Mutanen da ambaliya ta kashe a jihar Neja sun kai 230 sannan ana neman 400

Lokacin karatu: Minti 5

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Neja ya ƙaru zuwa 230 yayin da har yanzu ake neman sama da mutum 400, a cewar Mataimakin shugban ƙaramar hukumar Mokwa, Musa Kimboku.

Mataimakin shugban ƙaramar hukumar ya faɗa wa BBC cewa ana ci gaba da aikin tona ƙasa domin neman mutanen da ake tunanin ƙasa ta binne su.

Ya ce hakan ya taimaka wajen rage warin da yake tashi a yankin saboda gawarwaki.

Ana kallon ambaliyar a matsayin mafi muni cikin shekara 50 da aka taɓa gani a Najeriya, wadda ta zarta ta birnin Maiduguri a watan Satumban 2024.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta sanar da cewa kawo yanzu ambaliyar ta raba mutum fiye da 3,000 da gidajensu sannan ta lalata ɗaruruwan gidaje.

Wasu da abun ya shafa sun shaida wa BBC cewa ambaliyar ta fara da daddare ne a lokacin da jama'a ke barci wani abu da ya sa ruwan ya tafi da mutane da dama.

Tuni dai shugaba Tinubu ya umarci hukumar NEMA da ta kafa sansani domin tsugunar da waɗanda ambaliyar ta ɗiɗaita.

A ranar Laraba da daddare ne wata ambaliya ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja, inda ta yi sanadiyar rayuka da dama tare kuma da lalata gidaje.

Lamarin ya ɗimauta mutanen yankin saboda irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon dare ana tafka mamakon ruwan sama, wanda daga bisani ya janyo ambaliyar.

"Abin babu daɗin gani, wannan babban iftila'i ne. Mun samu gawawwaki da dama yashe a ƙasa," kamar yadda mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ya shaida wa BBC bayan ziyarar gani da ido da suka kai garin.

Ya ce lamarin ya ɗaiɗaita mutane da dama kuma yanzu suna zaman mafaka cikin makarantu.

"Ruwan ya yi ɓarna sosai a anguwannin Tifin Maza da Hausawa," in ji mataimakin gwamnan.

'Mutum 200 ne suka mutu'

Mataimakin gwamnan na jihar Neja ya ce mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar sun kai sama da 151.

Ya ce sun samu nasarar gano gawawwaki 151 zuwa yanzu.

"Na ga wasu gawawwaki 31 a garin Raba, ruwa ya kwace gadar da ta haɗa garin da Mokwa. Gidaje masu ɗimbin yawa sun rushe a wannan garin," a cewar kwamred Yakubu.

Sai dai BBC ta gano cewa mutum sama da 200 ne suka mutu zuwa yanzu.

Rahoton da hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Nsema ta fitar, ta ce ambaliyar ta shafi magidanta sama da 500, waɗanda al'ummominsu suka kai mutum 3,000.

An ruwaito cewa wasu iyalai sun rasa ƴan uwa biyu zuwa biyar ciki har da yara ƙanana.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa alkaluman waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa bayan da ruwa ya tafi da wasu zuwa cikin kogin Neja.

Ana neman sama da mutum 400

Har ila yau, mataimakin gwamnan na jihar Neja, Kwamred Yakubu Garba, ya ce baya ga mutanen da suka mutu, akwai wasu da dama da ba a gansu ba.

"Waɗanda suka ɓace ba a ga gawawwakinsu ba aƙalla sun fi mutum 400, ba mu san inda suke ba saboda ana ci gaba da nemansu," in ji Yakubu.

"Mun je asibiti mun ga mutane da dama da suka samu raunuka suna karɓan magani.

Ya ce tuni gwamnatin jihar Neja ta kafa tantuna domin kula da mutanen da iftila'in ya faɗa wa, inda aka kai musu abinci da magunguna yayin da ita ma gwamnatin tarayya ta kai abinci da tabarmai da kuma barguna.

'Ban taɓa ganin irin wannan ambaliya ba tun da aka haife ni'

Mai anguwar garin na Mokwa, Muhammad Aliyu Shaba, ya ce bai taɓa ganin irin ambaliyar da aka yi ba tun da aka haife sa.

"Kawai mun tashi da safe babu abin da muke iya gani sai ruwa na tafiya da gidaje," in ji Aliyu.

Ya ce duka hanyoyin garin sun lalace, wanda hakan na janyo cikas wajen aikin ceto.

Shi ma wani mazaunin yankin, mai suna Abubakar Isa, ya bayyana cewa lamarin ya fi karfinsu.

"Wannan babban al'amari ne, ya fi karfin mu babu abin da za mu iya yi," in ji shi.

Ya ce bai taɓa ganin irin ambaliyar ba a tsawon rayuwarsa.

Ya ƙara da cewa sun tashi da safe mutane sun fara harkokinsu, wasu ma har sun tafi gonakinsu - kawai sai ruwa ya fara malala.

"Kwatsam muka fara ganin ruwa na shiga gidajenmu, mutane da dama sun mutu - mutane sun rasa ɗaukacin amfanin gona da suka adana.

Tun da farko dai, hukumomi sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun ambaliya a aƙalla jihohi 15 cikin 36 na faɗin Najeriya.