Osimhen, Hakimi ko Salah, wane ne zai lashe ɗan wasan Afirka na 2025?

Asalin hoton, Getty Images
Achraf Hakimi da Mohamed Salah na a gaba-gaba cikin jerin ƴanwasa 10 da ake ganin za su iya lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa na Afirka na shekara ta 2025.
Hakimi, mai buga ɓangaren dama a cikin masu tsaron baya na ƙungiyar Paris St-Germain da ke Faransa ya taimaka wa ƙungiyar wajen lashe kofin ƙungiyoyi na ƙasar da kuma gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata, yayin da shi kuma Salah ya lashe kyautar ɗan wasan da ya fi kowane zura ƙwallo a gasar Premier ta Ingila, yayin da ƙungiyar ta kare kambinta a gasar.
Ɗan wasan gaba da Everton Iliman Ndiaye da kuma ɗan wasan tsakiya na Tottenham Hotspur Pape Matar Sarr, wadanda suka taimaka wa ƙasarsu Senegal samun gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026 na cikin jerin, tare kuma da ɗan Najeriya Victor Osimhen, wanda ya taɓa lashe kyautar a 2023.
Ɗan wasan tsakiya na Kamaru Andre-Frank Zambo Anguissa, ɗan wasan gaba na DR Congo Fiston Mayele, da Denis Bouanga na Gabon, da na Guinea Serhou Guirassy da kuma ɗan wasan tsakiya na Morocco Oussama Lamlioui duk suna cikin jerin ƴanwasan da aka lissafa.
Salah ya lashe kyautar a shekarar 2017 da kuma 2018, yayin da shi kuma Hakimi ya zamo na biyu a shekaru biyu da suka gabata.
Ɗan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Najeriya ba ya cikin jerin ƴanwasan da aka lissafo a bana, inda hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin ƙwararru wanda ya zaƙulo masu horaswa da ƴanwasan da suka "taka rawar gani" a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara.
An bayyana sunan mai horas da tawagar ƴan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Cape Verde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horaswa mafi ƙwazo bayan jagorantar tawagar ƙasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi.
Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Verde na cikin masu gogayyar lashe ƙungiya mafi hazaƙa a shekarar, tare da Morocco wadda a baya-bayan nan ta lashe kofin duniya na gasar ƙwallon ƙafa ta ƴan ƙasa da shekara 20.
Ƴanwasa mata na Najeriya Esther Okoronkwo da Rasheedat Ajibade na cikin waɗanda ke neman lashe kyautar zakarun ƴanwasa mata na Afirka na wannan shekarar.
Ya zuwa yanzu dai hukumar Caf ba ta bayyana ranar da za a yi bikin bayar da kyautar ba.
Ƴanwasan da ke takarar lashe zakarun Afirka na shekara ta 2025 - Maza
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan wasa mafi ƙwazo: Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli da Kamaru), Denis Bouanga (Los Angeles FC da Gabon), Serhou Guirassy (Borussia Dortmund da Guinea), Achraf Hakimi (Paris St-Germain da Moroko), Oussama Lamlioui (Renaissance Berkane), Fiston Mayele (Pyramids da DR Congo), Iliman Ndiaye (Everton da Senegal), Victor Osimhen (Galatasaray da Nigeria), Mohamed Salah (Liverpool da Masar), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur da Senegal).
Mai tsaron raga na maza: Yassine Bounou (Al Hilal da Moroko), Aymen Dahmen (CS Sfaxien da Tunisia), Marc Diouf (TP Mazembe da Senegal), Edouard Mendy (Al-Ahli da Senegal), Munir Mohamedi (RS Berkane da Moroko), Stanley Nwabali (Chippa Utd da Najeriya), Andre Onana (Trabzonspor da Kamaru), Ahmed El Shenawy (Pyramids da Masar), Vozinha (Chaves da Cape Verde), Ronwen Williams (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu).
Mai horas da ƙungiyar maza: Bubista (Cape Verde), Moine Chaabani (Renaissance Berkane), Hossam Hassan (Masar), Krunoslav Jurcic (Pyramids), Mohamed Ouahbi (Moroko U20), Romuald Rakotondrabe (Madagascar), Walid Regragui (Moroko), Tarik Sektioui (Moroko U23), Pape Thiaw (Senegal), Sami Trabelsi (Tunisia).
Tawagar maza: Algeria, Cape Verde, Masar, Ghana, Ivory Coast, Moroko, Moroko U20, Senegal, Afirka ta Kudu, Tunisia.
Za ku iya ganin cikakken jerin waɗanda ke neman lashe kyautukan a shafin hukumar Caf.
Ƴanwasan da ke takarar lashe zakarun Afirka na shekara ta 2025 - Mata
Ƴar wasa mafi ƙwazo: Rasheedat Ajibade (Paris St-Germain da Najeriya), Barbra Banda (Orlando Pride da Zambia), Portia Boakye (Hapoel Petah Tikva da Ghana), Tabitha Chawinga (Lyon da Malawi), Temwa Chawinga (Kansas City da Malawi), Ghizlaine Chebbak (Al Hilal da Moroko), Mama Diop (Strasbourg da Senegal), Rachael Kundananji (Bay FC da Zambia), Sanaa Mssoudy (AS FAR da Moroko), Esther Okoronkwo (AFC Toronto da Najeriya).
Mai tsaron raga na mace: Sedilame Boseja (Mamelodi Sundowns da Botswana), Andile Dlamini (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu), Habiba Emad (FC Masar da Masar), Khadija Er-Rmichi (AS FAR da Moroko), Fatoumata Karantao (MUSFAS Bamako da Mali), Cynthia Konlan (Swieqi United da Ghana), Adji Ndiaye (AS Bambey da Senegal), Fideline Ndoy (TP Mazembe da DR Congo), Chloe N'Gazi (Marseille da Algeria), Chiamaka Nnadozie (Brighton & Hove Albion da Najeriya).
Mai horas da ƙungiyar mata: Genoveva Anonman (15 de Agosto), Kim Bjorkegren (Ghana), Lamia Boumehdi (TP Mazembe), Desiree Ellis (Afirka ta Kudu), Carol Kanyemba (Zambia U17), Adelaide Koudougnon (Ivory Coast U17), Justin Madugu (Najeriya), Bankole Olowookere (Najeriya U17), Siaka Gigi Traore (ASEC Mimosas), Jorge Vilda (Moroko).
Tawagar mata: Kamaru U17, Ghana, Ivory Coast U17, Mali, Morocco, Najeriya, Najeriya U17, Afirka ta Kudu, Tanzania, Zambia U17.
Za ku iya ganin cikakken jerin waɗanda ke neman lashe kyautukan a shafin hukuma Caf.











