Muhimman abubuwa bakwai da kuke buƙatar sani kan zaɓen shugaban ƙasar Ghana

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Damian Zane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Ghana na shirin zaɓar sabon shugaba a babban zaɓen ƙasar da ke tafe a watan Disamba - mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia, da tsohon shugaban ƙasar Johm Mahama, su ne ƴan takara na gaba-gaba da ake sa ran za su iya lashe zaɓen.
Nana Akufo-Addo, wanda aka fara zaɓa a 2016, na shirin kammala wa'adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.
Yaushe za a yi babban zaɓen?
A ranar Asabar 7 ga watan Disamba, al'ummar Ghana kusan miliyan 18.8 da suka yi rajistar kaɗa kuri'a ne za su fita rumfunan zaɓe domin yin zaɓe karo na tara a ƙasar tun bayan sake ɓullo da siyasar jam'iyyu da yawa a farkon shekarun 1990.
A cikin shekara 30 da suka wuce, ƙasar ta fuskanci fafatawa mai zafi a zaɓuka, amma waɗanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali da lumana. Ghana na da kima a idon ƙasashen duniya na yadda ta ke miƙa ragamar mulki cikin tsanaki tsakanin wata gwamnati zuwa wata.
Me ƴan Ghana za su zaɓa?
A ranar zaɓe, za a gudanar da zaɓe ne a matakai biyu:
- Shugaban ƙasa – Akwai ƴan takara 12
- Ƴan majalisa – masu zaɓe a mazaɓu 275 a faɗin ƙasar za su zaɓi ƴan majalisa.
Wane ne zai zama shugaban ƙasar Ghana na gaba?

Asalin hoton, AFP
Duk da cewa mutum 12 ne ke takarar kujerar ta shugaban ƙasa, mutum biyu ne ake hasashen suna da damar lashe zaɓen. Tun bayan komawar siyasar jam'iyyu da yawa a 1992, ƴan takara daga jam'iyyar National Democratic Congress (NDC) da kuma New Patriotic Party (NPP) ne kaɗai ke lashe zaɓen ƙasar.
Mutanen biyu da ke sahun gaba su ne:
- Mahamudu Bawumia (NPP) - Kasancewarsa mataimakin shugaba Akufo-Addo na tsawon shekara takwas, mai shekara 61 ɗin da ya karanci fannin tattalin arziki a Jami'ar Oxford zai kafa tarihin zama Musulmi na farko da ya lashe zaɓen shugaban kasar. Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin ƙasar ya yi fice saboda kwarewa da ya yi a harkokin kuɗi. Sai dai hakan kuma zai iya zama masa cikas yayin da yake fuskantar suka bayan da da Ghana ta faɗa cikin tsananin matsin tattalin arziki wanda ba a taɓa gani ba cikin shekaru lokacin jagorancinsa.
- John Mahama (NDC) – Samun nasara a wannan zaɓe zai kasance kamar sake komawa kan mulki ne gare shi mai shekara 65 ganin cewa ya taɓa zama shugaban ƙasa na shekara huɗu da rabi daga 2012, amma ya sha kaye a zaɓen 2016. A lokacin da yake ofishi, ana kiransa da "Mr Dumsor", saboda yawan ɗaukewar wutar lantarki a zamaninsa. A daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki, Mahama ya sha alwashin "kawo mafita" nan take ga ƙasar da ke buƙatar kwararren shugaba.
Cikin sauran ƴan takara da ke da magoya baya sun haɗa da:
- Nana Kwame Bediako – Ya kasance ɗan kasuwa, wanda aka fi sani da “Cheddar”, ba shi da wani tarihi a siyasa amma ya yi tasiri sosai a kafofin sadarwa na zamani kuma yana samun goyon baya daga wajen matasa.
- Alan Kyerematen – Tsohon ministan, wanda ake kira, “Alan Cash”, ya bar jam'iyyar NPP a shekarar da ta gabata bayan korafin rashin yi masa daidai a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da aka yi. Zai samu goyon bayan ƴan jam'iyyar NPP a yankin Ashanti.
Mene ne manyan batutuwa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Batun tattalin arziki ne sahun gaba da ke mutane ke nuna damuwa a kai gabanin zaɓen ƙasar, musamman tsadar rayuwa da ake fama da shi. A karshen 2022, hauhawar farashi ya kai kashi 54. Duk da cewa ya yi kasa tun bayan wancan lokaci, amma farashin kayayyaki na ci gaba da tashi cikin sauri.
Bankin Duniya ya ce ƴan Ghana 850,000 suka faɗa cikin talauci a 2022 saboda ƙaruwar farashin kayayyaki. Waɗannan "mutane" sun shiga jerin mutum miliyan shida waɗanda tuni ke fama da talauci a faɗin ƙasar.
A karshen 2022, kuɗaɗen da gwamnati ke samu sun ragu inda kaɗan ya rage wanda zai tallafawa kasafin kuɗin ƙasar, abin da ya tilastawa Ghana neman taimakon asusun bayar da lamuni na duniya (IMF).
Rashin aikin yi tsakanin matasa da kuma ɗimbin ƴan ƙasar da ke fita wajen neman rayuwa mai inganci na cikin manyan batutuwa a baya-bayan nan.
Jam'iyyar NDC ta ce "babu wani abin a zo a gani" a ƙasar kuma ta buƙaci kawo gyara cikin gaggawa.
Jam'iyyar NPP mai mulki ta ce ta gina tattalin arziki mai karfi kuma yana kan hanyar samun ci gaba, don haka ba lokaci ne na kawo sauyi ba.
Nuna damuwa kan tasirin haƙar zinare ba bisa ka'ida ba kan muhalli - Haƙar zinare wanda aka fi sani da "galamsey" a ƙasar - ya kasance cikin manyan batutuwa da ke tattaunawa. An yaba da jerin zanga-zangar adawa da haƙar zinare ba bisa ka'ida ba da mutane suka yi gabanin zaɓen, wanda ya janyo gurɓacewar koguna da dama.
Dukkan jam'iyyu sun amince cewa dole ne a shawo kan batun, amma yayin da jam'iyyar NPP ta ce hakan yana da muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar domin bai wa ƙananan masu haƙar zinare damar ci gaba da aikinsu, ita kuwa NDC na kiran saka tsauraran matakai da kuma takaita bayar da sabbin lasisi.
Ta yaya zaɓen zai yi aiki?

Asalin hoton, AFP
Domin samun nasarar zaɓen shugaban ƙasar a zagaye na farko, dole ne ɗan takara ya samu sama da rabin kuri'u da aka kaɗa. Idan babu ɗan takarar da ya samu abin da ake so, to za a je zagaye na biyu tsakanin ƴan takara biyu da suka fi samun kuri'a a karshen watan Disamba.
Ana yin nasara a zaɓen majalisar ne bisa tsarin wanda ya fi samun yawan magoya baya, inda kowane ɗan majalisa zai iya tsayawa takarar kuma ya yi nasara ko da a ce magoya bayansa ba su haura kashi 50 cikin 100 ba.
A ranar zaɓe, kowane mai kaɗa kuri'a zai tafi zuwa rumfar zaɓensa tare da katin zaɓe, inda za a tantance su ta hanyar duba yatsunsu da na'ura sannan a ba su takardar kaɗa kuri'a guda biyu. Za a saka wa kowane mutum da ya kaɗa kuri'arsa tawada a ɗan karamin yatsa domin kaucewa zaɓe sau biyu.
Me ya faru a zaɓukan da suka gabata?
Tun 1992, Ghana ta gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa masu zafi.
A 2008, ƙasa da rabin kashi ne ya raba 'yan takara biyu a zagaye na biyu.
A 2012, wanda ya lashe zaɓen, Mahama, ya samu kashi 50 na kuri'u a zagayen farko da kuri'u ƙasa da 80,000.
Hakan ya janyo kalubantar zaɓen daga jam’iyyar NPP, inda ta ce an tafka maguɗi a wasu rumfunan zaɓe. Jam'iyyar ba ta yi nasara ba, amma hakan ya janyo hukumar zaɓen ƙasar ɓullo da sabbin matakan tabbatar da gaskiya.
Masu sa ido kan zaɓe sun sha yaba wa yadda aka gudanar da zaɓen.
Yaushe za a samu sakamakon zaɓen?
Duba da zaɓuka da suka gabata, hukumar zaɓe za ta sanar da sakamakon zaɓen zuwa ranar 10 ga watan Disamban, 2024.










