Diaz na jiran tayin Barca, Madrid na son Konate

Diaz

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Nottingham Forest za ta sake shawara kan buƙatar ɗanwasan Juventus Douglas Luiz a wannan bazara bayan kasa ɗauko ɗanwasan na tsakiya mai shekara 26. (Tuttosport - in Italian)

Everton ta nace kan ɗanwasan tsakiya na Genoa da Belgium mai shekara 22 Koni de Winter idan har ɗanwasan baya na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22 ya bar ƙungiyar. (Teamtalk)

Ɗanwasan gaba na Liverpool da Colombia mai shekara 28 Luis Diaz na son ya koma Barcelona a ƙarshen kaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Bournemouth na son mallakar golar Spain Kepa Arrizabalaga mai shekara 30 da ta karɓo aro daga Chelsea. (Telegraph - subscription required)

Manchester United na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Borussia Dortmund mai shekara 24 Felix Nmecha. (Florian Plettenberg)

Paris St-Germain da Real Madrid na sa ido kan Ibrahima Konate a Liverpool, yayin da ɗanwasan na Faransa mai shekara 25 ya ƙi sabunta kwangilar shi da za ta kawo ƙarshe a shekara mai zuwa. (Football Insider)

Sevilla na shirin fara farautar ɗanwasan tsakiya na Aston Villa da Netherlands midfielder Lamare Bogarde. (Estadio Deportivo - in Spanish)

Bayer Leverkusen da Parma da Wolfsburg da Liverpool da Manchester City da Brighton na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Independiente del Valle da Ecuado Johan Martinez. (Teamtalk)

Lyon za ta sayar da Rayan Cherki a ƙarshen kaka kuma Liverpool da Bayern Munich da Borussia Dortmund na cikin masu ribibin ɗanwasan na Faransa. (Sun)