'Zan yi tafiyar kilomita 500 don na kaɗa ƙuri'a'

Fajr Sulaimana ta shaida wa BBC cewa za ta yi tafiyar kilomita 500 daga Kumasi zuwa Walewale don yin zabe a karon farko.
Bayanan hoto, Fajr Sulaimana na daga cikin matasan Ghana da za su yi zabe a karon farko a 2024
    • Marubuci, Haruna Shehu Tangaza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Kumasi, Ghana
  • Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasar Ghana, wani rukunin masu zaɓe da ba a cika mayar da hankali kansu ba, amma kuma suka ƙagara su ga ranar zaɓen su ne matasa waɗanda za su jefa ƙuri’a a karon farko.

Kimanin matasa 850,000 ne za su jefa ƙuri’a a zaɓen na bana kuma ana ganin ƙuri’unsu za su iya yin tasiri wajen yanke hukuncin wanda zai shugabancin ƙasar a shekaru huɗu masu zuwa.

Daga cikin irin waannan matasa akwai waɗanda za su yi tafiya mai nisa zuwa garuruwansu, amma duk da haka suna ganin cewa hakan ne abin da ya fi dacewa.

Matashiya Fajr Suialimana ta shaida wa BBC cewa za ta yi tafiya ta tsawon kilomita 500 daga birnin Kumasi zuwa inda za ta kada ƙuri'a.

Sai dai duk da yake zumuɗinsu game da jefa ƙuri’a a karon farko a rayuwarsu kusan iri ɗaya ne, dalilansu na yankan katin zaɓe don jefa ƙuri’arsu takan sha bamban daga wannan mutum zuwa wancan.

Sai dai kuma akwai inda ra'ayoyinsu suka haɗu, wato batun samun aikin yi ga matasa.

Abduljaleel Salis matashi ne ɗan shekaru 21 da haihuwa, yana cikin matasan da za su jefa ƙuria a karon farko a bana ya ce: “Akwai jin daɗi ganin cewa ni zan je in yi zaɓen domin ɗora shugaban da zai kawo wa ƙasa ci gaba.

Domin idan kana son samun shugaban da zai yi maka abin da kake so, to dole kai ma sai ka je ka yi zaɓe.”

Babban abin da Abduljalal ke son Shugaban ya zaba ya mayar da hankali a kai shi ne samar da ayukkan-yi ga matsala, yana mai karawa da cewa lokaci ya yi da ya kamata ya samu abin-yi don daina dogaro kan iyaye da yayyensa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamar Abduljaleel, Ita ma Aisha Mohammed matashiya yar shekaru 19 ta ce tana cike da farin cikin cewa za ta yi zabe a karon farko a rayuwarta tare da bayyana jin daɗi na shiga a dama a da ita a wannan zaɓen.

“Idan ba ka yi zabe ba, ba ka da bakin magana idan shugaban da aka zaɓa ya yi abin da ba daidai ba.” In ji ta.

Akan ce karkacen wani daidan wani, ita kuwa matashiya Saratu Mahmud mai shekara 20 za ta jefa ƙuri’a ne don ta samu muryar neman akawo ƙarshen tsarin bayar da ilmin Sakandare Kyauta.

A cewarta, tsarin na bayar ilmi kyauta ya janyo yanzu ana komai na karatun kara-zube ba tare da bin tsari ba.

Abin da ya fi damun ta shi ne yadda ake bari ɗalibai mata da suka yi ciki ci gaba da zuwa makaranta a yanzu saɓanin a baya:

“Kafin tsarin na bayar da ilimi kyauta, ba a bari ‘yan matan da suka yi ciki su ci gaba da zuwa makaranta, amma yanzu ana bari. Sai ya zamana kowa na abin da yake so abin da ya sa yanzu ɗalibai mata ke ɗaukar ciki barkatai.”

A cewar alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar ta Ghana (EC), daga cikin masu zaɓen kimamin miliyan 18.7 da suka yanki katin jefa ƙuri'a a wannan zaɓen, fiye da dubu 850 matasa ne da za su jefa ƙuri’a a karon farko; kuma ana hasashen ƙuri’unsu ka iya yin tasiri mai ban-mamaki a wannan zaɓen.