Dalilai biyar da ke hana Super Eagles cin manyan wasanninta

Ƴan wasan

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta yi rashin narasa a wasan cike gurbi na zuwa Gasar Kofin Duniya tsakaninta da DR Kongo, ƴan ƙasar ke ta bayyana rashin jin daɗinsu.

Super Eagles ta yi rashin nasara ne a wasan a bugun fenareti bayan da aka tashi wasan 1-1.

Rashin nasarar Najeriya ya jefa wasu ƴanƙasar da dama - masu bibiyar wasannin - cikin takaici.

Inda suke zargin ƙungiyar da rashin taɓuka abin kirki a manyan wasanni masu muhimmanci ga ƙasar.

Lokuta uku na baya-baya da Najeriya ta yi rashin nasawa

Wasu ƴan ƙasar na zargin cewa Super Eagles kan fara wasa da nasara, domin jan hankalin ƴan ƙasar, sai kuma daga baya su karya musu zuciya.

A lokuta da dama idan tawagar ƙasar za ta soma wata gasa, wasu ƴan ƙasar da dama za su nuna rashin goyon bayan tawagar ƙasar.

Amma bayan fara samun nasara a wasannin farko na gasar sai hankalin mutane ya koma kan ƙungiyar, lamarin da ke sa idan ta yi rashin nasara yake baƙanta wa magoya baya rai.

  • Wasan ƙarshe na Gasar AFCON 2023

Tawagar Najeriya ta taka rawar gani a gasar AFCON ta 2023 da aka yi a ƙasar Ivory Coast, inda ta yi ta samun nasara a wasannin gasar, lamarin da ya ja hankalin ƴan ƙasar da dama suka goyi bayanta.

Amma kuma muryar magoya bayan ta koma ciki a wasan ƙarshe na gasar, bayan da ta yi rashin narasa a hannun Ivory Coast a wasan.

  • Wasan Neman gurbin Kofin Duniya 2026

A lokacin da aka sanya Najeriya cikin rukuni guda da Benin da Afirka ta Kudu da.... a wasannin neman gurbin zuwa Gasar Kofin Duniya, magoya bayan ƙwallon ƙafa a ƙasar sun yi zaton cewa ƙasar za ta kai bantenta.

To amma fatan mgoya bayan ya dusashe bayan da ta ƙare a mataki na biyu a rukunin, lamarin da ya sa ta je gasar wasannin cike gurbi na Afirka.

  • Wasannin cike gurbi na Kofin Duniya 2026

A lokacin da aka sanya Najeriya cikin ƙasashen Kamaru da Gabon da DR Kongo domin buga gasar da nufin fitar da ƙasa ɗaya, wasu ƴan ƙasar da dama sun nuna sarewarsu.

To amma nasarar da Super Eagles ɗin ta samu a wasanta da Gabon, ya sa magoya bayanta, sun ɗan samu fata, to amma sai DR Kongo ta cinyeta a wasan ƙarshe na gasar

ƴan wasa

Asalin hoton, Getty Images

Mece ce matsalar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin manufa mai ƙarfi daga masu horaswa.

Anas Sani Tukuntawa wani ɗan jarida mai sharhi kan al'amuran wasanni ya ce matsalar tana farawa ne daga ranar da aka ɗauki mai horaswa.

''Galibin masu horaswar da Najeriya ke ɗauka a baya-bayan nan alƙawarin da suke yi shi ne kai tawagar wasan ƙarshe, maimakon ɗaukar kofi'', in ji shi.

Ya ci ya kamata NFF ta faɗa musu cewa kofi muke so ku ɗauka ba kai mu wasan ƙarshe ba.

''Haka aka yi wa Eric Tenhag lokacin da ya je Manchester United, aka ce so ake ya ɗauki Premier, amma sai ya ba zai iya ɗaukar Premier ba, amma zai ɗauki kofin League Cup, kuma sai da a ɗauka'', in ji shi.

  • Raina wasu ƙasashen

Zaharadden Sale, Shugaban Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta ƙasa reshen jihar Kano ya ce wata matsalar ita ce raina ƙasashen da aka haɗa su domin buga wasanni.

''Idan ka duba ƙasahen da tun farko aka haɗa Najeriya a wasannin rukuni na shafe fagen, Afirka ta Kudu da Benin da kuma Zimbabwe duka ta raina su, wannan ya sa ƙasar ta kasa mayar da hankali a kai'', in ji shi.

  • Ƴan wasan na fifita ƙungiyoyinsu

Shugaban ƙungiyar marubata labaran wasannin ya ce wani dalilin kuma shi ne ƴan wasan na kaffa-kaffa ne domin kada su samu rauni hakan kuma ya shafi ƙungiyoyinsu na waje.

''Wannan yana sa ba sa buga wasan da jikinsu, saboda tsoron rauni'', in ji shi.

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

  • Dogaro da ɗan wasa ɗaya

Anas Tukuntawa ya ce wani dalilin shi ne yadda ƴanwasan ke mayar da dogara da Victor Osimhen.

''Za ka idan Osimhen na ciki kowa ya dage, ama da zarar an cire shi sai duka jikinsu ya yi sanyi'', in ji shi.

Ya ce ya kamata ƴan mai horaswa ya faɗa musu cewa dole su yi wasa ko ba Osimhen a cikin fili.

  • Fifita masu taka leda a waje

Mai sharhin wasannin ya ce ɗaya daga cikin matsalolin da tawagar ke samu shi ne fifita masu taka leda a kan na cikin gida.

''Kusan duka ƴan tawagar masu taka leda a waje ne, idan ana tsormawa da ƴan cikin gida su sauran za su gane akwai ƙalubale a gabansu'', in ji Tukuntawa.

Ya ci gaba da cewa mafi yawan masu taka leda a wajen ba su da kishi, ƙungiyar sosai.