Injiniya dan Najeriya da Turawa ke rububinsa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Malam Hadi Usman wani dattijo ne dan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya wanda ya ƙera abubuwan fasaha da dama.

Hakan tasa Turawa daga ƙasashen da suka ci gaba da dama kamar su Poland da Jamus da Kanada har ma da China suke rububin sayen fasaharsa.

Wasunsu kuma suna buri da fatan haɗa kai da shi don samar da wasu sabin fasahohin.

Daga cikin abubuwan da ya ƙeara a kwai gidan rediyo da jirgin helikwafta da wayar salula tun ma kafin ta shigo Najeriya.

Ya kuma ƙera risho mai aiki da ruwa. A taƙaice dai ya ce ya ƙera abubuwa 45 tun daga shekarar 1975.

Ya shaida wa BBC cewa an taɓa ƙoƙarin ƙona gidansa a wancan lokacin da ya ƙeara wayar hannun, don ba a riga an santa ba a sannan, saboda a cewarsu aljanu ne ke magana a cikin wayar.

A wannan bidiyon, BBC ta yi cikakkiyar hira da shi a kan irin wannan baiwa tasa, inda ya ce mutane da dama sun kasa yarda da baiwar fasahar tasa suna cewa tsafi yake yi.