Bashin karatu: Ana zargin jami'o'i da bankuna da zambatar ɗalibai

Asalin hoton, NELFUND
- Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Batun rancen karatu ga ɗaliban jami'oi'n Najeriya na neman tayar da ƙura a ƙasar bayan ɗaliban sun ce ana rub da ciki da kuɗaɗensu.
Shugabannin ɗaliban sun zargi shugabannin wasu jami'o'in da noƙe kuɗin rancen karatun na ɗalibai musamman idan sun riga sun biya da kuɗinsu.
"Ana tilasta wa ɗaliban nemo kuɗin makaranta, idan kuma sun biya daga baya sai a ce gwamnati ta turo kuɗinsu, kuma shugabannin makarantar su riƙe," in ji Umar Farouk Lawan mamba a kwamitin zartawa na hukumar bayar da bashin karatu ga ɗaliban Najeriya wato Nelfund kuma Tsohon shugaban ɗaliban Najeriya.
Sai dai wasu jami'oin sun musanta zargin suna riƙe kuɗaɗen ɗaliban da hukumar Nelfund ta tura wa ɗaliban.
Lamara Garba jami'in hulɗa da jama'a na Jami'ar Bayero Kano ya shaida wa BBC cewa babu kuɗin da suke karɓa daga kowane ɗalibi.
"Mu idan ɗalibi ya cika sharuɗɗan rancen, Nelfund za ta tura wa jami'a kuɗin makarantarsa sannan ta tura wa ɗalibi kuɗin kashewa duk wata kai tsaye, don haka ba bin da jami'a take karɓa gun ɗalibi," in ji shi.
A makon da ya gabata hukumar Nelfund ta bayyana damuwa tare da yin gargaɗi ga makarantun kan yadda ake riƙe kuɗaɗen ɗaliban bayan ta turo ba tare da sanar da su ba.
"Wani bincike ya nuna wasu makarantu suna riƙe kuɗaɗen ɗalibai bayan an biya su ba tare da sanar da ɗaliban ba, lamarin da ke haifar da ruɗani," kamar yadda sanarwar Nelfund a ranar 10 ga Afrilu ta bayyana.
Mene ne koken ɗaliban?
Shugabannin ɗaliban sun ce sun samu koke kusan a duka jami'oin Najeriya da ake riƙe kuɗaɗen karatun na ɗalibai.
Ɗaliban sun yi zargin cewa ana rike kuɗaɗen na tsawon lokaci, wani lokaci ma sun yi zargin cewa ana cinye masu.
"Shugabannin makarantun suna barin kuɗin ne a banki har tsawon lokaci don banki ya ajiye su samu riba, a cewar wakilin ɗaliban a hukumar Nelfund.
Ya ƙara da cewa sun yi allawadai da abin da ke faruwa a jami'oin yadda ake riƙe kuɗaɗen wani lokaci ma a cinye
Ya ce sun ɗauki matakai ciki har da shigar da ƙara kotu hukunta shugabannin da aka kama da hannu a lamarin kuɗin ɗaliban.
Martanin wasu Jami'o'in
Wasu jami'oin sun musanta zargin ɗaliban, inda suka nuna cewa akwai ragin haƙuri daga ɓangaren ɗaliban kafin a mayar masu da kuɗinsu da suka biya kuɗin makaranta kafin Nelfund ta turo.
Jami'ar Bayero ta ce Nelfund tana turo wa jami'a kuɗaɗen ɗalibai tare da sunayensu da fannin da suke karatu.
"Idan ɗalibi ya biya kuɗin makaranta kafin Nelfund ta tantance shi ta turo kuɗinsa, ana mayar wa ɗalibai kuɗaɗensu mu a nan Jami'ar Bayero da zarar an turo kuɗaɗen," in ji Lamara Garba jami'in hulɗa da jama'a na Jami'ar Bayero Kano.
Ya ƙara da cewa iya kuɗin da Nelfund ta biya, adadin ne ake mayar wa ɗalibi.
An kafa asusun ɗaliban ne domin ba su rancen kuɗi na makaranta da sauran hidimomi a yayin zangon karatunsu.
Hukumar Nelfund da gwamnatin tarayya ta kafa domin kula da bayar da rancen ta shata ka'idoji kuma sai ɗaliban da suka cancanta da cika sharuɗɗanta za su samu tallafin.
Ƙarƙashin tsarin rancen, ɗalibi ba zai biya bashin da aka ba shi ba har sai bayan shekaru biyu da kammala yi wa kasa hidima.
Wasu ɗaliban na bayyana fargaba kan yadda za a iya tara masu bashin alhali kuma makarantarsu ba ta sanar da su cewa an biya kuɗaɗensu ba.











