Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda cin zali ke shafar ƙwaƙwalwar yara
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Jornalist
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja
Ga yara da dama da ke fuskantar cin zali a makaranta, tabon da cin zalin ke bari a rayuwarsu abu ne me zurfi kusan a ce fiye da ciwon da ke kan fatarsa.
Asusun kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) ta ce damuwar da al'ummar duniya ke nunawa tana ta'azzara a kan buƙatar tsare lafiyar kwakwalwar daliban makaranta
A tattaunawarsa da BBC, Emmanuel Paul Asan, ƙwararen likita kan tunanin ɗan adam da ke aiki a asibitin Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya bayyana cin zali tsakanin yara a matsayin wadansu halayya da ke faruwa tsakanin yara a makaranta da suka haɗa da zage-zage da neman faɗa, da zolaya, da duka da sanyawa mutane wadansu irin sunaye da ba su dace ba da dai sauransu.
Nau'ikan cin zali
Dakta Asan ya ce cin zali ya kasu kashi-kashi kuma ya ƙunshi;
- Cin zali na jiki: Wanna ya haɗa da duka da harbin dutse ko wani abu daban da tofawa wani yaro yawun baki da laƙawa wani yaro sata da ƙwacewa sauran yara kayansu da sauransu.
Likitan ya ce yayin da cin zali na jiki ke haifar da lahani ga jikin yaro, wannan nau'in cin zalin na haifar da lahani na tunani.
Irin wannan mugun nufi da wulaƙanci daga wasu yaran na lalata tunanin yaran da aka zalunta na kansu da na matsayinsu a makaranta har da ma matsayinsu a duniya.
- Zage-zage: Wannan ya haɗa da zagi mai cutarwa da zolaya da kiran wasu yaran da sunayen da bai dace ba saboda wani yanayi na halittarsu da wulaƙanci, da tsoratarwa, da kalaman nuna wariya har da na launin fata da cin zarafi da aibantawa, da cin zalin yaran da ke yawan shiru ko ba su cika magana ba da dai sauransu.
- Cin zalin da jama'a suke yi: Wannan ya haɗa da harara domin tsoratarwa da cire wasu daga cikin wasu kungiyoyi, da tsegumi ko yaɗa jita-jita, da sanya wasu su zama kamar wawaye, da lalata mutuncin mutum da dai sauransu.
- Cin zali a shafukan sada zumunta: A nan kuwa, za a ga yadda ake yaɗa abubuwan tsana idan wani ya ɗora hotonsa ko ya wallafa wani saƙo, da har zai saka mutum ya ji kamar duk an fi shi a duniya, wasu ma har suna kashe kansu kan irin waɗannan abubuwan, in ji likitan.
- Cin zali na launin fata: Wannan ya haɗa da wulaƙanta mutane saboda ƙabilarsu ko kalar fatarsu ko al'adarsu da sauransu.
- Cin zali kan addini: Wannan kuma ya haɗa da zaluntar mutane saboda asalin addininsu ko aƙidarsu in ji likitan.
- Cin zali kan masu nakasa: Wannan shi ne kin yi hulɗa da wani ko gudun wani ko yi musu mugun nufi saboda suna da nakasa da sanya wani ya ji ba daɗi, ko yin barkwanci don cutar da wani saboda rashin lafiya ko nakasa.
- Cin zali na jinsi: Wannan ya hada da yi wa wasu mutane mugun nufi, ko sanya musu rashin jin daɗi saboda jinsinsu ko yin barkwanci kan jinsin mutum ko taɓa mutum ba da izininsa ba ko kuma yaɗa jita-jita ta jima'i, in ji dakta Asan.
Likitan ya ƙara da cewa irin waɗannan cin zali na haifar wa da yara da dama matsaloli na rashin girmama kansu ko kuma ga kisa ma, ko ya kai su ga aikata wasu abubuwan da ba su dace ba saboda kawai suna son su shiga yanayi na zamani.
Illolin cin zali tsakanin yara
Dakta Ansa ya ce ainihin cin zali na farawa ne daga makaranta, inda yaro zai je makaranta ya hadu da wasu yaran kuma su fara cin zalinsa ta fanni daban-daban wanda ke haifar da illoli iri-iri.
Likitan ya ce illolin cin zali sun ƙunshi;
- Yawanci yaran da ake zalunta ba sa samun ci gaba ta fannin karatu saboda idan yaro ya zauna a aji kuma malami na koyarwa, tunaninsa da hankalinsa ba ya tare da malamin sai dai tare da waɗanda suke cin zalin sa, tunanin abubuwan da za su masa idan suka fita daga aji da sauransu.
- Ihu a cikin barci: Illa ta biyu ita ce za a ga yaro yana yawan ihu a barcinsa ko mafarke-mafarke ko kuka ko kuma ba ya samun isashen bacci da dare yadda ya kamata wanda ba wani abu ke janyo hakan ba face tunane-tunane iri-iri.
- Wasu yaran na samun tunanin kashe kansu.
- Yaran da ake cin zali suna ɗaukar kansu a matsayin su ba kowa ba ne saboda tsananin cin zalin da suka fuskanta.
Likitan ya ce iyaye su kasance suna kulawa da bincike da kyau idan sun lura da irin waɗannan illoli game da ƴaƴansu.
Ta yaya cin zali ke shafar ƙwaƙwalwar yaro?
Likitan ya ce cin zali na shafar ƙwaƙwalwar yaro ta fanni daban-daban. Sun hada da
- Haifar da ciwon ƙwaƙwalwa.
- Mutum na iya kamuwa da hawan jini tun yana yaro har ya girma
- Likitan ya ce cin zali na iya saka yaro ya kasance cikin rashin kwanciyar hankali da ƙunci da tsoro da bacin rai har girmansa.
- Cin zalin yaro na iya jefa yaro cikin damuwa har idan ya girma ko da ace an daina zagin sa ko cin zalinsa."
- "Yara na iya samun tananin da bai kamata ba, kamar irin ba su da matsayi, sauran mutane sun fi su, suna ƙasƙantar da kansu, ko da sun san abu a aji, su kasa magana da sauransu."
- "Wasu yaran da aka zalunta suna girma da yunƙurin kashe kansu saboda tsananin cin zalin da aka yi musu."
- Cin zali na iya jefa yaro cikin damuwa har idan ya girma ko da ace an daina zagin sa ko cin zalinsa kamar yadda Hauwa Ahmad Aminu, wata uwa da aka taba cin zalin ɗiyarta, Zainab Ahmad Aminu a makaranta ta shaida wa BBC.
Hauwa ta ce a lokacin da ƴar ta ke makaranta, a ƙaramar sakandare, an ba ta shugabar ɗalibai lamarin da ya haddasa kishi tsakaninta da wata inda ta yi amfani da yara suka dinga cin zarafin ƴarta wadda har suka kai ga yi mata barazana da rayuwarta.
"Hakan ya jefa ƴata cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali har ta kasance tana yawan suma da jijiga wanda har yayi mata illa.
"Mun yi shekara bakwai muna fama, mun je asibiti sau da yawa har da nasu Landan da Dubai, da Indiya, da Saudiyya har ma Cairo, amma duk inda muka je sai likitocin su ce mana damuwa ta riga ta yi mata yawa a ƙwaƙwalwarta wanda daga nan ƙwaƙalwarta ta fara shanyewa har hakan ya yi sandaiyar mutuwarta."
Uwar ta ce ba su gano matsalar cin zalin da ƴarta ke fuskanta a makaranta ba da wuri saboda ta ƙi fada musu abin da ke faruwa kasancewa tana cikin tsoro.
Shin akwai abubuwan da ke sa wasu yaran su ji sun fi wasu rauni?
Dakta Asan ya ce wasu yaran da suka tashi daga iyalan da marasa ƙarfi ne na ji kamar sun fi rauni ko ba su kai matsayin wasu ba.
"Yaro zai iya ganin cewa babansa keke yake hawa kuma da keken yake kai shi makaranta yayin da kuma wasu yaran da motoci ake kai su makaranta, yaron zai ji kamar shi ƙarami ne, bai kai matsayin sauran ba, saboda haka zai ji kamar ya fi su rauni."
"Ko kuma yanayin abincin da suke kai wa makaranta ma na iya sa wani yaron ya ji sauran sun fi shi."
"Wasu yaran da ba su da kokari ko saurin fahimta a aji kuma suna iya jin cewa sauran yaran sun fi su, ganin yadda malaman ke fifita su sama da su da dai sauransu."
"Wasu yaran kuma da ke da nakasa ko wata cuta ma na iya jin kamar sun fi sauran yaran rauni."
Likitan ya ce irin waɗannan abubuwa na iya kai wa ga cin zali da kuma ƙasƙanta mutum.
Ta yaya iyaye da malamai za su gane ana cin zalin yaro?
Daktan ya ƙara da cewa idan aka tashi cin zaliN wani yaro, ba a yi a gaban iyayen yaron ko malamansa ba, cin zalin suna faruwa ne a lokacin wasa ko kuma lokacin da babu malami a aji.
Ya ce yadda iyaye da malamai za su gane cewa ana cin zalin yaro shi ne duba halayen yaro da ɗabi'arsa ballantana idan yana yin wasu abubuwan da bai dace ba, kamar yaro ya kasance yana yawan kuka idan an ce masa ya je makaranta ko kuma idan yana tsoron amsa tambaya a aji.
"Idan kuma yaro ba ya samun isashen bacci ko ba ya cika wasa, yana yawan keɓe kansa gefe ɗaya, to ya kamata iyaye da malamai su binciki yaron su ji."
"Idan yaro ba ya son shiga cikin abokansa wajen wasa ko wani abu daban, yana ƙi, shi ma ya kamata iyaye da malamai su ankara kuma su ɗau mataki."
Liktan ya ce idan iyayen yaron ko malamansa suna son su tutuɓe shi, ka da su yi hakan ta hanyar amfani da tsoro ko riƙe bulala ko wani abu, sun tutuɓe shi a hankali, cikin lumana.
Za a iya maganace matsalar cin zali?
Dakta Asan ya ce akwai wasu abubuwan da iyaye ya kamata su dinga la'akari da su, kamar irin abubuwan da suke koya wa yaransu da kuma faɗa musu ta ɓangaran addini da kuma hulɗa da mutane.
Ya ce iyaye da malamai su kasance suna koya wa yara yadda za su girmama sauran yara ko da kuwa a ce akwai babanci tsakaninsu ta fannin kuɗi, yanayin rayuwa da sauransu.
Ya kuma ce iyaye da malamai su kasance suna koyawa yara abubuwan da al'umma za su amince da shi.
Ya kuma shawarci wasu iyaye da su dage wajen yi wa ƴaƴansu gyara ko da kuwa ba za su ji dadin hakan ba, ba ta hanyar duka ba ko amfani da tsoro sosai ba.
Ya kuma ce malamai da masu makaranta su kasance suna sa ido sosai kan al'amuran yara a makaranta kuma su rage fifita wani yaro sama da sauran.
Ya ƙara da cewa iyaye su kasance suna koyar da halayyar kirki da tausayawa ga yara.
Ya shawarci malaman makaranta na boko da na addini su dabbaka fahimtar al'umma a cikin azuzuwan, ya ce hakan na iya rage abubuwan da ke haddasa cin zali.
Likitan ya ce iyaye da malamai su dage wajen fahimtar sabbin halayen yara kamar su yawan harara da zolayar wasu da dariyar ƙeta da shiga matsalar da ba ruwansa da dai saurasu.
Likitan ya kuma ba da shawarar shiga tsakani ko shirye-shiryen shawo kan cin zali da za su nuna tasiri wajen magance irin wannnan matsalar ta cin zali.