Hanyoyin da ya kamata ku bi domin samun bashin karatu a Najeriya
Hanyoyin da ya kamata ku bi domin samun bashin karatu a Najeriya
Jami'i a hukumar bayar da lamunin karatu ta Najeriya, Nelfund Umar Mukhtar ya ce lissafa hanyoyin da ɗalibi mai son samun lamun karatu daga hukumar kamar haka:
- Dole me neman lamunin ya zama ɗalibi
- Dole ne ya mallaki lambar kasancewarsa ɗan Najeriya
- Dole ya mallaki lambar banki ta BVN
- Mkarantar da mutum yake so ta tabbatar da bayanan gamsuwa a kan ɗalibi
Jami'in ya ƙara da cewa bayan ɗalibi ya kammala karatunsa ne sannan bayan shekara biyu da gama yi wa ƙasa hidima lokacin ne ake sa ran zai fara biyan kaso 10 cikin 100 na albashinsa domin fara biyan bashin.
Dangane kuma da batun kuɗin ruwa da wasu mutanen ke shakka, sai jami'in ya ce "babu kuɗin ruwa shi ya sa ma muke kiran sa da lamuni maimakon bashi."
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ɗalibai sama da 40,000 ne suka karɓi bashin karatun.



