Abin da ya kamata mutum ya yi idan ya ji tsawa

Asalin hoton, Getty Images
Da dama mutane ba su san tsawa da ake yi a lokacin ruwan sama tana iya kisa ba.
A makon da ya gabata ne wasu mutum biyu suka mutu a ƙauyen Ƴar Kogi da ke ƙaramar hukumar Gezawa sakamakon tsawar da ta sauka a kansu lokacin da ake sheƙa ruwa kamar da bakin ƙwarya.
To amma wata yarinya ɗaya ta tsallake rijiya da baya daga lamarin inda aka kwantar da ita a asibiti.
Bayanai sun ce tsawar ce ta fara sauka kafin ruwa kamar da bakin ƙwarya ya fara zuba.
"Yara suna gindin bishiya sai kawai muka ji tsawa ta sauka a gindin wannan bishiya sai muka ga ya baje sai muka ga duk kayan jikinsu sun ƙone kuma nantake duk suka mutu. Sai dai yarinya ɗaya ta rayu," in ji Malam Ado Garba, dagacin ƙauyen na Ƴar Kogi.
Yadda ake samun tsawa
Farfesa Mohammad Alhaji ƙwararre ne kan muhalli kuma malami a jami'ar Aliko Ɗangote da ke Wudil a Kano ya yi bayani kan abin da ke haddasa tsawa.
"Tsawa tana faruwa ne a lokacin da giragizai suka hau sararin samaniya dab da saukar ruwan sama ko kuma lokacin da ruwan ke sauka.
"Ita tsawar na faruwa ne saboda yanayin haɗuwar giragizan a sararin samaniya wanda kuma haɗuwar tasu na haifar da ƙwayoyin maganaɗisu mai alamar tarawa da kuma alamar ɗebewa, to duk lokacin da suka haɗu dole ka ga walƙiya kuma dole ka ga tsawa." In ji Farfesa Mohammed
Yadda ake samun walƙiya
Ita kuma walƙiya maganaɗisu ne na haske da ke fitowa daga giragizan da ake yi wa laƙabi da raƙumin ruwa da Hausa ko kuma 'Cumulonimbus' da Turanci.
"Su waɗannan gira-gizai na hauhawa ne sakamakon wannan haske da yake faruwa. Idan aka haska sai ta zama mai zafi wadda za ta buɗe ta kuma ƙara kaurarewa ta cika wajen abin da ya sa dole ne ta fashe. To lokacin da ta fashe shi ne za ta zo a matsayin walƙiya sannan kuma tsawa ta biyo baya."
"To idan aka yi wannan tsawa da walkiya kuma bisa rashin sa'a mutum yana kusa da inda turakun wutar lantarki suke ko kuma yana kusa da wata doguwar bishiya. To wannan hasken shi ne yake biyowa wannan bishiyar ko kuma doguwar sandar wutar lantarkin ta zo ta samu mutane wanda idan kwana ya kare ma sai a rasa rai."
Hanyoyin kare kai
Farfesa Mohammad Alhaji ya ce domin kiyayewa daga fuskantar illar tsawa ya bayar da wsu dabaru kamar haka:
- Da zaran aka ji rugugin tsawar idan kana gindin bishiya ko kuma turken wutar lantarki ko kuma maganaɗisu na wayoyi abin da ya kamata ka fara yi shi ne ka yi maza-maza ka bar wurin.
- Sai ka rufe kunnenka ka tafi wurin ɓuya kuma bisa son samu a shiga irin gidajen ƙasa na gargajiya su ne suke kare mutane daga tsawa saboda ba sa ɗauke da maganaɗisu.
- A guji shiga cikin mota ko manyan gine-gine da sunan neman mafaka.
- Idan aka ga tsawa ka da a tsaya a fili fetal ko kuma saman gini.
- Ka da a tsaya a tsaye - A zauna a haɗe ƙafafu a wuri ɗaya tare da saka hannaye a cikin gwiwoyi da rufe kunnuwa.










