Tinubu ya naɗa C.G. Musa ministan tsaron Najeriya

Asalin hoton, Defense HQ Nigeria
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura sunan tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, mai ritaya zuwa majalisar dattawan ƙasar domin tantance shi a matsayin ministan tsaro.
A wata takarda da Tinubu ya aika, ya buƙaci majalisar ta tantance Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin, kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
A ranar Litinin 1 ga watan Disamba ne Ministan Tsaron Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙaminsa, sannan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da matakin.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanguga ya fitar ranar Litinin ɗin da daddare, ya ce Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar da ya aika wa shugaba Bola Tinubu, inda sanarwar ta ƙara da cewa Badaru ya ajiye aikin ne bisa dalilai na neman lafiya.
Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro, musamman dawowar garkuwa da mutane a yankin arewacin ƙasar, musamman a makarantu da kuma hare-hare a wasu jihohi, ciki har da jihar Kano da ba a saba ganin haka ba a baya.
A watan jiya ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 25 a jihar Kebbi, sannan aka sace wasu kimanin 300 a jihar Neja, da kuma wasu a wasu jihohin duk da cewa an ceto na Kebbi baki ɗayansu.
Haka an samu rahoton kashe-kashe, ciki har da jihar Borno inda aka kashe wasu manoma, da kuma hafsan sojin ƙasa, Birgediya Janar Uba Musa da ake zaton ƴan ISAWP sun kashe, duk da cewa rundunar sojin ƙasa ba ta tabbatar ba har zuwa yanzu.
Murabus ɗin Badaru
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A makon jiya ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalolin tsaro a ƙasar, inda ya ɗauki matakai guda da ya ce za a yi domin daƙile matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Najeriya ta ƙara tsaka mai wuya ne bayan da aka fara yaɗa zargin yi wa Kiristocin ƙasar kisan kiyashi, lamarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya karɓa hannu biyu-biyu, har ya yi barazanar tura sojoji zuwa Najeriya domin "su yi yaƙi da ta'addanci."
Bayan barazanar ta Trump ne aka kai harin kan masu ibada a wani coci da ke jihar Kwara, sannan aka yi garkuwa da ɗaliban wata makarantar Katolika a jihar Neja da satar mutane a jihar Kogi, lamarin da ya ƙara fama ciwon da ƙasar ke fama da shi na tsaro.
Sai dai Tinubu ya tura tawaga ta musamman a ƙarƙashin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu zuwa Amurka domin ganawa da hukumomin tsaron ƙasar, inda suka tattauna kan zargin na gwamnatin Amurka, da kuma ba ƙasar bayanin "haƙiƙanin abubuwan da ke faruwa a ƙasar."
Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayanin abubuwan da suka cimmawa ba, amma fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa sun cimma wasu matakai, sannan ƙasar ta sanar da kafa kwamitin ƴan ƙasar a ƙarƙashin Ribadu domin ganawa da wakilan da Amurka za ta kafa domin su yi aiki tare da domin magance matsalar da Najeriya ke fuskanta.
Sai dai duk kafin nan, ƙasar ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, inda ƙasar ke fama da ƙungiyoyin ƴanbindiga da suke addabar sassan ƙasar daban-daban, lamarin da ya sa ƴan ƙasar ke ta kira da a ɗauki mataki.
Wane ne Christophe Gwabin Musa?
An haifi Christopher Musa ne a ranar 25 ga watan Disamban shekarar 1967 a jihar Sokoto, kuma shi ne babban hafsan tsaron ƙasar daga 2023 zuwa watan Oktoban shekarar 2025.
A shekarar 1991 ne ya fito daga kwalejin horar da hafsoshin soja ta Najeriya, wato NDA, inda ya fara aiki a shekarar a matsayin soja mai anini ɗaya.
A shekarar 2021 ne aka zaɓi Musa domin ya jagoranci aikin soji na musamman na Operation Hadin Kai wato yaƙi da Boko Haram, inda daga can ya zama shugaban sashen mayaƙa na Infantry, kafin Tinubu ya naɗa shi a matsayin babban hafsan tsaron ƙasar.
'A sakar masa mara idan ana son aiki'
Dama dai awanni kaɗan kafin Mohammed Badaru ya ajiye muƙaminsa na minista, an ga tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar CG Musa mai ritaya a fadar gwamnatin Najeriya, inda aka ce ya gana da Bola Tinubu na wani ɗan lokaci a ranar ta Litinin.
Wasu dai suna ganin sabon sauyin ba zai rasa nasaba da tattaunawar da Najeriya ke yi da Amurka ba.
Sai dai a nasa jawabin, Group Captain Sadiq Garba Shehu mai ritaya ya shaida wa BBC cewa matsalar ba a zaɓo wanda zai yi ba ne kawai.
A cewarsa, Janar CG Musa ya yi matuƙa ƙoƙari wajen fito da tagomashin da ke cikin ofishin babban hafsan tsaro, "domin a baya ofishi ne kawai da aka tanada amma babu takamaiman bayani kan ayyukansa. Amma zuwansa ya gyara aikin ofishin sosai," in ji shi.
Sai dai ya ce irin matsalar da ke tattare da ofishin babban hafsan tsaron, haka ma akwai matsalar a ofishin ministan tsaro a Najeriya.
"Lallai akwai buƙatar a zaƙulo janar ƙwararre kuma gwarzo domin maye gurbin, amma ba gwarzantar kawai ake buƙata ba, dole ana buƙatar a tsara ayyukan ofishin. A Najeriya za ka ga ministan bai da takaimamen tsarin aiki, za ka ga manyan hafsoshin babu tabbacin ko suna ƙarƙashinsa ko a'a."
Ya ce idan ana so a samu sakamako mai kyau, dole a samu gwarzo, sannan a sakar masa mara ya yi aikinsa yadda ya dace. "domin lallai muna da ƙwararrun janarori, kuma na san zuwa yanzu Tinubu ya fahimci cewa lallai tsohon janar ɗin ne zai yi samar da sakamakon da ake buƙata," in ji Sadiq.











