Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu biyar da suka fi jan hankali game da mummunar ambaliya a Maiduguri
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Bayan abubuwan da hukumomi a Najeriya suka tabbatar da faruwarsu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri na jihar Borno, akwai waɗanda ba a sani ba da kuma waɗanda aka yi hasashe.
Zuwa yanzu hukumar ba da agaji ta ƙasa Nema ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 37, yayin da gwamnatin jihar ta ce sama da mutum miliyan ɗaya lamarin ya shafa.
Wannan ce ambaliya mafi muni da jihar ta gani cikin shekara 30 bayan faruwar makamanciyarta lokacin da madatsar ruwa ta Alau ta ɓalle a watan Satumban shekarar 1994.
A wannan karon ma, ɗaya daga cikin makwararar kogin na Alau ce ta ɓalle sakamakon tumbatsar da ya yi saboda mamakon ruwan sama a ranar Litinin da tsakar dare.
Mun duba wasu abubuwa da suka fi jan hankali a jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Bazamar dabbobi masu haɗari daga gidan zoo
Gidan ajiyar namun daji na Sanda Kyarimi Park Zoo na ɗaya daga cikin wurare na musamman da ruwa ya antaya tare da wanke kayayyaki, ciki har da dabbobin gidan kansu.
Wata sanarwa da gidan zoo ɗin ya fitar ranar Talata ta ce ruwan ya kashe sama da kashi 80 cikin 100 na dabbobin, waɗanda suka haɗa da zakuna, da kada, da jimuna.
"Akwai kuma wasu dabbobi masu haɗari da ruwan ya janye zuwa unguwanninmu kamar macizai, da kada," in ji sanarwar, tana mai shawartar mazauna birnin su kula da kyau.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu wani rahoto game da ɓarna da waɗannan dabbobi suka yi.
Da gaske fursunoni sun gudu daga gidan yari?
Wani mazaunin birnin Maiduguri ya shaida wa BBC yadda ruwa ya mamaye babban gidan yari na birnin.
"Yanzu haka ina tsaye a bakin babban gidan yari na Maiduguri, ga shi nan ruwa iya kallonka kuma sai ƙaruwa yake yi," in ji shi. Motoci duk sun maƙale. Wasu ma da rigunan barcinsu suka fita kan tituna."
Jim kaɗan bayan haka wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito cewa sama da fursunoni 200 ne suka tsere daga gidan yarin mai matsakaicin tsaro.
Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta tabbatar da cewa ta fara aikin kwashe tsararrun zuwa wani wurin daban amma ba ta musanta ko tabbatar da guduwarsu ba.
Kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton hukumar ta Nigerian Correctional Service ba ta sake bayar da wani ƙarin bayani ba game da lamarin.
Kashim Shettima tsamo-tsamo a fadar Shehun Borno
Wani muhimmin wuri da ya kurɓi ruwan kogin nan shi ne fadar Shehun Borno Abubakar Umar-Ibn Garbai.
Hotuna da bidiyon da aka ɗauka sun nuna yadda ruwan ya mamaye gaba da kuma kewayen ginin daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima yake kai ziyarar jaje.
Haka nan, an ga mataimakin shugaban ƙasar yana tafiya a cikin ruwan da ya shanye kusan tsawon ƙafarsa gaba ɗaya lokacin da yake shiga fadar.
"Za mu ɗauki dukkan matakan da suka dace domin ganin mun share hawayenku," a cewarsa yayin da yake yi wa mutanen da suka taru a jihar tasa jawabi.
Annoba tsakanin 'yan gudun hijira
Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar cutar kwalara a wani sansanin ƴan gudun hijira na gaggawa da aka buɗe a Maiduguri.
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta buɗe sansanin Bakassi domin tsugunarwa da kuma tallafa wa mutanen da suka rasa muhallansu.
Cikin wani rahoto da ofishin hukumar kula da ayyukan jin-ƙai na MDD (OCHA) ya fitar, ya ce abubuwan da mutanen suke buƙata a yanzu su ne abinci, da matsuguni da kuma tsaftataccen ruwan sha.
Sanarwar ta ƙara da cewa ruwan da ake sha a yanzu ya gurɓata, kuma zai iya janyo ɓarkewar cutuka kamar amai da gudawa wato kwalara. "Rashin tsaftataccen ruwan sha barazana ne ga ƙananan yara, tsofaffi da kuma masu buƙata ta musamman," in ji hukumar.
Rahoton na MDD ya ce kafin ambaliya ta baya-bayan nan, sama da mutum 123,000 ne ambaliyar ta shafa a Maiduguri tun watan Agusta, inda ta ce ta kuma lalata ababen more rayuwa da kuma ƙara barazanar ɓarkewar cutuka a sansanonin da suka cika da ƴan gudun hijira.
Ƙarin ruwan sama
Yayin da ake ci gaba da alhinin wannan bala'i, hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen ƙarin tsawa da ruwan sama tsawon kwana uku a faɗin ƙasar, ciki har da jihar ta Borno.
A wata sanarwa kan yanayi da hukumar ta fitar ranar Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Borno, da Adamawa, da Taraba, da Yobe, da Katsina, da Sokoto, da kuma Kaduna a ranar Laraba.
NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu ɓangarorin jihohoin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.
Hukumar ta kuma ce za a samu iska mai ƙarfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama'a da su ɗauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.
Hukumar Nema ta ce ambaliya ta kashe aƙalla mutum 229 a Najeriya zuwa yanzu tun daga farkon 2024.