Ta yaya za a shawo kan ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga Najeriya?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A baya-bayan nan an samu rahotannin kai hare-hare da dama a arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin Najeriya, bayan wani ɗan lokaci na sassauci.

Na baya-bayan nan shi ne wanda mayaƙan Boko Haram suka kai a garin Shikarkir da ke ƙaramar Chibok ta jihar Borno, inda suka ƙona wani coci da gidajen mutane.

Sun kai wannan harin ne kimanin awa 24 bayan sun kai wani harin a ƙauyen Bazir, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙona wani cocin daban.

Sai dai harin da ya fi girgiza al'umma na baya-bayan nan shi ne harin da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, lamarin da ya yi ajalin manoma da masunta da dama a ƙaramar hukumar Kukawa da ke jihar Borno.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan yaɗa labaru na jihar Borno, Usman Tar ya ce "aƙalla mutum 40" ne suka halaka sanadiyyar harin.

Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da neman wasu mutanen da ba a san inda suke ba tun bayan kai harin.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi alla-wadai da harin, sannan ya yi kira ga dakarun Najeriya masu aiki a rundunar Operation Hadin Kai da su zaƙulo "ƴan ta'addan" da ke aikata ta'asa a yankin Dumba mai maƙwaftaka da Tafkin Chadi.

Wannan ne hari na uku mafi muni a cikin mako ɗaya a jihar Borno, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Janairun 2025, wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan fashin daji ne sun yi wa ƴan sintiri na rundunar tsaro ta Katsina Community Watch Corp kwantar-ɓauna a ƙaramar hukumar Safana, lamarin da ya haifar da asarar rayukan aƙalla mutum 20, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Wannan ya sanya mutane da dama na tambayar cewa mene ne ya sanya irin waɗannan hare-hare suka sake dawowa?

Me hakan ke nufi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana tsaro sun ce duk wani hari, barazana ce ga tsaron Najeriya.

Group Captain Sadiq mai ritaya ya ce yadda Boko Haram ta yunƙuro tana kai hare-hare a yanzu abin damuwa ne domin kuwa tamkar tana son sake yunƙurowa ne.

Masanin tsaron ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga rashin isassun sojojin da ke ƙƙarin yaƙi da ƙungiyar da kuma rashin sanya ido da kulawa na ƴan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

"Zai yi kyau idan shugabannin siyasa za su riƙa sanya ido kan ayyukan sojoji, koda wata-wata ne, domin sanin yadda abubuwa ke tafiya," in ji shi.

Ya ce bai kamata shugabannin siyasa su riƙa ja baya daga sanya ido kan ayyukan sojoji ba. Idan ya kasance suna shakkar sanya wa sojojin ido domin gudun kada su samu matsala da sojojijn ne, hakan zai iya cutar da ƙasar.

"Idan shugabannin siyasa na gudun su samu matsala da sojojin ne, to lallai ƙasa na cikin haɗari," in ji shi.

Ya bayyana cewa ƙarancin sojojin da ke yaƙi da Boko Haram ne ya Sanya aka kasa kawar da ƙungiyar baki ɗaya a cikin kimanin shekara 15 da ta kwashe tana aiwatar da waɗannan kashe-kashe.

"Sojojin Najeriya sun yi ƙaranci, shi ya sa muke fuskantar waɗannan matsaloli," in ji shi.

Sai dai ya bayyana cewa matsalar ba ta shafi ɓangaren soja ne kawai ba, ya haɗa da sauran ɓangarori kamar ofishin shugaban ƙasa da majalisar dokoki, kasancewar ba su sanya ido kan matsalar yadda ya kamata.

Mece ce maslaha?

Captain Sadiq ya ce ya kamata Najeriya ta ci gajiyar makudan kudaden da ake ware wa ɓangaren tsaro wajen ganin an ɗauki ƙarin sojoji.

Ya ce "Najeriya na buƙatar ƙarin sojoji a maimakon kuɗaɗen da ake kashewa a wasu ɓangarorin na tsaro."

Haka ya bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnati ta riƙa neman shawara daga masana a ɓangaren tsaro, musamman tsofaffin sojoji, waɗanda za su taimaka da shawarwari kan yadda za a riƙa tafiyar da ɓangaren.

Captain Sadiq ya ce ya kamata ofishin shugaban ƙasa da ministan lafiya da kuma ƴan majalisa su riƙa sanya ido kan ayyukan sojoji, musamman yadda ake kashe kuɗin da ake ware wa ɓangaren.