Shin ko yaushe tirka-tirkar shugabanci za ta ƙare a jam'iyyar PDP?

Asalin hoton, PDP
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana cigaba da tattauna yiwuwar samun maslaha a rikicin cikin gida da ya dabaibaye babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, wato PDP, ganin yadda rikicin da ya yi mata katutu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa na tsawon lokaci.
A ranar Litinin din nan ne ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar suka zauna domin tattaunawa tare da samar da maslaha a game da rikice-rikicen jam'iyyar, bayan ɓangarori biyu a jam'iyyar sun dakatar da juna.
Tun da farko, wani ɓangare na jam'iyyar ya sanar da dakatar da sakataren watsa labarai na ƙasa na jam'iyyar, Debo Ologunagba, da mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Kamaldeen Ajibade.
Sai kuma wani ɓangaren kuma ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na riko, Umar Damagun, tare da naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Wannan ya sa gwamnonin suka zauna domin samar da maslaha, inda bayan taron suka sanar da soke dakatarwar da aka yi wa Damagum ɗin, da ma sauran waɗanda aka dakatar baki ɗaya, sannan suka buƙaci kowa ya koma muƙaminsa a cigaba da aiki.
Wannan na ƙunshe ne cikin jawabin da shugaban gwamnonin jam'iyyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi wa manema labarai a safiyar jiya Talata.
Wannan ke nufin Damagum zai ci gaba da riƙe kujerar shugaban jam'iyyar na riƙo.
Sai dai zuwa yaushe Damagun zai cigba da riƙe kujerar? Kuma shin wannan maslahar za ta kashe wutar, ko kuma an kashe maciji ne ba a sare masa kai ba?
Me ya janyo rikicin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rikice-rikice a siyasa ba sabon abu ba ne, musamman a tsakanin jam'iyyu manya da suke riƙe da madafun iko.
Jam'iyyar PDP ta sha fama da rikice-rikice tun daga kafuwarta a shekarar 1998, kimanin shekara 26 da suka gabata, tun tana da mulki, har zuwa barinta mulki.
Tun bayan kayar da PDP da APC ta yi a zaɓen 2015 ne aka fara samu matsala, inda jam'iyyar ta dare biyu a tsakanin shugabancin tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Maƙarfi da tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff.
Jam'iyyar yanzu ita ce babbar jam'iyyar adawa, wannan ya sa ake tunanin rikice-rikicen bai rasa nasaba da hanƙoron neman takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027.
Ana tunanin hakan ne kasancewar rikicin da ake ciki yanzu ya samo asali ne daga zaɓen fitar da ɗantakara na zaɓen 2022, wanda aka yi a ranar 28 da Mayun shekarar 2022, inda Atiku Abubakar ya doke Wike.
Wike da sauran gwamnonin na ƙungiyar G5 suka ce ba za su goya bayan Atiku ba, sai shugaban jam'iyyar na ƙasa na lokacin, Iyorchia Ayu ya sauka, sannan a samu wani sabon shugaban daga kudu. Sai dai ba a samu wannan hakan ba, har aka yi zaɓe, inda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya doke Atiku, inda ɓangaren Atiku suka zargi Wike da yi w APC aiki a zaɓen.
'Damagun - shugaban riƙo mai cike da taƙaddama'

Asalin hoton, FACEBOOK/Umar Iliya Damagum
Bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024, inda Atiku Abubakar ya sha kaye, sai rikicin na PDP ya ɗauki sabon salo.
Kwatsam sai shugabannin PDP na mazaɓar Iyorchia Ayu suka sanar da dakatar da shi, sannan kotu ta tabbatar da dakatarwar.
Bayan dakatar da shi, sai Umar Damagun, wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar daga arewa, sai ya zama shugaban jam'iyyar na riƙo.
Ana cikin wannan ne, sai Tinubu ya naɗa Wike minista, wanda hakan ya sa magoya bayan jam'iyyar da dama suka buƙaci a dakatar da shi, sannan a ladabtar da shi.
Sai dai duk da kiraye-kirayen da aka riƙa yi na a ladabtar da Wike, Damagun bai amsa ba. Nan ne rikicin ya ƙara ƙamari, inda jam'iyyar ta fara komawa kan Atiku da Wike, wanda aka fara tun bayan zaben fid-da-gwani.
Haka kuma a zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers, tsagin Wike ya samu nasara a kan tsagin gwamnan jihar, Sim Fubara, lamarin da ya sa wasu suka ce akwai lauje cikin naɗin ganin an ƙwace jagorancin jam'iyyar daga hannun gwamna mai ci.
Wannan ya sa wasu ƴan jam'iyyar suke zargin cewa Damagun ya zama ɗan amshin shatan Wike, inda wasu daga ciki suka dage kai da fata sai ya sauka tunda dama shugabancin riƙo ne.
A nan ne wasu gwamnonin jam'iyyar PDP, musamman gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce hakan ba daidai ba ne, dole a mayar da shugabancin jam'iyyar a ƙarƙashin gwamna Fubara.
Wace illa rikicin ke yi wa PDP?
A game da waɗannan rikice-rikicen, Farfesa Yahaya Tanko Baba, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke jami’ar Usman Dafodiyo ya ce, "Wannan rikici ba sabon abu ne idan ana nazarin jam’iyyu musammam saboda mafi akasari jam’iyya mai mulki ba ta cika bari jam’iyya adawa ta zauna lafiya ba.
"Mun san cewa wannan rikici na PDP ya samo asali ne tun kafin a yi babban zaɓen 2023, inda wasu gwamnoni suka bijirewa jam’iyyar suka ja daga da wanda yake takara kan wata matsaya ta sai an cire shugaban jam’iyyar na wancan lokacin wato Iyorchia Ayu."
Farfesa Baba ya ƙara da cewa bayan zaɓe rikicin ya ƙara ta'azzara ne saboda, "ana zargin jam’iyya mai mulki tana da hannu. Duk waɗannan matsalolin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Rivers Wike. Rashin sasantawa da shi da kuma aikin da yake yi a gwamnatin APC na da alaƙa da zurfin rikicin na PDP."
Me ya kamata PDP ta yi gabanin zaɓen 2027?
A game da maslahar da gwamnonin PDP ta yi kuwa, farfesa Baba ya ce za ta iya taimakawa na wani ɗan lokaci.
"Amma ƙila yanzu za a iya samun ɗan sauƙi. Sauƙin da za a samu shi ne dama jam’iyya, musamman ta adawa gwamnoni su ne ƙarfinta domin su ne suke bayar da gudunmuwa wajen tafiyarta. To idan suka samu matsaya a kan wani abu, to suna da ƙarfin murƙushe duk wata matsala da ta kunno kai sai dai idan daga cikinsu aka samu wata ɓarakar kuma.
Sai dai masanin siyasar ya bayyana cewa wannan rikicin zai iya tasiri a kan shirin jam'iyyar game da zaɓe mai zuwa sai dai idan sun yi tufkar hanci.
"Manufar ita ce su cigaba da rikici har zuwa zaɓen mai zuwa. Kuma idan ba su sasanta wannan rikicin ba har zuwa wata shekara, to lallai zai taɓa tasirinta a zaɓe mai zuwa."
A ƙarshe ya ce akwai buƙatar babbar jam'iyyar adawar ta zauna ta sasanta tsakanin ƴaƴanta masu mata biyayya, "sannan a saurari waɗanda suke da buƙatun da ba su saɓa da dokokin jam'iyyar ba. Amma akwai ɓangare da ta fito ƙarara ja daga da jam'iyyar, wannan zai yi wahala a samu jituwa da su."










