zama balagaggen sauro mai tashi
- Balagaggiyar macen sauro kan rayu tsawon kwana 42 zuwa 56
- Balagaggen namijin sauro kan rayu tsawon kwana 10 kacal
Waɗanne cutuka sauro ke haddasawa?
Da zarar an yi maganar sauro abin da ke fara zuwa ran mutane, musamman mazauna ƙasashen Afirka, shi ne zazzaɓin maleriya.
Tabbas maleriya ce mafi mugunyar cuta da sauro ke yaɗawa. A cewar WHO, zazzaɓi maleriya ya kama mutum miliyan 263 a 2023 a fadin duniya, sannan ya kashe mutum 597 000.
Hukumar WHO ta ce a 2023, kashi 94 cikin 100 (miliyan 246) na masu zazzaɓin maleriya suna ƙasashen Afirka, da kuma kashi 95 (569,000) na waɗanda suka mutu.
Sai dai akwai cutuka aƙalla bakwai da aka tabbatar sauro kan haifar, kuma dukkansu sun fi kama da zazzaɓi. Su ne:
- Chikungunya
- Dengue
- Lymphatic filariasis
- Maleriya
- Rift Valley
- Shawara (Yellow Fever)
- Zika
A cewar WHO, yara 'yan ƙasa da shekara biyar ne suka fi shiga haɗari na cutukan da sauro ke yaɗawa.
Ta yaya sauro ke yaɗa maleriya?
Akasarin mutane na kamuwa da zazzaɓin maleriya ne bayan sauron da ke ɗauke da ƙwayar cutar ya cije su.
Sauron kan samu cutar ne bayan ya ci ji wani mutum ko dabba da ta riga ta kamu da cutar, ko kuma ya sha jinin halittar da ke da cutar.
Bayan mako ɗaya kuma, sai wannan sauron ya ciji wani mutumin kuma ya saka masa ƙwayoyin ta yawunsa.
Ta haka ne kuma za su ci gaba da yaɗa ta a jikin mutane.
Mutum kan kamu da maleriya ta wasu hanyoyin da ba su cika faruwa ba kamar:
- Wajen ƙarin jini
- Dashen gaɓa
- Amfani da sirinji ko allurar da aka yi wa wanda ya kamu da cutar amfani da su
- Ko kuma uwa ta harba wa jaririn da ke cikinta kafin ko kuma a lokacin haihuwa
Wane sauro ne ke yaɗa maleriya?

Asalin hoton, Reuters
Masana kiwon lafiya sun tabbatar cewa mutum ba zai iya yaɗa wa mutum cutar maleriya ba, illa ta wasu hanyoyi ƙalian da ba su cika faruwa ba.
Kamar yadda muka fara bayani a sama, macen sauro mai suna Anopheles ce kaɗai ke cizo.
Wannan dalilin ya sa ita kaɗaice ke yaɗa maleriya daga wani mutum zuwa wani.
Wace annoba sauro ke yaɗawa?
Wani rahoto da hukumar kiyaye yaɗuwar cutuka ta nahiyar Turai ECDC ta fitar a 2023 ya ce nau'in sauro na Aedes albopictus da ke ɗauke da ƙwayar cutar chikungunya ya sauka a ƙasashen Turai 13.
A gefe guda kuma, nau'in Aedes aegypt da ke ɗauke da ƙwayar cutar shawara (yellow fever), da Zika, da West Nile, ya samu gindin zama a ƙasar Cyprus, kuma masana kimiyya sun yi gargaɗin zai iya yaɗuwa wasu ƙasashe.
A cewar rahoton, a 2022 an samu:
- mutum 1,133 da suka kamu da zazzaɓin West Nile, inda 92 suka mutu
- mutane da yawa sun kamu a ƙasashen Italiya, Girka, Romania, Jamus, Hungary, Croatia, Austria, Faransa, Sifaniya, Slovakia, Bulgaria
- mutum 71 da suka kamu da zazzaɓin dangue a Turai










