Manyan ƴantakara biyu da suka gwara kan ƴan arewacin Ghana

Zaɓen Ghana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban kasar Ghana Muhamudu Bawumia da tsohon shugaban kasar John Mahama
    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, Accra, Ghana
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ƴan arewacin Ghana da aka fi sani da mutanen kan tudu sun shiga ruɗani da samun rabuwar kai dangane da mutumin da za su zaɓa a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi ranar Asabar, 7 ga watan Disamba.

Ƴantakara 12 ne ke fafatawa a zaɓen neman shugabancin ƙasar na 2024 domin maye gurbin shugaba Nana Akufo-Addo wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.

Sai dai kuma ana kallon fafatawar za ta fi zafi tsakanin tsohon shugaban ƙasar John Dramani Mahama na jam’iyyar adawa ta NDC da mataimakin shugaba mai ci, Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP, waɗanda dukkanin su sun fito ne daga ɓangare ɗaya wato arewaci ko kuma kan tudu kamar yadda ake faɗi a Ghana.

Wakilinmu Usman Minjibir ya yi mana duba dangane da al'amarin.

'Sun gwara mana kai'

Malam Sani Isiyaku wani mazaunin unguwar Nima da ke birnin na Accra wanda Bahaushe ne ya ce "wallahi ni ban san wa zan zaɓa ba tunda ni ba ni da jam'iyya ballantana na ce zan bi abin da jam'iyyata ta ce."

Kuma masana kimiyyar siyasa da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun jaddada tunanin da malam Sani yake da shi.

Musa Abdulmajid wani masanin kimiyyar siyasa ne a Ghana ya kuma shaida min cewa "wannan takara ta raba kan al'ummar Zango. Mutanen Zagonninmu idan ka shiga za ka ji yadda kowa yake yabon ɗantakararsa.

A baya dai jam'iyyar NDC ce take da ƙarfi a Zangonni amma tun bayan da Mahamudu Bawumia ya zama mataimakin shugaban ƙasa sai jam'iyyar NPP ta samu gindin zama a Zangonni." In ji Musa Abdulmajid.

Ya kuma ƙara da fito da batun addini wanda ya ce shi ma zai yi tasiri wajen raba gardama a tsakanin ƴantakarar guda biyu a tsakanin ƴan arewacin Ghana.

"Idan ka yi zancen Musulunci, Bawumia Musulmi ne amma kuma shi ma John Dramani ƙanensa wanda attajirin mai kuɗi ne Musulmi ne kuma yana da alaƙar kusa da al'ummar Zango", kamar yadda ya ce.

'Akwai yiwuwar zuwa zagaye na biyu'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bello Ɗan Rakiya wanda masanin kimiyyar siyasa ne ya ce sakamakon fitowar mutanen biyu daga yanki ɗaya da kuma sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi ya sa yanzu haka masu kuri'ar jin ra'ayin mutane ke hasashen cewa za a iya kai wa ga gudanar da zaɓe zagaye na biyu kasancewar bai zama lallai a samu zakara ba a fafatawa ta farko ba.

"Akwai wata ƙungiya da ake kira Global Info Analytics na Moussa Dakwa ya nuna jam'iyyar hamayya ta NDC ce za ta samu nasara inda za ta samu kaso 53 cikin ɗari na ƙuri'un da za a kaɗa.

To amma kuma shi ma wani Dr Smart ya gano cewa jam'iyya mai mulki ce ta NPP za ta lashe zaɓen da kaso 49 cikin 100 na ƙuri'un da za a kaɗa, inda ita kuma jam'iyyar NDC za ta samu kaso 47.

Wato shi wannan na nuna cewa ba za a samu wanda ya lashe zaɓen ba a karon farko har sai an kai ga zagaye na biyu tunda da ba za a samu wanda ya samu kaso fiye da 50 ba kamar yadda tsarin mulkin Ghana ya tanada." In ji Ɗan Rakiya.

John Dramani Mahma - NDC mai hamayya

Tsohon shugaban Ghana kuma ɗan takarar jam'iyyar adawa, John Dramani Mahma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Ghana kuma ɗan takarar jam'iyyar adawa, John Dramani Mahma

John Dramani Mahama ya taɓa zama shugaban Ghana a 2012, bayan rasuwar marigayi John Attah Mills.

Mahama ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa daga shekara ta 2009 zuwa 2012, lokacin ya tsaya takara aka kuma zaɓe su da marigayi shugaba John Attah Mills a karkashin jam`iyyarsu ta NDC.

Kodayake a ƙarshe ƙaddara ta sa ya ɗare karagar mulki a matsayin shugaban ƙasa, ana saura wata huɗu wa`adin mulkinsu ya cika, sakamakon rasuwar magabacinsa, wato shugaba John Attah Mills.

Sai dai a 2016 burinsa na tazarce ya samu naƙasu sakamakon shan kaye daga abokin karawarsa, Nana Addo Akufo wanda a yanzu haka yake wa'adinsa na biyu.

A 2020, John Dramani ya kuma fafatawa da Nana Akufo Addo wanda ke neman tazarce a lokacin, inda ya kuma kayar da John Dramani a karo na biyu.

Wannan ce takaran John Dramani Mahma ta neman zama shugaban ƙasar Ghana ta uku.

Ɗan takarar babbar jam'iyyar ta hamayya a Ghana, John Dramani Mahama, ya lashi takobin ɗaukar tsattsauran mataki kan matsalar cin hanci da rashawa idan ya yi nasara a zaɓen na watan Disamba.

Mista Mahama ƙwararre ne a harkar sadarwa, sannan masanin tarihi ne kuma marubuci ne.

An daɗe ana bugawa da shi a jam`iyyar NDC, kasancewar ya zama ɗan majalisar dokokin Ghana a ƙarkashin jam'iyyar har sau uku, wato daga 1997 zuwa 2009.

An haifi Dramani Mahma ne a watan Nuwamban 1958, a lardin Bole Bamboi da ke arewacin Ghana.

Mahaifin Dramani Mahama , wato Emmanuel Adama Mahama attajirin manomi ne, kuma ɗan siyasa da ya yi nasa zamanin tare da madugun siyasar jumhuriya ta farko a Ghana, Dr Kwame Nkurumah.

Mahamudu Bawumia - NPP mai mulki

Mataimakin shugaban Ghana kuma ɗan takara na jam'iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Ghana kuma ɗan takara na jam'iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia

Mahamudu Bawumia ya tashi daga ɗan siyasar da ba a san shi ba zuwa matakin mataimakin shugaban ƙasa a Ghana - kuma a watan Disamba zai iya kafa tarihin zama shugaban ƙasa Musulmi na farko a ƙasar.

Jam'iyyar New Patriotic (NPP) mai mulkin ƙasar Ghana ta zaɓi Bawumia, wanda a yanzu yake mataimakin shugaban ƙasa a matsayin ɗan takararta a babban zaɓe mai zuwa.

Magoyin bayan ƙungiyar Tottenham Hotspur ɗin mai shekaru 61, ya yi suna a ƙasar.

Shi haziƙi ne da ya yi karatu a jami'ar Oxford, ana kuma yawan ganin sa sanye da tabarau, kuma ana yi masa lakabi da "Mr Digital" saboda alƙawarin da ya yi na sauya Ghana zuwa ɓangaren fasaha.

Amma ganin cewa shi ne shugaban tawagar tattalin arziki na gwamnatin ƙasar, yawancin 'yan Ghana na danganta shi Bawumia da matsalar tsadar rayuwa da suke fuskanta.

"Mr Digital" ya shiga fagen siyasa a 2008, inda ya haifar da nishaɗi da kuma shakku.

Bawumia ɗan shekara 44 ne wanda bai taɓa riƙe muƙamin gwamnati ba, amma duk da haka Akufo-Addo - a lokacin ɗa yake takarar shugaban ƙasa - ya zaɓe shi a matsayin abokin takararsa.

Mahaifin Bawumia Alhaji ya yi aiki a gwamnatocin farko na Ghana bayan da ƙasar ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1957, inda ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Firaminista Kwame Nkrumah.

Amma Bawumia wanda ya karanci fannin tattalin arziki da kuma banki - ya zama mataimakin gwamnan babban bankin Ghana.

Sauran ƴantakara

  • Alan John Kwadwo Kyerematen – Independent Candidate
  • Christian Kwabena Andrews – Ghana Union Movement
  • Daniel Augustus Lartey Jnr – Great Consolidated Popular Party
  • George Twum-Barima-Adu – Independent Candidate
  • Nana Kwame Bediako – Independent Candidate
  • Hassan Abdulai Ayariga – All People’s Congress
  • Kofi Akpaloo – Liberal Party of Ghana
  • Mohammed Frimpong – National Democratic Party
  • Nana Akosua Frimpomaa – Convention People’s Party
  • Kofi Koranteng – Independent Candidate