Vinicius ya ci wa Brazil wasa da ƙwallo mai ƙayatarwa

Asalin hoton, Reuters
Ɗanwasan gaban Real Madrid Vinicius Junior ya taimaka wa Brazil doke Columbia a wasan neman gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026 da ƙayatacciyar ƙwallon da ya ci.
Ƙwallon da Vinicius ya ci a minti na 90+9 daga wajen yadi na 18 ce ta tabbatar da nasarar Brazil ɗin da ci 2-1 a filin wasa na BRB Garrincha da ke ƙasar.
Tun da farko Brazil ɗin ce ta fara cin ƙwallo ta ƙafar Raphinha daga bugun finareti tun a minti na 6 da take wasa, kafin Luis Diaz na Liverpool ya farke ta a minti na 41.
Sai dai nasarar ba ta zo wa Brazil da sauƙi ba saboda yadda ɗanwasan tsakiya Gerson da mai tsaron raga Alisson suka ji rauni, abin da ke nufin sun bi sawun Martinelli da Gabriel Jesus, da Neymar Jr. jinya.
Sakamakon ya sa Brazil ta koma ta biyu a teburin rukunin nahiyar Kudancin Amurka da maki 21 kafin Uruguay ta buga wasanta wadda ke da maki 20 a matsayi na uku.
Argentina ce ta ɗaya a teburin mai maki 25 a yanzu, kuma wasan Brazil na gaba da Argentinar za ta ziyarta ranar 26 ga watan Maris.
Tawaga bakwai da suka ƙare a saman teburin ne za su samu gurbi kaitsaye zuwa gasar da ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su karɓi baƙunci, sannan ƙarin wasu biyu su shiga wasannin neman cike gurbi.






