Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra'ila ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa bayan Hamas ta miƙa gawarwakin ƴan ƙasarta huɗu
Isra'ila ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa a wani ɓangare na rukunnin karshe na musayar fursunoni a mataki na farko na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Motoci Bas sun kwashe wasunsu zuwa Ramallah da ke gabar yamma da kogin Jordan inda suka samu kyakyawan tarba. Akwai kuma wasu da aka kai gabashin Kudus.
Ita kuma Hamas ta saki gawawwaki Isra'ilawa hudu da suke garkuwa da su, wadanda jami'an sojin Isra'ila ke tantacewa.
Fursunonin Falasɗinawa da aka saka sun hada da mutane sama da 400 da sojojin Isra'ila suka kwashe a Gaza a lokacin yaƙi da kuma mutane 50 da aka yankewa hukuncin dauri rai da rai a gidajen yarin Isra'ila.
Yahya Shrida ɗaya daga cikin Falasɗinawa da suka shaki iskan 'yanci, ya nuna farin cikinsa lokacin da ya ga 'yanuwansa da abokan sun fito domin tarbarsa a Ramallah.
A tattaunawarsa da 'yan jarida ya ce ba zai iya kwatanta abin da yake ji a zuciyarsa ba.
"An fito damu daga kangin azaba, kamar an tono mu ne daga cikin kaburbura. Babu wani wanda ake tsare da shi da zai iya bayyana yanayin da muka shiga musamman ganin sau biyu ana samun jinkiri wajen sakinmu.
"Mun sha azabar da ta zarta a goya ma tsauni. Ba zan iya misaltawa ko bada labari ba, ba zan iya cewa komai ba."
Iman Sahloul na daga cikin iyalai da 'yan uwan Fursnonin da suka yi carko-carko a gaban asibitin da tarayyar Turai ta samar a Gaza, suna jiran mutanensu. Ta shaidawa BBC cewa ba ta da buri da ya wuce yin ido hudu da mijinta
"Ba zan iya kwatanta abin da zan ji ba, da zarran na jiyo muryarsa, Idan na jiyo muryarsa duniya ba za ta iya daukan farin cikin da zai mamaye ni ba.
"Idan har na ganshi, yanayi ne da ban ma san abin da zai faru ba. Ban ma san abin da zan ji ba.
Da fari dai an samu jinkiri wajen sakin Falasdianwan 600 a ranar Asabar bayan Isra'ila ta zargi Hamas da karya ka'idojin tsagaita wuta.
Hamas ta bai wa Isra'ila gawawakin mutanen nata hudu a wani kebaben yanayi cikin sirri, wannan na da alaka da alla-wadai da Isra'ila tayi da yadda Hamas ke fitowa fili ana nunawa duniya musayar fursunoni da shirya taro ana kade-kade.
Gawawaki da aka ba ta a yanzu haka take bincike kwajin kwayoyin halittarsu, sun hada da na Shlomo Mansour mai shekara 86 da Ohad Yahalomi mai shekara 50 da kuma Tsachi Idan mai shekara 50, sai kuma Itzik Elgarat mai shekara 69.