Shin zuma ya fi sukari aminci ga lafiya?

Zuma da suga

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Zuma wani ɗanɗano ne da ya ɗara sukari zaƙi kuma yake da alfanu sosai, shin zai iya zama abin da za a koma dogaro maimakon suga?

Wata kwararriya kan abinci mai gina jiki Jo Lewin ta yi bayani kan irin alfanun da zuma ke da shi.

Ta yaya ake samar da zuma?

Zuma wani ruwa ne mai zaƙi da kudan zuma ke samar da shi, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen rayuwa da kuma kasancewa abinci mai gina jiki ga kudajen.

Kowane kudan zuma yana samar da matsakaicin rabin cokali na zuma a tsawon rayuwarsa. Idan aka yi la'akari da tarin zumar da ake samarwa a kowace shekara, hakan na nuna cewa kudajen zuma da yawa ne ke wannan aiki.

Akwai kwari da dama da ke iya samar da zuma amma kudan zuma ne kadai yake iya samar da zumar da ake samu a kantuna.

Wannan ba a dare daya ya faru ba, an dauki miliyoyin shekaru.

An fara ambato batun zuma tun rubuce-rubucen zamanin da - an yi amfani da shi a matsayin alfanu na abinci da kuma magani.

Zuma

Asalin hoton, Getty Images

A yau, zuma ya zama abin ɗanɗano mai daɗi da ya yi suna a duniya, kuma ana amfani da shi a wasu kayayyakin da ake ci wanda ke buƙatar sukari, har ma da kayan lemu.

Zuma dai ya fi sukari zaƙi, kuma saboda ɗanɗanonsa kaɗan ma yana iya wadatar da mutum.

Har ila yau, masana sun ce nau'in zuma da ya fi yin baƙi, ya fi ɗanɗano mai daɗi.

Sinadaran da ke cikin zuma

Zuma na ɗauke da sinadarin fructose da ya kai kashi 40, sai kuma sukarin da jiki ke buƙata kashi 40, da ruwa - har ma da sauran sinadarai da suka haɗa da iron calcium, potassium da kuma magnesium.

Sakamakon yawan sinadarin fructose da ke cikin zuma ne ya sa ya fi sukari zaƙi. Nau'in abinci ne da ke da sinadarin carbohydrate.

Ita zuma tana da yawan sinadaran kuzarin da abinci ke samarwa, abin da ke sa ta ɗaga yawan sukarin da ke jikin ɗan'adam.

Cokali ɗaya na zuma zai samar da:

Kuzarin da abinci ke samarwa 58

Gram 15.3 na sinadarin carbohydrates

Gram 0.1 na sinadarin protein

Gram 0 na sinadarin fat

ZUMA

Asalin hoton, Getty Images

Shin zuma ya fi sukari aminci ga lafiya?

Zuma dai tana da wasu sinadarai da ba su cika ɗaga sukarin da ke jikin ɗan'adam ba da sauri. Saboda zuma tana da zaƙi a kan suga, ya sa mutane ke shan ɗan kaɗan.

Ga mutanen da ke da cutar suga ko waɗanda ke ƙoƙarin daidaita yawan sukarin da ke jikinsu, bai dace su maye gurbin suga da zuma ba saboda dukansu suna iya shafar yawan sukarin da ke jiki.

Yana da kyau a kuma tuna cewa, kamar wasu sinadarai, zuma ba ta da "sukari" a cikinta.

Idan ka fi son zuma, ka yi ƙoƙarin zaɓan nau'uka daban-daban - waɗanda ke ɗauke da nau'in sinadarin vitamin da enzymes da sauransu, kuma a kayyade yawan shansa.

Sai dai, mutane da dama sun yi watsi da irin alfanun da shan zuma ke da shi.