Shin ko zanga-zangar da ake shirin yi ranar ƴancin kan Najeriya za ta yi tasiri?

Asalin hoton, Getty Images
A karo na biyu a tsawon wata biyu wasu ƴan Najeriya sun sake yi kiran da a fita zanga-zanga domin nuna damuwa kan yanayin matsin tattalin arziƙi da yan ƙasar ke ciki.
Wannan dai ita ce zanga-zanga irinta ta biyu tun bayan wadda aka yi a watan Agusta wadda kuma gwamnati ta ce shiri ne ƙoƙarin "kifar" da gwamnatin dimokraɗiyya wani abu da ya janyo har aka kama wasu mutane kuma aka aike da su gidan yari.
To sai dai masu zanga-zangar ta ranar ƴanci sun ce abin da ya faru a watan Agusta ba zai sa su yi ƙasa a gwiwa ba.
Su wane ne ke shirya zanga-zangar?

Asalin hoton, Omowole/X
Waɗanda suka shirya zanga-zangar dai mai taken #FearlessOctober1 sun ce an shiryata ne domin ci gaba da wadda aka fara mai taken #Endbadgovernance a watan Agusta.
Jagoran masu kiran a gudanar da zanga-zangar kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Omowale Sowore ya ce "mun shirya tsaf" domin gudanar da zanga-zangar, inda ya ƙara da cewa ’za mu hau kan tituna da ƙarfe bakwai na safe na ranar da aka tsara."
Saboda halin gwamnatin da ke ci yanzu, ba zan bayyana tsare-tsaren zanga-zangar ba. Amma dai zan tabbatar muku cewa za a yi zanga-zanga. Zan kuma sake tabbatar da cewa ni ma zan halarci zanga-zangar domin yin alawadai da tsare-tsaren gwamnati na tursasa wa talakawa," kamar yadda Sowore ya shaida wa jaridar Daily Trust.
To sai dai kuma ya yi ƙarin hasken cewa zanga-zangar za ta zama ta lumana.
"Zanga-zangar wadda za a gudanar a faɗin ƙasar za ta kasance ta lumana kamar a koyaushe... Ba za a yi mana barazana ba. Babu wani ƙarfin tuwo ko tarzoma da za ta hana mu fadin gaskiya ga shugabanni ba." In ji Sowore.
Buƙatu 10 da masu zanga-zanga ke nema daga gwamnati

Asalin hoton, Sowore/X
Mista Sowore ya ce da zarar gwamnati ta biya buƙatun ƴan Najeriya guda 10 to ba za a sake jin su sun hau tituna da sunan zanga-zanga ba. Ya kuma lissafa su kamar haka;
- Sakin mutanen da ake tsare da su a zanga-zangar #Endbadgovernance da kuma dukkannin fursunonin da ake tsare da su saboda siyasa kamar Nnamdi Kanu.
- Bai wa ma'aikata isasshen albashi
- Mayar da tallafin man fetur
- Samar da tsaro
- Fito da hanyoyin ƙirƙirar ayyukan yi ga miliyoyin ƴan ƙasar da ba su da aiki
- Haɓaka tattalin arziƙi
- Samar da wutar lantarki
- Yin garambawul ga fannin ilimi
- Sake fasalin ƙasa da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima
- Yi wa sashen shari'a da tsarin zaɓe garambawul
Wane tasiri zanga-zangar #FearlessOctober1 za ta yi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Mukhtar Bello Maisudan wanda malami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce lallai zanga-zangar za ta yi tasiri musamman idan ta lumana ce kamar yadda tsarin mulki ya tanadar.
"Tasirin shi ne zanga-zangar za ta nuna wa gwamnati cewa ƴan Najeriya fa har yanzu ba su gaji da nuna mata cewa abin da take ba daidai ba ne ba. Ba za a zuba ido a ƙyale su su yi duk abin da suke su yi ba wanda matsala ce a mulkin dimokraɗiyya.
Hakan kuwa ita kanta gwamnatin za ta amfana ta hanyoyi guda biyu: gwamnati za ta ɗauki darasi ta samar da sauye-sauye sannan gwamnati za ta gane cewa ƴan ƙasar sun san ƴancinsu." In ji Dakta Maisudan.
Ya ƙara da cewa tasirin irin wannan zanga-zanga ta lumana na fitowa fili ne musamman a lokacin da ba a jin amon muryoyin jam'iyyun adawa.
Masana dai na cewa babban tasirin da zanga-zangar watan Agusta ta yi shi ne irin yadda tun kafin zanga-zangar gwamnati ta yi ta bai wa ƴan ƙasa baki da ka da su yi da kuma irin tallafin abinci da ta alƙawarta.
Bambancin zanga-zangar #FearlessOctober1 da ta #Endbadgoverance

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Mukhtar Bello Maisudan
ya lallai za a samu bambance-bambance tsakanin zanga-zangar guda biyu kamar haka:
- Ba kowa ke maganar zanga-zangar #FearlessOctober1. Wasu jagorori ne musamman daga kudancin Najeriya ke ta kwarmata bayananta saɓanin zanga-zanga-zangar #Endbadgovernance waɗanda a arewacin Najeriya ta fi yin tasiri.
- Zanga-zangar watan Okotoba da alama za ta fi tsari ba kamar wadda aka yi a watan Agusta ba wadda al'amura suka rincaɓe.
- Wannan zanga-zargar bai zama lallai ta samu jama'a masu yawa ba kamar ta baya waƙila saboda tsoron da jama'a suke da shi na abin da ya faru a wadda ta gabata da kuma tunanin cewa babu wani tasiri da zanga-zangar ta yi sakamakon rashin ganin sauyi bayan ta.











