Ƴan arewacin Najeriya 10 da ake amfana da baiwarsu a shafukan sada zumunta

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Masana da ƙwararru kan harkokin lafiya kan bai wa masu amfani da shafukan zumunta shawarar su guji ɓata lokaci mai yawa a kan shafukan - amma shakka babu masu zaman hira da kallace-kallace ne kawai ke buƙatar wannan shawara.

Dalili a nan shi ne, duk wanda ke neman ciyar da rayuwarsa gaba ta hanyar bin shafukan koyo da koyarwa ba zai so ya bi shawarar likitocin can ba.

Ƙididdiga ta nuna ya zuwa watan Fabrairun 2024, a kullum ana wallafa bidiyo kusan miliyan 34 a dandalin TikTok kawai, sai dai ba dukansu ke amfanar al'umma ba.

Kamar sauran al'ummar duniya, miliyoyin 'yan Najeriya na kaiwa da komowa a shafukan sada zumunta, amma samun masu yaɗa abin da zai sauya rayuwar mutane daga cikinsu abu ne mai wuya.

A wannan maƙala mun duba mutum 10 daga cikin waɗanda 'yan Najeriya ke amfana da su kyauta.

1. Dr Hadi Usman (Hadi Radio)

Malam Hadi Usman dattijo ne ɗan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, wanda aka fi sani da Dr Hadi Usman ko kuma Dr Hadi Radio a shafukan zumunta.

Dattijon ya ƙera abubuwan fasaha daban-daban har 75 tun daga 1975 zuwa watan Maris na 2022, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Dattijon abin da ya sa Turawa daga ƙasashen Poland da Jamus da Kanada da China ke rububin sayen fasaharsa.

Daga cikin abubuwan da ya ƙera akwai gidan rediyo, da jirgin helikwafta da wayar salula tun kafin ta shigo Najeriya.

Shafinsa na Facebook mai suna DrHadi Usman na da mabiya sama da 118,000 da ke samun ilimai da suka haɗa fasaha, ƙere-ƙere, da tarihi a kyauta. Idan yana son ya buɗe ajin da sai an biya kuɗi kuma yakan sanar.

2. Awwal (Ahmad) Janyau

Shekara biyu kafin yanzu, Awwal Ahmad Janyau ya shahara ne a matsayin ɗan jaridar gidan rediyon BBC Hausa.

Amma yanzu Janyau na janyo hankalin ma'abota shafukan zumunta ne zuwa ga yadda ake rubuta daidaitacciyar Hausa a Facebook, da Instagram, da Tiktok, da X - wanda ake kira Twitter a baya -, da LinkedIn, a matsayinsa na masani kan harshen Hausa.

Awwal kan haɗa darussa cike da bayanai da misalan yadda ake furtawa da kuma rubuta kalmomi da jimlolin Hausa a shafukan nasa kyauta ba tare da ko kwabon masu kallo ba.

Yana da mabiya 33k a Facebook, da sama da 8.5k a TikTok. Amma a bayyane take cewa ba iya mabiyansa ne kawai ke amfana da ilimin nasa ba.

3. Dr. Maryam Ahmed Almustapha

Idan kuna neman darussa game da lafiyar jikin ɗan'adam, kawai shafin Dr. Maryam Ahmed Almustapha za ku je.

Da zarar kun yi hakan, za ku tarar da ƙarin mabiyanta sama da 216k a Facebook, da wasu 263.8k a TikTok, da 68.8k a Instagram, inda take tsage bayanai game da abubuwan da jikin ɗan'adam ya ƙunsa da kuma yadda ake kula da jiki.

Indai a shafukan Dr Maryam ne ba sai kun biya ko kwabo ba kafin ku amfana.

A cikin wannan bidiyon da ta wallafa dab da fara azumin watan Ramadana na bana, likitar ta bayyana yadda jikin mutum ke aiki idan yana azumi.

Amma BBC ma ta yi irin wannan labari: Mene ne ke faruwa da jikinmu idan muna azumi?

4. Dr. Naima Idris (Girls Talk Series)

Gare ku mata - duk wadda ke son ƙarin ilimi game da lafiya da kuma tsaftar jikinta, tana iya ziyartar shafin Dr. Naima Idris Usman, wadda aka fi sani da Girls Talk Seiries a shafukan zumunta.

Naima likitar mata ce da koyar da dubundubatar mata tsafta, musamman tsaftar al'aurarsu ta hanyar bidiyo da sauti.

Wani lokaci a 2021, ta faɗa wa BBC Hausa cewa ta fara wayar da kan mata ne saboda yadda wasu ke cewa wai idan mace ta saka maggi a gabanta sai ƙara mata matsi.

Mutum sama da 468k ne ke bin likitar da ta yi karatu a China a Facebook, da wasu fiye da 161k a Instagram. Akasarin darussanta kyauta ne, kodayake tana sanarwa idan za a biya kuɗi.

5. Nura Muhammad (Speaking English with Nura)

Wannan kuma masu son yin Turanci kamar Turawan Ingila abin ya shafa. Idan burinku shi ne zubo Turanci kamar yadda masu abin ke yi, to ba ku da wata matsaya illa shafin Nura Muhammad.

Nura ɗan jarida ne a Radio Nigeria, kuma masu sauraronsa shaida ne cewa bakin nasa fa ya kwana biyu da juyewa.

Idan kuka leƙa shafinsa na Facebook za ku tarar da mabiya aƙalla 4.9k, da 2.2k a TikTok, waɗanda ke samun darussan Ingilishi a ɓagas.

Ya yi wa shirin nasa laƙabi da Speaking English With Nura.

6. MD Sulaiman (Trademastermind)

Yadda abubuwa suka yi ƙamari a Najeriya a 'yan watannin nan, za ku so ku koyi yadda za ku dinga sayar da hajarku har a ƙasashen ƙetare, kuma a nan ne za ku buƙaci ƙwarewar MD Sulaiman.

An fi sanin matashin da suna trademastermind, inda yake koyar da mabiyansa 149.8K a TikTok yadda za su iya kai hajojinsu ƙasashen ƙetare, musamman China.

Bakanon yana kuma koyar da nau'in sana'o'in da za su fi karɓuwa idan mutum yana son fitar da kayansa zuwa waje.

Kazalika, mabiyansa na Instagram sun zarta 5.7k.

7. Aisha Abba Grema (aishanbarno)

Matashiyar da aka fi sani da aishanbarno a shafukan sada zumunta, Aisha ta fuskanci akwai ƙarancin malaman harshen Kanuri, abin da ya sa ta buɗe ajin koyar da Kanuranci ke nan a shafukan zumuntarta.

Wannan fa ƙari ne a kan abinci da al'adun Kanuri da ta saba koyarwa ga mabiyanta 71.7k a TikTok da 21k a Facebook, da 40.1k a Instagram, duka a kyauta.

8. Muhammad Dalhatu (bturai25)

Muhammad matashi ne mai baiwar gano yadda ake sarrafa makamashin gawayi domin yin girki cikin kwanciyar hankali.

Zaune a kan keken guragu, bturai25 kan koyar da al'umma yadda ake sarrafa gawayi kuma a yi girki ba tare da kashe kuɗi mai yawa ba, kamar wannan da ya koya yadda ake amfani da diddigar gawayin da ake zubarwa.

Akwai ire-iren waɗannan bidiyo a shafinsa na TikTok da mutum 22k ke bibiya - amma tabbas ba su kaiɗai ne ke amfana ba.

9. Abba Idaris Galadima (A I Engenia Kano)

Engenia Kano - kamar yadda aka fi saninsa a dandalin TikTok - ƙwararren makanike ne da ba shi ɓoye iliminsa.

Shifinsa na TikTok mai mabiya 48.7k cike yake da bayanai kan injinan mota iri-iri, da yadda ake gyaransu, da ma yadda ake gane ko inji ya samu matsala.

Jigari-jigarin makanikai da game-gari irina ka iya leƙawa don sanin ko injiniyan yana da ƙwarewa kan injin motarku don samjun ilimi a kyauta.

10. Kadijah Yumcam

Idan masoya cima - ko rudaye - suka ji labarin abin da Yumcam ke yi a Instagram ɗinta na tabbata sai sun kai ziyara.

Kai waɗanda ma ba rudayen ba za su so su koyi yadda ake girka abinci daban-daban kamar irin wannan dambun da ta koya wa ma'abota BBC Hausa a cikin watan azumi.

Shafinta na Instagram (mai mabiya 52.9k), da na TikTok (2.5k) cike suke da darussan koyi-da-kanka har sai kun darje.