Cin zarafin mata: 'Na saba da dukan da mijina yake min'

    • Marubuci, Daga BBC Monitoring
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Essential Media Insight

Muryar Maryam ta girgiza jama'a da dama bayan ta bayyana abin da ya faru tsakaninta da mijinta lokacin da ya ci zarafinta a bainar jama'a.

"Yadda mutane suka dauki abin kamar ba laifi ba ne miji ya doki matarsa. Babu doka akan haka, kuma babu wani gida da ya tsira, ko 'yan sanda ba za su iya komi ba akai. Wasu gidajen kuma sai su rika ikirarin sun waye suna cewa 'Kai wannan ai matsalarku ce ta iyali'."

Ba kasafai ake jin irin labarinta ba a kasarta Iran, amma tun bayan kirkirar manhajar Podcast da ake wallafa murya ta cikinta, mata da dama suke bayyana irin yadda suka fuskanci cin zarafi.

Maryam ta samar musu da wani kwarin gwiwa (ba sunanta ba ne na gaskiya amma) ta yadda za su yi amfani da manhajojin zamani su furta abin da suka dade yana damunsu, domin kalubalantar wasu dabi'un al'ada marasa kyau a cikin al'umma.

'Matsalar iyali'

Maryam mai shekara 34 ta hadu da mijinta a jami'a inda ta karanci ilimin halayyar kananan yara.

Ta bijirewa iyayenta da ke Tehran kan cewa sai ta auri mijin da take so, wanda take wa kallon mai saukin ra'ayi mai fafutukar ba da 'yancin aiki.

Amma kwanaki kaɗan gabanin aurensu, sai ta gano akwai lauje cikin naɗi. Ta cikin manhajar ta bayyana yadda 'fatanta da kuma yadda ta yi saurin karɓar faduwa' ya kuma hana ta neman taimako daga iyayenta.

Ta jurewa walakanci na zahiri da na boye yayin aurenta, lokacin da abin ya ƙazanta da kanta ta yarda ta yi kuskure.

Bayan duka wadannan abubuwa, kamar dai ko wacce mace a Iran Maryam ta ta shi da iyayenta masu matsagaicin karfi: " Mace za ta shiga gidan mijinta da fararen tufafi na aure kuma a barta cikin farinsu."

Maryam ta ce al'adu da yawa da aka yarda da su a cikin al'umma ne suka hana ta fitowa daga gidan mijinta da wuri.

A al'adar 'yan Iran matsalar iyali abu ne na sirri da ba a fiye bayyana ta ba. Sakamakon haka ne cin zarafi ya zama kamar wata wutar daji, a kasar kuma kullum a ana shawartar mata da su yi shiru kan matsalar iyalansu.

A karshe dai Maryam ta yanke shawarar ta bar gidan mijinta bayan dukan da ta sha a hannunsa wanda ya janyo aka kwantar da ita a asibiti. Bayan farfadowarta daga suman da ta yi, ta kasa mutsawa saboda munanan raunukan da ke jikinta, sai ta tambayi kanta : "Me ya kawo ni nan me yasa hakan ya faru da ni?"

Bayan 'yan satuttuka, sai aka sallameta daga asibiti nan da nan ta shigar da kuken a raba aurensu. Sai kuma aka yi sa'a iyayenta suka goyi bayanta - amma ba duka wadanda suka shiga irin halinta ba ne ke samun wannan sa'ar.

A ko wanne zango na Podcast, sai wata mace ta daban ta zo ta bayyana irin cin zarafin da ta fuskanta ko take fuskanta daga wajen namiji ko wani dan uwanta.

Sabuwar doka?

Kamar yadda suke samun labaran mutane, shirin Podcast din na auna yadda mata ke gaza samun kariya musamman wadanda ake cin zarafi ta hanyar iyali.

Bayanan da aka buga a hukumance na karshe a Iran an wallafa su ne shekara 16 baya, wanda ya gano biyu cikin uku na matan Iran na fama da wannan matsala.

Kugiyar Amnesty da ke zaune a Landan cikin wani rahoto da ta fitar kan Iran a 2013 ta ce, matan kasar na "fuskantar mariya a dokoki da kuma wasu mu'amaloli masu alaka da aure da saki, da gado da rikon yara da dokokin cikin gida da kuma tafiye-tafiye zuwa wasu kasashe".

Wani kisa da wani mahaifi ya yi wa 'yarsa a matsayin wata al'ada da suke kira kisan fitar kunya ya sanya shugaban kasar Hassan Rouhani ya bukaci cikin gaggawa a sake bibiyar ƙudurin da ke kare hakkin mata. shekara 10 a kalla bayan watsi da aka yi da shi.

Kudurin na bukatar 'yan majalisar kasar masu ra'ayin rikau su amince da shi sannan ya zama doka - zai samar da wani sauyi babba kan 'yancin mata a karon farko tun bayan juyin-juya-hali da aka samu a 1979.

Za ta rika daukar cin zarafin mata na zahiri a matsayin babban laifi, kuma a karon farko za a samar da hukuncin walakanta mata a zahiri da kuma kafafen sada zumunta.

Shekara biyar bayan mutuwar aurenta, amma Maryam ta ce ba ta taba jin dadin rayuwarta ba.

Ta yi amannar cewa bai wa mutane 'yanci furta albarkacin bakinsu zai kawo karshen wannan mummunar al'ada, wadda ta yi koke akai, "ta kuma yi maganin masu cin zarafi."