Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matsalar kisan mata ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a duniya
Matsalar cin zarafin mata musamman ma abin da ya danganci kisa abu ne da ke ci gaba da wanzuwa a sassan duniya, kamar yadda bincike ya nuna.
Yayin da ranar 25 ga watan Nuwamba ta kewayo - wadda rana ce ta yaƙi da cin zarafin mata - mun yi duba a kan rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a kan matsalar kisan mata a shekarar da ta wuce ta 2023.
Rahoton wanda ya ƙunshi batun kisan mata a hannun abokan zamansu ko 'yan uwansu na nuni da cewa a duniya wannan matsala har yanzu tana nan daram sai ma ƙaruwa take yi a sassan duniya daban-daban.
Binciken ya nuna cewa a faɗin duniya baki ɗaya an kashe mata da 'yan mata 85,000 da niyya a 2023.
Kuma kashi 60 cikin ɗari kisa ne na niyya - inda 51,000 - ya kasance kisa ne da abokan zama ko miji ko saurayi, ko dangi suka yi wa matan.
Ƙiyasi ya nuna cewa mata da 'yan mata 140 ne ke mutuwa a duk rana a hannun miji ko saurayi ko wani dangin matan, wanda hakan ke nufin a duk minti 10 ana kashe mata ko yarinya a duniya.
A shekarar da ta gabata kamar yadda muke bayani matsalar kisan matan da 'yan mata ta fi tsanani a nahiyar Afirka sai kuma Amurka ta Arewa da ta Kudu ke bi mata baya sannan sai nahiyar Osheniya (Oceania) da ke zaman ta uku.
A Turai da yankin nahiyar Amurka ta Arewa da ta Kudu yawancin mata ana kashe su ne a gida, wato mazajensu ko samarinsu ne ke kashe su, yayin da a sauran wurare kuma 'yan uwa ko danginsu ne ke kashe su.
“Matsalar cin zarafin mata da 'yan mata ba aba ce da ta fi ƙarfin magancewa ba - matsala ce da za a iya maganinta - abin da muke buƙata shi ne dokoki masu tsauri, da inganta tara alƙaluma, da dagewar gwamnati kan gaskiya, da rashin nuna sassauci da ƙara samar da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin fafutukar kare 'yancin mata da kuma na hukuma.
Yayin da muke tunkarar bikin shekara 30 da ƙaddamar da dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya kan 'yancin mata a Beijin da kuma ƙudurin tabbatar da 'yancin yara da sauran al'umma a 2025, lokaci ne da ya kamata shugabannin duniya su haɗa kai su aiki tuƙuru cikin gaggawa tare da samar da duk abin da ake buƙata na ganin bayan wannan matsala", kamar yadda babbar darekta ta mata a Majalisar Ɗinkin Duniya, Sima Bahous ta ayyana.
Ita kuwa shugabar hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi da aikata miyagun laifuka ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Ghada Waly, cewa ta yi;
“Sabon rahoton na kisan mata ya nuna matuƙar buƙatar da ake da ita kan samar da dokoki da hukunci na shari'a mai masu tsanani da za a riƙa hukunta masu aikata lafin, tare da tallafa wa waɗanda aka ci zarafin yadda ya kamata, ciki har da samar da hanyoyin bayar da rahoton matsalar.
Jami'ar ta ƙara da cewa: “Haka kuma dole ne mu yi yaƙi na kawar da dukkanin wasu bambance-bambance da ke cutar da mata a fannin mulki da kuma al'adu da ke nuna musu bambanci, waɗanda ke ƙara ta'azzara cin zarafin matan.
“Yayin da ake fara kamfen na wannan shekara na fafutukar kare 'yancin mata da 'yan mata, dole ne mu tashi tsaye a yanzu domin kare rayuwar mata,” in ji ta
Yayin da bikin cika shekara 30 da ayyana dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya na kare 'yancin mata ke ƙaratowa a 2025, haɗi da cikar wa'adin shekara biyar da na aiwatar da shirin cimma muradun cigaba mai ɗorewa na Majalisar, hakan ya bayar da muhimmiyar damar haɗa kan masu ruwa da tsaki don su ɗauki ƙwararan matakan da suka dace na tabbatar da 'yancin mata.
Wannan ya haɗa da kawo ƙarshen cin zarafin mata da 'yan mata ba tare da hukunci ba.
Kwana 16 na fafutukar yaƙi da cin zarafin mata:
A cikin kwanaki 16 na fafutukar, hukumar mata ta Majalisar Ɗinkin Duniya za ta nemi mahukunta su farfaɗo da ƙudurin tabbatar da gaskiya da adalci.
A wannan shekara za mu yi bikin cika shekara 25 na ranar duniya ta yaƙi da cin zarafin mata inda za a yi taro na musamman a birnin New York ranar Litinin - 25 ga watan Nuwamba - inda za a nuna matakan da suka fi dacewa na yaƙi da cin zarafin mata da sauran matsaloli da ke tarnaƙi ga wannan ƙuduri da kuma yadda za a samu cigaba.
An ƙaddamar da wani maudu'i na shafin sada zumunta da muhawara na duniya kan yaƙi da matsalar cin zarafin mata- inda za a yi amfani da - #NoExcuse da kuma #16Days.
Yadda matsalar take a Najeriya
Kamar yadda rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa nahiyar Afirka ita ce kan gaba wajen yawan matsalar cin zarafin mata, da takan kai har da kisan matan, a takanin abokan zama ko danginsu, mun karkato ƙasa-ƙasa a cikin nahiyar domin sanin yadda lamarin yake a ƙasa mafi yawan al'umma a nahiyar ta Afirka - Najeriya.
Hajiya Hafsat Baba - mai fafutuka, kuma tsohuwa Kwamishinar Kula da Ayyukan Jinkai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, kuma tsohuwar Kwamishinar Mata, ta sheda wa BBC cewa rahoton da ya nuna ƙaruwar matsalar a duniya musamman Afirka haka yake, idan aka waiwayi Najeriya ma.
Ta ce wani abu da ya sa a yanzu ma suke ganin ta'azzarar matsalar shi ne matsalar tsadar rayuwa, inda ta ce a yanzu abin da suke gani shi ne ɗan ƙaramin abu da bai taka kara ya karya ba sai ya haddasa rikici a zamantakewa fiye da shekarun baya.
''Kowa zuciyarshi tana wuya za ka ga ɗan abin da bai taka kara ya karya ba sai ya kai ga duka a tsakanin ma'aurata wani lokaci dukan ya yi tsanani har ya kai ga rasa rayukan,'' in ji ta.
Haka kuma mai fafutukar ta ce matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya musamman a arewa ita ma ta ƙara janyo ƙaruwar wannan matsala ta cin zarafin mata da ma kisansu.
''Akwai wata al'ada tamu a nan Arewa wadda ba a cika magana ba idan ana samun saɓani a zamantakewa sai a ce a rufe magana kar ta fita - to wannan yakan kai tun daga zage-zage tsakanin ma'aurata har a kai ga duka wani lokaci har a rasa ra,'' in ji ta.
Ta ce a yawancin lokaci idan aka kai hari gari ko wata makaranta mata abin ke shafa inda ake kama su a tafi daji da su ana wulakanta su ta hanyar lalata a gaban 'ya'ya ko iyaye - kuma hakan yakan taɓa hankalin mace ta inda ko an kai ta wani wajen gyaran hankali ko tunani wannan ɓacin rai ba zai rabu da ita ba - baya ga haka ma wasu matan da dama kan rasa ransu a irin waɗannan hare-hare da cin zarafi.
Dangane da alƙaluma kuwa mai fafutukar ta ce a Najeriya abu ne mawuyaci samun alƙaluman yawan matan da ake cin zarafi ko ma waɗanda ake kashewa.
''Ba za a ce babu ba ko kuma da akwai saboda ka san yawanci alƙaluma irin waɗannan muna da sakaci a kansu,'' ta ce.
Tsohuwar kwamishinar ta ce ba za ta manta ba a shekara ta 2022 lokacin tana riƙe da muƙami, sun samu alƙaluma na matan da aka ci zarafinsu a jihar Kaduna har 2,680 a wannan shekara.
Hajiya Hafsat ta ce wata matsala ma a cikin al'umma ko ma da ana da tsarin tattara bayanai ko alƙaluman akwai wasu da dama da ba za su kai da kundin ba saboda ba a kai rahoto ko ma kai ƙara domin a bi haƙƙi, saboda abubuwa da dama - kama daga rashin hukunci mai tsanani ko tabbatar da gaskiya da adalci da sauransu.