Hanyoyi hudu da Zelensky ke jan hankalin duniya a kan yakin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da sojoji ke can fagen daga suna yaƙi bayan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine, Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky shi kuma na can yana ta ganin yadda za ya yi domin samun taimako daga ƙasashen duniya.
Ɗaya daga cikin abubuwan da Mista Zelensky ya yi akwai taruka da dama da shugabannin ƙasashen duniya a Kyiv da kuma ɗaukar hoto da fitattun mutane.
A yayin da Ukraine ke fuskantar matsin lamba daga Rasha, Ukraine ɗin na buƙatar taimakon ƙasashen waje domin daƙile dakarun Rasha daga ci gaba da shiga ciki.
Domin samun goyon bayansa, masu kula da ɓangaren wasa labarai na shugaban ƙasar sun samo wasu hanyoyi domin jan hankalin duniya kan irin abubuwan da ake fuskanta a ƙasar.
Taimakon muhimman mutane

Asalin hoton, Reuters
Wayar da kan mutanen duniya da fitattu ko kuma sanannun mutane suke yi tun bayan soma wannan yaƙi, inda suke goyon bayan Ukraine tare da tara kuɗi masu yawa ya taimaka.
Cikin waɗanda ke wannan aikin har da tsohon ɗan ƙwallo David Beckham da mawaƙi Ed Sheeran da ƴan fim kamar su Sean Penn da Ashton Kutcher da Mila Kunis wadda ƴar Ukraine ce.
Ƴar fim Angelina Jolie wadda wakiliya ce ta musamman a Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta kai ziyara Ukraine a watan Afrilu inda ta haɗu da masu aikin sa kai da ƴan gudun hijira.
Mista Zellensky wanda tsohon ɗan wasan barkwanci ne ba wai baƙo bane a wannan harkar inda ya haɗe da mutanensa da ke goyon bayan ƙasarsa.
Karɓar baƙi ƴan siyasa (ko kuma zama baƙo a taron intanet)

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Irin waɗannan hotunan Mista Zelensky yana yin su tare da tare da shugabannin ƙasashen Turai inda yake neman shawo kan Tarayyar Turan da ta amince da Ukraine ta shiga ƙungiyar, tare da kuma samun ƙarin makamai.
Cikin shugabannin ƙasashen da suka kai ziyara Kyiv a yan kwanakin nan har da Emmanuel Macron na Faransa da Mario Draghi na Italy da Olaf Scholz na Jamus da Klaus lohannis na Romania.
Haka kuma akwai Firaiministan Birtaniya Boris Johnson da Justin Trudeau na Canada, sai dai babu Joe Biden na Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden ya samar da biliyoyin daloli da kuma makamai ga Ukraine inda ya ce ba ya so ya ƙara jawo wa Ukraine ƙarin wahala, musamman idan ya ce zai tsaya a ƙasar a tafiyar da za ya yi nan gaba zuwa Turai.
Ƙasashen da ba na yamma ba sun fi samun rabuwa a goyon bayan da suke ba Ukraine a yaƙi, duk da cewa Mista Zelensky na ta neman taimako, inda ake jan hankalin ƙasashen Afrika kan abin da zai iya biyowa baya sakamakon yaƙin Ukraine.
Ya bayyana cewa Yan Afrika sun zama kamar fursunonin yaƙi kuma suna fuskantar barazanar yunwa saboda yaƙin ya jawo ƙarancin taki da hatsi - sai dai BBC ta gano ƙasashen Afrika huɗu ne kacal cikin 55 suka shiga taron anda aka yi ta intanet.
Sauran tarukan da aka yi na bidiyo an halarce su kuma an yaba wa Mista Zelensky kan bayanansa da ya yi wa Majalisar Tarayyar Amurka da Tarayyar Turai da Jamus da Japan da Faransa da Sifaniya da Majalisun Italiya da sauran su.
Nuna wa duniya

Asalin hoton, EPA
Mista Zelensky ya kuma yi wani abu da ya nuna wa duniya irin ɓarnar da Rasha ta yi wa Ukraine , ta hanyar zagayawa zuwa biranen da aka lalata da kuma kai zuyara ga sojojin da ke fagen daga da asibitoci.
Ya yi tafiyarsa ta farko zuwa birnin kudancin ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita a ranar Asabar inda ya yi zagaye a birnin Mykolaiv.
A lokacin da ya kai, Mista Zelensky ya je ya duba gine-ginen da suka lalace haka kuma ya haɗu da sojoji da jami'ai da ma'aikatan lafiya.
Haka kuma shugaban Ukraienɗin ya kai ziyara birnin Odesa da ke yammacin ƙasar wanda aka yi ta kai masa harin makamai masu linzami tun bayan da aka fara wannan yaƙi.
A cikin ƴan makonnin nan, ya kai ziyara wasu daga cikin biranen da ake yaƙi ciki har da Kharki da ke gabashin ƙasar, inda ya bijirewa dakarun Rasha ya je har wurin da ake tsananin yaƙi.
'Kada a koma wani abu'

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da dakarun Ukraine ke ta fafatawa a faten daga, shugaban ƙasan ya nuna jajircewa domin ganin duka duniya ba ta juya wa Ukraine baya ba a wannan lokaci.
Ya yi magana sosai da mutane da dama ciki har da sanannun mutane da shugabannin duniya, ɗaliban jami'o'i a Amurka da kuma jaridun duniya, da kuma manyan ƴan kasuwa daga Doha da Davos.
A watan da ya gabata, ya shiga taron 'Cannes Film Festival' wanda taron duniya ne kan film inda ya yi bayani ta intanet, bayanin da ba a san zai yi ba inda har jama'a suka tafa masa.
A yayin da yake magana, Mista Zelensky ya ce kada a bari duniya ta zama wani abu daban.











