Jami'o'i da kwalejojin Najeriya da ka iya amincewa da mafi ƙanƙantar maki a Jamb

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaliban Najeriya da za su kammala makaratun sakandire na neman jami'o'in da za su amince da mafi ƙanƙantar makin Jamb domin samun guraben karatu, saboda mummunan sakamakon jarrabawar shiga manyan makarantu ta Jamb da aka samu a wannan shekara.
Hukumar Jamb - wadda ke shirya jarrabawar da ke bai wa ɗaliban da suka kammala sakandire damar samun shiga manyan makarantu a ƙasar - ta sanar da samun gagarumar faɗuwa a jarrabawar bana.
Jarrabawar 2025 ta kasance cikin waɗanda aka fi samun munin sakamakonsu a tarihin Jamb.
Kusan ɗalibai miliyan biyu ne suka rubuta jarrabawar, amma kusan mutum 12,400 ne suka samu maki fiye da 300.
Kodayake daga baya hukumar ta amince da samun kura-kurai a tsarin gudanar da jarrabawar, waɗanda suka kasance cikin dalilan faɗuwar jarrabawar.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ya nemi afuwar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar da iyayensu, lamarin da ya sa har ya yi kuka a gidan talbijin a ƙasar.
Hukumar ta kuma sake shirya jarabawa ga wasu ɗaliban da lamarin ya shafa, ind ake sa ran fitowar sakamakon a ranar Laraba.
A ƙa'ida duk wanda ya samu maki 200 a jarrabawar, ana kallonsa a matsayin wanda ya ci jarrabawar, kodayake wasu jami'o'in kan bai wa ɗaliban da suka samu maki 180 guraben karatu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To amma a shekarun baya-bayan nan sakamakon rashin cin jarrabawar da wasu ɗaliban ke yi, wasu jami'o'in sun rage makin da suka ƙayyade zuwa 150 domin bayar da gurbin karatu, yayin da a bana ake raɗe-raɗin cewa za su iya ragewa fiye da haka.
Wata ma'aikaciyar jami'ar jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta shaida wa sashen BBC Pidgin cewa kawo yanzu jami'arsu ba ta sanar da adadin makin da za ta ƙayyade a bana ba, ''amma ba na tsammanin zai wuce 140'', kamar yadda ta bayyana.
Haka ma wani ma'aikacin Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da a baya aka fi sani da Jami'ar jihar Anambra ya bayana wa wakilinmu cewa ''Jami'ar ba za ta amince da makin da ya yi ƙasa da 150 ba, musamman ga kwasa-kwasan da ba su danganci kiwon lafiya da fannin shari'a ba''.
Haka shi ma wani ma'aikacin jami'ar jihar Sokoto, ya ce ''ya yi wuri jami'ar ta yanke hukunci kan adadin makin da za ta ƙayyade, kasancewar har yanzu Jamb ba ta kammala fitar da duka sakamakon jarrabawar wannan shekara ba''.
Ma'aikacin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce a watan Agusta ne jami'ar za ta yi zama domin ƙayyade maki da za ta sanya don baya da gurbin karatu, kuma zuwa lokacin Jamb ta bayyana musu a hukumance matakin da za a ɗauka.
Sai dai ya ce ko a shekerar da ta gabata ma maki 140 jami'ar ta ƙayyade domin bayar da gurbin karatu.
Wasu jami'o'in da za su iya amincewa da mafi ƙanƙantar maki a Jamb
Bisa la'akari da abubuwan da suka faru a baya da tattaunawa da wasu ma'aikata ɗaliban wasu jami'o'in Najeriya, ga jerin wasu makaratu da ake ganin za su iya amincewa da mafi ƙanƙantar maki.
- Jami'ar Jihar Abia da ke Uturu (ABSU) - 140
- Jami'ar Jihar Ebonyi - 140
- Jami'ar Jihar Ekiti - 140
- Jami'ar Jihar Delta - 140
- Jami'ar Tarayya da ke Gashua, Jihar Yobe - 140
- Jami'ar Kingsley Ozumba Mbadiwe da ke jihar Imo - 140
- Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke Anambra -150
- Jami'ar Jihar Sokoto -140
- Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto - 140
- Jami'ar Jihar Benue da ke Makurdi - 150
- Kwalejin fasaha ta Akanu Ibiam ta tarayya da ke jihar Ebonyi - 100
- Kwalejin fasaha ta jihar Delta - 100
- Kwalejin fasaha ta jihar Kano - 100
- Kwalejin fasaha ta Tarayya ta Ede da ke jihar Osun - 120
- Kwalejin fasaha ta Ayede da ke jihar Oyo - 120
Bayanan sakamakon Jamb a ƴan shekarun nan

Asalin hoton, Jamb
A shekarar 2022, UTME ta sanar da cewa ɗalibai 378,639 ne suka samu maki samu maki fiye da 200, yayin da ɗalibai 520,596 suka samu maki 190 zuwa sama, sai kuma 704,991 da suka samu maki 180 zuwa sama.
Ɗalibai 934,103 kuma suka samu maki 170 ko fiye, sannan kuma ɗalibai 1,192,057 suka samu maki 160 zuwa sama.
A 2024 kuma jimillar ɗalibai 1,904,189 ne suka rubuta jarrabawar ta UTME, yayin da ɗalibai 1,989,668 suka yi rajistar jarrabawar a 2023.
Hukumar Jamb ta ce daga cikin sakamakon ɗalibai 1,842,464 da ta fitar a bana, kashi 0.4 ne kawai suka samu maki 300 zuwa sama, yayin da kashi 20 suka samu maki 200 zuwa sama.
A 2019 lokacin da aka samu munin sakamakon jarabawar Jamb, hukumar tare da haɗin gwiwar jami'o'in ƙasar sun amince da rage adadin makin da za a ƙayyade domin bayar da gurbin karatu zuwa 160.
Haka ma a zangon karatu na 2022/2023, Jamb ta ƙayyade mafi ƙarancin makin bayar da gurbin karatu ya fara daga 140 zuwa sama, saboda ƙarancin cin Jamb a shekarar.











