Yadda Moroko ta yi wuf da kyautukan gwarazan ƴan ƙallon Afirka na 2025

Achraf Hakimi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

An sanar da ɗan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe ƙyautar karon farko bayan shekara 52.

Ɗan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku.

Mai tsaron bayan Moroko ya karɓi ƙyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.

Shi ne na farko daga Moroko da ya karbi ƙyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma mai tsaron baya na farko tun bayan ɗan kasar Zaire, Bwanga Tshimen a 1973.

Moroko ce ta lashe yawancin kyautukan da aka raba daga ciki har da ta mace mafi ƙwazo a 2025 ga Ghizlane Chebbak mai taka leda a Saudiya da mai tsaron ragar Al-Hilal, Yassine Bounou a matakin mafi taka rawar gani a shekarar nan.

Gwarzuwar shekara: Ghizlane Chebbak

Ghizlane Chebbak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ghizlane Chebbak

Ghizlane Chebbak ta kafa tarihi a matsayin ƴar Moroko ta farko da ta lashe wannan kyauta tun da aka fara bayar da ita a shekarar 2001.

Ƴar wasan mai shekara 35 ita ce ta zama wadda ta fi zura ƙwallo a raga a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afirka ta 2024, inda ta zura ƙwallo mai ƙayatarwa a wasan ƙarshe na gasar.

Ghizlane Chebbak

Asalin hoton, Confederation of African Football

Duk da haka Moroko ta sha kashi a hannun Najeriya da ci 3-2, kuma mutane da dama sun yi tunanin cewa ƴar wasan Najeriya Ajibade ce za ta samu kyautar, kasancewar ita ce ta lashe kyautar wadda ta fi kowace ƴar wasa ƙwazo a gasar ta cin kofin nahiyar Afirka.

"Na yi matuƙar murnar lashe wannan kyauta," in ji Chebbak. "Wannan sakamakon jajircewa ce ta tsawon shekaru."

Duk da haka Najeriya ba ta tashi hannu-rabbana ba, kasancewar an bai wa Chiamaka Nnadozie lambar yabo ta mai tsaron raga mafi ƙwazo ta shekarar 2025.

Waɗanda suka lashe kyautuka

Gwarzon ɗan ƙwallo Afirka: Achraf Hakimi (Paris St-Germain da Morocco)

Gwarzuwar ƴar ƙwallon Afirka: Ghizlaine Chebbak (Al-Hilal da Morocco)

Mai horas da tawagar maza: Bubista (Cape Verde)

Mai tsaron raga na maza: Yassine Bonou (Al-Hilal da Morocco)

Mai tsaron raga mace: Chiamaka Nnadozie (Brighton da Hove Albion & Nigeria)

Ƙasar da ta fi ƙwazo: Morocco ƴan ƙasa da shekara 20

Ƙasar da ta fi ƙwazo a ɓangaren mata: Najeriya

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo: Pyramids (Masar)

Ɗan ƙwallon ƙungiyar ƙasa da ƙasa mafi ƙwazo: Fiston Mayele (Pyramids da DR Congo)

Matashin ɗan ƙwallo mafi ƙwazo: Othmane Maamma (Watford da Morocco)

Matashiyar ƴar wasa mafi ƙwazo: Doha El Madani (AS FAR da Morocco)

Ƙwallo mafi ƙayatarwa (daga masoya ƙwallon ƙafa): Clement Mzize na ƙungiyar Young Africans a karawa da TP Mazembe.