Zaɓen Ghana: Wane ne ɗantakarar shugabancin Ghana Mahamudu Bawumia?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 6
Mahamudu Bawumia ya tashi daga ɗan siyasa da ba a san shi ba zuwa matakin matamakin shugaban ƙasa a Ghana - kuma a watan Disamba zai iya kafa tarihin zama shugaban ƙasa Musulmi na farko a ƙasar.
Jam'iyyar New Patriotic (NPP) mai mulkin ƙasar Ghana ta zaɓi Bawumia, wanda a yanzu yake mataimakin shugaban ƙasa a matsayin ɗan takararta a babban zaɓe mai zuwa.
Magoyin bayan ƙungiyar Tottenham Hotspur ɗin mai shekaru 61, ya yi suna a ƙasar.
Shi haziki ne da ya yi karatu a jami'ar Oxford, ana kuma yawan ganinsa sanye da tabarau, kuma ana yi masa lakabi da "Mr Digital" saboda alkawarin da ya yi na sauya Ghana zuwa ɓangaren fasaha.
Amma ganin cewa shi ne shugaban tawagar tattalin arziki na gwamnatin ƙasar, yawancin 'yan Ghana na danganta shi Bawumia da matsalar tsadar rayuwa da suke fuskanta.
Idan Bawumia ya shawo kan sukar da ake yi masa ya kuma lashe zaɓe, zai maye gurbin shugaban ƙasar na yanzu Nana Akufo-Addo, wanda ke dab da kammala wa'adin mulkinsa na biyu.
"Mr Digital" ya shiga fagen siyasa a 2008, inda ya haifar da nishaɗi da kuma shakku.
Bawumia ɗan shekara 44 ne wanda bai taɓa riƙe muƙamin gwamnati ba, amma duk da haka Akufo-Addo - a lokacin ɗa yake takarar shugaban ƙasa - ya zaɓe shi a matsayin abokin takararsa.
Mahaifin Bawumia Alhaji ya yi aiki a gwamnatocin farko na Ghana bayan da ƙasar ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1957, inda ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Firaminista Kwame Nkrumah.
Amma Bawumia wanda ya karanci fannin tattalin arziki da kuma banki - ya zama mataimakin gwamnan babban bankin Ghana.
A wajen masu sharhi da dama da kuma nawasu a cikin jam’iyyar NPP, bai dace Akufo-Addo ya ɗauki Bawumia mataimakin shugaban ƙasa a kan sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Akufo-Addo dai ya sha kaye a zaɓen a hannun John Atta Mills na jam'iyyar NDC da ƴar tazara.
Bawumia ya yi rashin nasara a mataimakin shugaban ƙasa da aka ɗauke shi - amma kamfen ɗin sa na kwarjini ya rufe bakin yawancin masu sukarsa.
"Ya kori kamfen na NPP. Ina ganin babu wanda zai iya yin aiki mafi kyau, dangane da goyon bayan da ya bai wa NPP," kamar yadda masanin kimiyyar siyasa na Ghana Dr Clement Sefa-Nyarko ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, Mahamudu Bawumia
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akufo-Addo da Bawumia sun sake shiga takarar zaɓe a 2012. Sai dai, sun sake yin rashin nasara.
Jam'iyyar NPP ta kalubalanci sakamakon zaɓen a kotun koli, inda suka zaɓi Bawumia a matsayin babban shaidarsu.
Yayin zaman kotun, wanda aka watsa a gidan talabijin ɗin ƙasar, Bawumia ya bayyana ba tare da wata razana ba.
"Mutane sun yi ta tambaya, wanene wannan mutumi? Shi ne mutuminsa da suka nunawa goyon baya," a cewar Dr Sefa Nyarko, wanda malami ne a King's College da ke birnin Landan, da ke bayar da darussa kan shugabanci a Afrika.
Akufo-Addo ya yanke shawarar ci gaba da ɗaukar Bawumia a matsayin mataimakinsa, kuma a 2016, a takararsu ta uku, jam'iyyar NPP ta lashe zaɓe da kashi 51.3. Daga karshe, Bawumia ya zama mataimakin shugaban ƙasa.
Bawumia ya fara gwagwarmaya ne tun a 1963, lokacin da aka haifesa cikin wani babban iyali a birnin Tamale da ke arewacin Ghana.
Shi ne yaro na 12 cikin ƴaƴan mahaifinsa 18. Matansa kuma nawa?
Bayan kammala makarantar firamare da kuma sakandari a Ghana, Bawumia ya tafi zuwa Birtaniya domin yin karatun digiri, inda daga nan ya zarce da karatun digiri na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami'ar Oxford.
Ya shiga aikin tasi da kuma mai share-share domin tallafawa karatunsa.
Ya koma Ghana a shekara ta 2000 domin yin aiki a babban bankin ƙasar, inda ya zarce har zuwa matakin mataimakin gwamnan bankin.

Asalin hoton, AFP
Bawumia ya yi kamfen a kan sanin tattalin arziki da ya yi a lokacin da yake ƙoƙarin zama mataimakin shugaban ƙasa.
Don haka, ya fuskanci suka sosai a lokacin da Ghana ta faɗa cikin matsin tattalin arziki mafi muni a cikin shekarun karakashin jagorancinsa.
Hauhawar farashi ya kai kashi 54 cikin 100 a cikin Disamba 2022 kuma lamarin ya tilasta wa ƙasar ciyo bashi na dala biliyan 3 daga asusun ba da lamuni na duniya (IMF) bayan da bashin da ake bin gwamnati ya ƙaru.
Da yake mayar da martani kan sukar, Bawumia ya ce ƙungiyar kula da tattalin arzikin da yake shugabanta, ba ta da"hurumin ɗaukar mataki" kuma shawara kaɗai take bai wa gwamnati.
Amma ga mutane da yawa, hakan bai kamata.
"Game da hali, da mutunci, mutane sun fara tambayar kansu: 'Mene ne wannan? Ta yaya aka zo nan? Mun yi tunanin kai ne mafi kyawun mutum, kuma dubi inda muka zo', " in ji Franklin Cudjoe, wani mai sharhi kan harkokin siyasa ɗan ƙasar Ghana kuma shugaban cibiyar mai suna Imani, a tattaunawarsa da BBC.
A matsayinsa na masanin tattalin arziki, Bawumia ya kuma yi suna kasancewarsa mai hankoron ganin an samu sauyi na zamani.
Ghana ta samu ci gaba sosai a harkokin fasaha da kuma sadarwa na zamani, musamman a fannoni kamar na wayar salula, kamar yadda Charles Abani, shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a Ghana, ya bayyana a watan da ya gabata.
Bawumia ne ya jagoranci wannan ci gaba da aka samu, in ji jaridar African Business, yayin da jaridar The Chronicle kuma ta yaba wa Bawumia da "kwarewar tsarin zamani" da yake da ita.
Bawumia ya ce ya kaddamar da wani shirin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin Ghana da kamfanin Zipline na ƙasar Amurka, wanda ya kai ga samar da babbar hanyar bayar da allurar riga-kafi a duniya.
Ya ce ya tuntuɓi Zipline da ke amfani da jirage marasa matuki wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya zuwa asibitocin da ke da wuyar isa, bayan mahaifinsa ya mutu sakamakon zubar jini.
Ko da yake wasu na murna da zimmar fasaha da yake da ita, wasu kuwa suna nuna shakku.
Mista Cudjoe ya ce Bawumia na yin kamfen ne kan tsarin fasaha na zamani maimakon fuskantar muhawara kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.
Mista Cudjoe ya ce "Ko Bawumia na kan mulki ko a'a, dole ne a yi amfani da tsarin zamani a ƙasar nan saboda mun riga mun fara shi."
Dr Sefa-Nyarko ya yi magana kan Bawumia inda ya ce: "Abin da ya samu nasara a kai shi ne aika wa da kuma iƙirarin kawo ci gaba na zamani na gwamnati mai ci."

Asalin hoton, Mahamudu Bawumia
Rayuwar Bawumia ta kasance mai karfi a yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa. Matarsa Samira, da suka shafe tsawon shekara 20 tare, tsohuwar sarauniyar kyau ce wadda ake sha'awar kwalliyarta.
Ita ma uwargidrsa ta yi suna idan aka zo ɓnagaren siyasar jam’iyya – kuma ta shiga rangadin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar NPP.
Ma'auratan suna da 'ya'ya hudu. Su mabiya addinin Musulunci ne - addinin da kusan mutum ɗaya cikin biyar na 'yan Ghana ke bi.
Yawancin mutane a Ghana Kiristoci ne amma babu wata shaida da ke nuna cewa fitowa daga wasu tsirarun addinai zai kawo cikas ga damar zaɓen Bawumia, in ji Dr Sefa-Nyarko.
Dr Sefa-Nyarko ya ƙara da cewa NPP ta ba da cikakken goyon bayanta ga takarar Bawumia, "duk da kasancewarsa Musulmi".
"Wannan na iya nuna gagarumin goyon baya da yake samu a faɗin ƙasar."
Asalin Bawumia na iya zama babban sakamako fiye da addininsa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya fito ne daga arewacin Ghana, wanda ɗaya ne daga cikin wuraren da jam'iyyar NDC ta fi karfi.
Ta hanyar zaɓar Bawumia a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, NPP za ta yi fatan samun nasara a arewaci, tare da ci gaba da samun goyon bayan da tuni take da shi a yankin kudanci.
Bawumia dai ya ratsa arewa da kudu da gabas da kuma yamma, inda tafiya da wata motar bas ɗauke da taken "zai yiwu".
Ga wasu, suna kallonsa a matsayin sahun gaba a almubazzaranci, amma mataimakin shugaban ƙasar yana da kwarin gwiwar da yake da shi tun a lokacin yana ɗan shekaru 44, a fafutukar mulki na tsawon shekara takwas.
“Ina da karfin gwiwar amincewa idan abubuwa ba su tafi yadda ya kamata,” kamar yadda ya shaida wa masu kaɗa kuri’a a cikin manufofinsa na yaƙin neman zaɓe.
"Amma ina da tunanin abubuwa masu yiwuwa, da kuma imani a kan mu, cewa za mu iya tashi mu cimma manyan abubuwa a rayuwarmu."











