Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan ci gaba da faɗuwar darajar naira

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Lokacin karatu: Minti 5
Darajar takardar kuɗin Najeriya - naira na ci gaba da faɗuwa lamarin da ke tasiri ga tattalin arzikinta da kuma janyo hauhawar farashin kayayyaki da ya kai wani mataki da ba a taɓa gani ba a tarihi.
Ko a ranar Litinin, ana sayar da naira a hukumance kan naira 1,700 kowace dala ɗaya. Wannan ne mataki mafi muni da darajar naira ta taɓa kai wa tun ranar 19 ga watan Fabarairun bana da a lokacin ake sayar da ita kan naira 1,730 kowace dala ɗaya.
A watan Janairu ne babban bankin Najeriya, CBN ya ce ya soma aiwatar da tsarin inganta kasuwar musayar kuɗaɗe na gajere da matsakaici da kuma dogon zango da nufin kawo sauyi.
Halin da darajar kuɗin Najeriya ke ciki dai na ƙara taɓarɓarewar al'amura da kuma jefa rayuwar al'umma cikin mawuyacin hali - wani lamari da masana ke cewa akwai aiki ja a ɓangaren gwamnati matuƙar tana son ta daidaita al'amura domin talaka ya samu sauƙi.
Batun faɗuwar darajar kuɗin na Najeriya ya ja hankalin ƴan ƙasar musamman a shafukan sada zumunta na intanet inda wasu ke mamaki, wasu kuma ke ta jefa tambayoyi kan makomar naira.
Mun zaƙulo ra'ayoyin wasu ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta kan halin da naira ke ci, ɗaya daga cikin batutuwan da ake tattaunawa a ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1
Ibrahim BK, wani ma'abocin shafin Fesbuk ne inda a saƙon da ya wallafa a shafin nasa, yake cewa 'Bambancin tsakanin ɗala da naira na da girma sosai, ko da kana samun naira ɗaya kullum, ba za ka iya tara dala ɗaya ba cikin shekara huɗu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi kuwa iam_Precious daga shafin X, cewa ya yi "waɗanda aka haifa a 2020 zuwa yanzu, ba za su taɓa yarda cewa an yi zamanin da naira hamsin ce takardar kuɗi mafi girma a Najeriya."
Sai dai duk da yadda wasu al'ummar Najeriya ke yanke ƙauna game da halin da naira ke ciki, akwai wasu da har yanzu suke ganin duk da ƙalubalen da ake fuskanta, wata rana sai labari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Bayan tambayar da shafin Sim ya yi kan ko akwai kuɗin wata ƙasar da zai kawo ƙarshen kaka-gidan da dala ta yi? Emma Ofem dai yana ganin "wata rana, naira za ta dawo da martabarta kan dala."

Dakta Aminu Yusuf cewa ya yi "ban ga wani dalilin da zai sa ba za a canji dala ɗaya kan naira ɗaya ba."
Abin da ya sa darajar naira ke ci gaba da karyewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani ƙwararre kan sha'anin kuɗi, Victor Aluyi ya ce irin wannan faɗuwa da naira ke yi ba ya nuna darajar takardar kuɗin.
Ya ƙara da cewa babbar matsalar da ke janyo tashin farashin dala shi ne tsarin da gwamnatin ta bijiro da shi kan naira na fuskantar babban ƙalubale saboda rashin dalar da ake buƙata domin aiwaatar da tsarin.
Tattalin arzikin Najeriya na buƙatar dala wajen tafiyar da shi kasancewar galibi ana shigo da kayayyakin da ƙasar ke amfani da su ne daga wasu ƙasashen amma ba ta iya samar da kayayyakin da al'ummarta ke buƙata.
Masanin ya ce tsarin daidaita naira da aka soma aiwatarwa watannin baya na fama da ƙalubale da dama.
Ɗaya daga cikin matsalolin, a cewarsa shi ne mutane ba su yi amanna da tsarin ba - dalilin ke nan da mutane ke sayen dala duk da yadda farashinta ya yi sama saboda suna tunanin za su samu kuɗi idan suka yi hakan.
Ƙwararren, Victor Aluyi ya bayyana cewa tsarin na CBN bai fayyace abubuwa ba saboda bankin ba ya samar da bayanai abin da ya sa mutane ba su fahimci abin da ke faruwa ba. Ya kuma ce wannan ne ya sa wasu tsiraru ke amfani da yanayin da ake ciki domin amfanar kansu.
Akwai kuma yankasuwa da suke yaɗa jita-jita ba wai saboda suna son musayar kuɗin idan naira ta faɗi ba amma saboda ba su da tabbacin abin da zai faru idan suka buƙaci sayen dala nan da wata biyu masu zuwa.
Abu na biyu shi ne lokacin da gwamnati ta soma aiwatar da tsarin, ya buɗe masu ido sun gane cewa tashin da dala take a yanzu ba ƙarami ba ne.
Abin da hakan ke nufi, a cewar Aluyi, shi ne, "abubuwa sun cunkushe wa CBN".
"Ba za ka iya daidaita darajar naira kawai da baki ba... a haƙiƙanin gaskiya da zarar ka daidaita naira, dole ne ka samu kuɗin dala da zai tallafa wa tsarin. Idan ba ka samu dala don taimaka wa tsarin ba, to babu abin da zai faru.
"Babban ƙalubalen shi ne babu dalar da za ta taimaka wa tsarin, ana yawan buƙatar dala dalilin da ya sa darajar naira ke ci gaba da sauka a kan dala ke nan."
Wani mai sharhi kan musayar kuɗaɗen waje, Kyle Chapman, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faɗuwar da naira ke yi ya zama ruwan dare kasancewar abin na faruwa a kai a kai.
Chapman ya ƙara cewa idan darajar naira na yawan faɗuwa, ba za a rika samun masu saka hannun jari a Najeriya ba.
Yadda za a magance faɗuwar darajar naira
Aluyi ya ce yana ganin wataƙila wani abu ya faru nan kusa da zai sauya yadda darajar naira ke tafiya a yanzu.
Baya ga wannan, ya ce dole ne gwamnati ta ƙara shigar da dala cikin tattalin arziki.
Ya ce gwamnati za ta iya ƙara abin da take samu daga ɗanyen mai ta hanyar ƙara samar da shi.
Ra'ayin wani mai sharhi kan musayar kuɗaɗen waje, Kyle Chapman, ya zo ɗaya da na Aluyi inda ya ce farashin naira a hukumance ya kusa yin daidai da na kasuwar bayan fage saboda CBN ba zai iya warware basukan da yake bi ba sabo da ƙarancin dala.
Ya kuma ce akwai buƙatar gwamnati ta ƙara kuɗin ruwa ta yadda hakan zai karkato da hankalin masu hannun jari.
Aluyi ya ce idan aka ƙara kuɗin ruwa, zai ƙara yawan kuɗaɗen ƙasashen waje wanda hakan ka iya yawan kuɗaɗen waje da ke hannun gwamnati.
Ya ƙara da cewa duk da cewa wannan ba tsari bane na dindindin, amma zai taimaka wa gwamnati wajen shawo kan matsalar faɗuwar darajar kuɗin naira.











