'Yan takara 13 za su fafata a zaɓen Shugaban Ƙasar Ghana

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasan Ghana na fama da rashin aikin yi
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar zaben kasar Ghana ta amince da sunayen mutum goma sha uku, wadanda za su tsaya a takarar mukamin shugaban kasar a zaben da za a yi a ranar 7 ga watan Disamba mai zuwa.

Cikin 'yan takaran har da mataimakin shugaban kasar, Dokta Mahamudu Bawumia da tsohom shugaban kasar, John Mahama.

Da farko 'yan takara talatin da takwas ne suka nuna sha'awar tsayawa takarar, amma kuma goma sha uku ne suka tsallake.

'Yan kasar ta Ghana ba shugaban kasa kadai za su zaba a ranar 7 ga watan Disamba mai zuwa ba, akwai zaben 'yan majalisu, kuma a ranar 7 ga watan Junairun shekarar 2025 ne wa'adin mulkin shugaba Nana Akufo Addo ke karewa.

Ana sa ran za a yi zazzafar fafatawa tsakanin 'yan takarar, kasancewar tsohon shugaban kasar John Mahama mai shekara 65 ya sake dawowa zawarcin kujerar shugaban kasar.

Sai kuma mataimakin shugaban kasa na jam'iyya mai mulki Dokta Mahamudu Bawumia da ke son kafa tarihin yin wa'adin mulki a karo na biyu tun bayan Ghana ta ta koma turbar dimukuradiyya a shekarar 1992.

Sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasar sun hada da, tsohon ministan kasuwanci da zuba jari Alan John Kwadwo Kyerematen, wanda ya rikide ya zama dan takarar indifenda.

Nana Kwame Bediako, wanda shi ne karon farko da ya taba tsayawa takara, akwai mata 'yan takara guda biyu wato Nana Akosua Frimpomaa da Akua Donkor.

Dukkan 'yan takarar shugaban kasar, sun yi wa 'yan Ghana alkawura da dama, daga ciki akwai farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai babbar jam'iyyar adawa a Ghana ta nuna damuwa kan halin da hukumar zaben kasar ke ciki, inda ko a ranar Talata sai da ma'aikatan suka gudanar da zanga-zanga a daukacin kasar.

Duk da haka hukumar zaben ta tabbatar wa 'yan kasa za ta tabbatar an gyara da kauce wa duk wasu kura-kurai da ka iya tada zaune tsaye lokacin zaben.

Tuni kuma aka fara shirya tarukan wayar da kai da bai wa ma'aikata horo domin samun ingantaccen zabe.