Yakin Ukraine: Tsawon wanne lokaci ƙasashen Yamma za su ci gaba da goyon bayan Ukraine?

Boris Johnson, Emmanuel Macron da kuma Joe Biden

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Amurka a wajen taron G7 da aka yi a watan Maris
    • Marubuci, Daga Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilinmu kan harkokin difilomasiyya

Yayin da dakarun Rasha ke kara samun nasara a yankin gabashin Donbas, ko akwai mata matsala ne daga kasashen Yamma wajen taimaka wa Ukraine?

Shugaban Rasha Vladimir Putin daga fadarsa yake bai wa dakarunsa umarnin yadda za su fafata, abin da ke sa kasashen Yamma nazari a kan yadda za su taimaka wa Ukraine don ta kare kanta daga Rasha.

A gefe guda, yana kallon gwamnatin Birtaniya da Poland da kuma sauran kasashen yankin Baltic a matsayin wadanda ke son ganin bayansa.

Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya, Liz Truss, ta ce "Akwai bukatar mu tabbatar 'yan Ukraine sun fatattaki Rasha daga kasarsu da kansu".

To amma a bangare guda, Mr Putin na kallon shugabannin kasashen Faransa da Jamusa da kuma Italiya a matsayin masu wata muguwar manufa game da kasarsa.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz

Asalin hoton, Getty Images

Da yake jawabi a farkon watan Mayu, shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kira a tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine, sannan ya bukaci kasashen Yamma da kada su ci zarafin wani ko kuma daukar fansa a kan wani.

Washegari kuma, sai firaministan Italiya, Mario Draghi, ya yi bayani a fadar gwamnatin Amurka cewa ya kamata al'ummar Turai su fara tunani a kan yiwuwar yadda za a fara tattaunawa a kan batun tsagaita wuta.

Bayan wata tattaunawa ta waya da suka yi tsawon mini 80, Olaf Scholz da Mr Macron, sun kira Mr Putin a kan samar da hanyar da za a bai wa Ukraine damar fitar da hatsinta ta kogin Black sea.

Sai dai kuma akwai wasu shugabannin kasashen da suke gani gara a rinka cuzguna Rasha shi ne mafi a'ala.

Ko shakka babu, shugaban Amurka shi ne babbar damuwar Rasha.

Joe Biden ya sha nuna wa Rasha cewa hare-haren da take kai wa a Ukraine za su zama laifin yaki.

Sannan a makon nan ne ya tabbatar da cewa zai aika da makaman roka zuwa Ukraine don tunkarar Rasha.

Tsohon firaminista kuma shuga Dmitry Medvedev, sun ce matakin Amurkan bai dace ba.

To amma duk da haka a ranar Larabar da ta wuce, Amurka ta bayyana shirinta na tura karin makamai ga Ukraine abin da Rasha ta ce hakan kara rura wutar rikicin ne.

Makamin atilari

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da shugaban Amurka zai yi jawabin da bai shiryaw ba, jan aiki zai koma kan sakataren harkokin wajensa Antony Blinken, wanda zai bayyana matsayar kasarsu.

A taron kungiyar tsaro ta NATO, da ministocin harkokin wajen kungiyar suka yi a baya-bayan nan a Berlin, Mr Blinken ya ce Amurka da kawayenta yanzu sun mayar da hankali wajen bai wa Ukraine manyan makamai don fafatawa a fagen yaki da kuma kare kanta daga dukkan barazana daga Rasha.

Bisa la'akari da wadannna kalamai na Mr Blinken, ya nuna cewa ko an fara samun baraka ne daga wajen kasashen Yamma a kan Ukraine?

Tuni dai kasashen Yamma suka fara neman mafita a kan matsayar Rasha na dai samar musu da mai da iskar dinta, saboda sun ce duk da matakin Rashan hakan ba zai hana sanya musu karin wasu takunkuman ba.

Akwai bukatar samar da karin makamai ga Ukraine

Kasashen Yamma sun yi alkawura da dama, Ukraine kuma na jira to amma abin da ake kai mata bai taka kara ya karya ba.

A makon nan, Amurka da Jamus, sun yi alkawarin aike wa da karin makamai musamman na roka da atilari ga Ukraine don kare kanta da ga hare haren Rasha.

To amma zargin cewa Jamus na jan kafa a kan duk wasu alkawura da ta dauka, da kuma batun cewa Biden ya hakikance cewa makaman da Amurka za ta aika wa Ukraine, za a yi amfani da su wajen dakile hare-haren Rasha a Ukraine, ya sa wasu na ganin me yasa kasashen yamma son takaita taimakonsu a kan yakin Ukraine.

Wani sojan Ukraine rike da makami

Asalin hoton, Reuters

An yi amanna cewa Mr Putin ya kaddamar yakin ne da tabbacin cewa kasashen yamma ba za su iya yin komai ba.

Wasu sabbin rahotanni daga Rasha, sun ce har yanzu rasha na da kwarin gwiwa kuma da sannu a hankali tana samun nasara a fagen yaki, don haka tana ganin ko ba dade koba jima kasashen yamma za su gaji da bawa Ukraine Tallafi.

A makon nan ne Birtaniya ta girgiza zuciyar Rasha bayan da ta yi gargadin cewa gidajen Rasha akalla miliyan shida zasu fuskanci matsalar rashin wutar lantarki, muddin Rashan da dakatar da kai mata iskar gas a lokacin sanyi.

Shin ko fusata jama'a a kasashen yamma zai dakile taimakon da ake ba wa Ukraine?

Babban abin tsoro da fargaba ne inda a watan daya gabata shugabar hukumar leken asirin Amurka ta yi wa majalisar dokokin kasar cikakken bayani.

Ta ce Mr Putin na kokarin karya lagon Amurka da ma kasashen Turai a yayin da ake samun karanci abinci da tashin farashin kayayyaki da na makamashi.

Emmanuel Macron da Olaf Scholz a Berlin

Asalin hoton, EPA

Duk da shakkun da ake dashi cewa turawa Ukraine da makamai da kasashen yamma ke yi kamar suna cutar da kansu ne, hakan bai girgiza matsyaar da suke da ita a kan Ukraine ba.

To amma har yanzu dai barakar na nan.

Ian Bond, ya ce idan har wani bangare ya fara samun wata nasara, to za su iya samun matsala.

Ma'anar abin da yake cewa ita ce idan har Rasha ta tsallaka zuwa gabashin Ukraine ta kai ga kogin Dnieper, abin tambayar anan shi ne iyakokin nawa Ukraine zata sadaukar kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta?

Sannan idan kuma sojojin Ukraine suka fara fatattakar na Rasha, to dole za ka fara jin kasashen yamma na cewa kada su kwace wasu yankuna na Donbas da Rasha ke iko da su tun 2014.