Waɗanne takardu ne Amurka za ta fitar kan binciken Tinubu?

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Martanin da gwamnatin Najeriya ta mayar kan hukuncin wata kotun Amurka game da binciken da hukumomin tsaron ƙasar suka yi kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jawo sabon cecekuce kan rayuwarsa a Amurka.
Tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wasu ƴanjarida da kuma masu adawa da takarar Tinubu suka tono labarin da ke cewa hukumomin Amurka sun taɓa binciken shi kan ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, har ma aka ƙwace masa wasu kuɗaɗe a shekarun 1990.
A ranar 8 ga watan Afrilu ne wata kotun Gundumar Columbia da ke Amurka ta bai wa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) da kuma kuma hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (DEA) umarnin su fitar da bayanan binciken da suka gudanar kan Tinubu shekaru 30 da suka wuce.
A ranar Lahadi kuma mai magana da yawun gwamnatin Tinubu ya mayar da martani game da umarnin alƙalin, yana mai cewa "babu wani sabon abu a takardun da za a fitar".
"Babu wani sabon labari. Rahotonnin da Agent Moss na FBI da kuma DEA suka rubuta ya daɗe a bainar jama'a sama da shekara 30. Rahotonnin ba su shafa wa shugaban Najeriya laifi ba," kamar yadda Bayo Onanuga ya bayyana cikin wata sanarwa.
Batun karɓe wa Tinubu kuɗi a Amurka ya ja hankali sosai kafin zaɓen 2023, inda ƴantakarar adawa Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi amfani da shi a matsayin ɗaya daga hujjojinsu na rashin cancantar Tinubu a matsayin ɗantakara.
Sai dai ba su yi nasara ba bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi watsi da iƙirarin nasu.
Me hukuncin kotun ya ce?

Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook
A takardun hukuncin da BBC ta gani, Mai Shari'a Beryl A. Howell ya bai wa FBI da DEA umarnin "karɓa da kuma amsa buƙatar neman bayanai" bisa dokar ƴancin neman bayanai ta Freedom of Information Act (FOIA) da wani Ba'amruke Aaron Greenspan ya aika musu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar kotun, amsar da hukumomin suka dinga bayarwa da ta kira da "Glomar responses" ta yadda suke ƙin tabbatarwa ko ƙaryata bayanin da 'ƴnjarida ke nema.
A tsakanin 2022 da 2023, ɗanjarida mai binciken ƙwaƙwaf Greenspan ya nemi bayanan a kan Tinubu da wasu mutum uku Lee Andrew Edwards, Mueez Adegboyega Akande, Abiodun Agbele, waɗanda aka yi zargin suna da alaƙar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.
Sau shida Greenspan yana tura buƙatun neman bayanan a ma'aikatun gwamnati da dama game da wani gungun masu ta'ammali da hodar ibilis a Chicago a shekarun 1990.
Sauran ma'aikatun da ɗanjaridar ya rubuta wa wasiƙa sun ƙunshi ma'aikatar harkokin waje, da hukumar leƙen asiri ta CIA, ta tattara haraji Internal Revenue Service (IRS).
A cewar takardun shari'ar, biyar daga cikin ma'aikatun sun bayar da amsar "Glomar response" - wato sun ƙi musantawa ko tabbatar da bayanan.
Daga baya ne Greenspan ya shigar da ƙara a kotu domin ƙalubalantar ma'aikatun game da 'yancinsa na neman bayanai da dokar FOIA ta ba shi.
Hukuncin da Mai Shari'a Howell ya bayar a ranar Talatar ya ce amsar da FBI da DEA suka riƙa bayarwa ba ta dace ba.
Alƙalin ya kuma ce ma'aikatun sun kasa bayar da gamsasshiyar hujjar cigaba da riƙe da sirranta bayanan.
"FBI da DEA sun tabbatar da binciken da suka yi kan Tinubu mai alaƙa da safarar miyagun ƙwayoyi - saboda haka duk wani abu da zai biyo baya game da bincken, to buƙatar jama'a ta sanin abin da ya faru ta fi ƙarfin ɓoye bayanan da ake yi.
Me ɗanjaridar ke so a bayyana?
Babban abin da Mista Greenspan ke nema shi ne fitar da bayanan abin da binciken FBI da DEA ya ƙunsa game da Tinubu da sauran waɗanda aka zarga, da kuma sakamakon abin da ya gano.
Aaron Greenspan ya ce yana fatan za su bi umarnin kotun.
Kotun ta bai wa sauran waɗanda ake ƙara a shari'ar umarnin su bayar da rahoto zuwa 2 ga watan Mayun 2025 game da matsayin sauran lamurran da ke tattare da batun, kamar yadda yake ƙunshe a hukuncin da ta yanke.
Gwamnatin Najeriya ta ce lauyoyi na cigaba da nazarin umarnin kotun, amma ba ta bayyana ƙarara ko za ta yi ƙarin bayani ba bayan kammala nazarin.











