Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya ta tilastawa Amarya da Ango zuwa wajen bikinsu a cikin tukunya a India
Hotunan wasu ma'aurata zaune a cikin tukunyar girki kan ruwa na ratsa tittuna da ambaliya ta shafa domin isa wajen bikinsu a gabashin India ya ja hankalin mutane.
Amarya da Angonta sun yanke hukuncin isa wajen bikinsu ne ta wannan hanya sakamakon ambaliyar ruwa da ta malale ko ina a yankinsu.
Akash da Aishwarya sun lashi takobin tabbatuwar aurensu duk da cewa kauyensu na Thalavady a jihar Kerala ya cika maƙil da ruwa a ranar Litinin.
Hotunansu da aka karaɗe shafukan sada zumunta na nuna yada mutanen biyu wadanda duk ma'aikatan lafiya ne zaune cikin tukunyar su na fara'a.
Ruwan sama mai karfi a yankin Kerala ya haifar da ambaliyar ruwa da sanadin rayuka da zabtarewar kasa.
Rafuna sun cika sun batse haka zalika gadoji da manyan tittuna sun lalace - a wasu sassan kauyuka duk sun ɗaiɗaita.
An tsara gudanar da bikin Akash da Aishwarya a wani karamin wajen bauta da ke halavady, sai dai ambaliyar ta shafi wani ɓangare na wajen taron bikin.
Amaryar da Angonta sun aro tukunyar karfe ne daga wani karamin wajen bauta suka kuma nemi taimakon wasu maza su rinƙa jansu har zuwa wajen bikin nasu.
"Ya kasance bikin da ba zamu taɓa mantawa da shi ba," a cewar amaryar, Aishwarya, lokacin tattaunawarta da tashar Asianet.
Sabbin ma'auratan sun ce da fari sun tsara gudanar da bikinsu da karamin taron mutane kalilan, sai dai yanayin da bikin ya riske su da hotunan da aka rinƙa yaɗawa komai ya sauya domin ranar ta kasance wadda ba za su taɓa mantawa da shi ba a tarihi.
Akash ya ce sun jima da tsayar da ranar bikin nasu don haka ba za su ɗage ranar ba duk da cewa ya zo musu cikin ambaliyar ruwa.
Ya kara da cewa tukunyar girki ta kasance zabi na karshe a garesu don isa wajen bikin.