Darajar kuɗaɗen Afirka: Wasu na kuka wasu na dariya

Tarin dalilai sun haɗu sun tura tattalin arziƙin duniya cikin hargitsi a shekarun baya-bayan nan.

Da farko dai annobar korona wadda ta ɓulla a 2020 ce ta kusan dakatar da harkokin kasuwanci, da kuma mamayar ƙasar Ukraine da Rasha ta yi a watan Fabrairun wannan shekara.

Ga ƙasashen Afirka, sun fara shiga rikici ne tun ma kafin bayyanar waɗannan matsaloli na duniya.

Nauyin biyan bashin da ke kansu yana ta ƙaruwa, farashin wasu kayayyaki ya faɗi, lamarin da ya zabge yawan kuɗin ƙasashen wajen da wasu ƙasashe ke samu.

Da wannan, lamari ya taɓarɓarewa kuɗaɗen ƙasashen Afirka masu yawa ke nan idan aka kwatanta da darajar dalar Amurka.

Sai dai a baya-bayan nan kuma, labarin ya zama biyu da kuɗaɗen ƙasashen da darajarsu ke bunƙasa da kuma kudaɗen da darajarsu take daɗa ɓalɓalcewa a kan dalar Amurka.

A tsawon wannan shekara, darajar kuɗin Zambiya wato Kwacha ta ƙaru fiye da sauran kuɗaɗen duniya idan an kwatanta da dalar Amurka.

Darajarta ta ƙaru da kashi 15% zuwa yanzu a 2022 inda aka canzar da kwacha 15.93 a kan dalar Amurka ɗaya a ranar Talata.

Ƙwararru sun ɗora wannan nasara a kan ƙoƙarin da shugaban ƙasar Hakainde Hichilema ya yi na farfaɗo da tattalin arziƙin Zambiya, akasari ta hanyar sake tsarin basukan ƙasashen waje da ke kan ƙasar don harkoki su ɗore ga Zambiya.

A watan Satumba, ƙasar da ke yankin kudancin Afirka ta cimma wata muhimmiyar yarjejeniya da Asusun Lamuni na Duniya inda ya ba ta bashin ceto tattalin arziƙi kimanin $1.3bn.

Kuɗin za su farfaɗo da muhimman tsare-tsaren tattalin arziƙin rayuwar al'umma kamar samar da kuɗaɗen gudanar da makarantu da asibitoci yayin da gwamnati ta shiga ƙoƙarin sake sasantawa da China da sauran masu ba da rance a kan hanyar da za ta biya basuka masu tsadar kuɗin ruwa.

Matakin ya dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari na ƙasashen waje kan ƙasar mai arziƙin ma'adanin tagulla.

Hakan ya kuma rage kaifin hauhawar farashi a daidai lokacin da hatta ƙasashe mafi ci gaban tattalin arziƙi a duniya ke fama da farashin kaya ba ji ba gani.

Hauhawar farashi a Zambiya ya faɗi daga tashin da ya yi zuwa kashi 21% a watan Okotoban bara zuwa kashi 9.9% a cikin watan jiya.

Can kuma inda kuka nufi yamma zuwa Ghana, darajar cedi tana inda kwacha yake a shekara ta 2015.

Ranar Litinin, cibiyar bin diddigin darajar kuɗaɗe ta Bloomberg da ke nazari kan kuɗin ƙasa 148, ta sanya cedi a matsayin kuɗi mafi faɗuwar daraja a duniya.

Da tsakar ranar Talata, an sayar da cedi 11.64 a kan dalar Amurka ɗaya. Hakan ya nuna faɗuwar kashi 48% na darajar kuɗin na Ghana a cikin wata goma sha biyu.

Darajar cedi ta faɗi ƙasa warwas ne saboda masu zuba jari na ƙetare ba su da ƙwarin gwiwa a kan Ghana, inda suka riƙa watsar da takardun lamunin ƙasar da aka fi cinikinsu da dalar Amurka daga harkokinsu na Ghana.

A cewar Babbar Cibiyar kula da Hada-hadar hannayen jari ta ƙasar, jimillar takardun lamuni na gwamnati da na kamfanoni da ke hannun masu zuba jari na ƙasashen waje ta ragu zuwa kashi 12.3% a watan Agusta.

Hakan ya sa Ghana ta kasa samun bashi mai rangwame daga kasuwannin ba da rance na duniya, haka kuma wata yarjejeniyar karɓo bashin $3bn irin wadda ƙasar Zambiya ta samu daga Asusun Lamuni na Duniya cikin gaggawa har yanzu ana tattaunawa a kai.

Sakamakon haka, tsadar rayuwa a Ghana ta yi matuƙar ƙaruwa a cikin shekara ɗaya da rabi, yayin da hauhawar farashi ta kai kashi 37.2% a watan Satumba.

A ranar Litinin, sai da 'yan kasuwa a birnin Accra suka yi barazanar rufe harkokinsu, karo na biyu ke nan a cikin wata biyu, inda suke kokawa kan tsadar gudanar da kasuwanci a ƙasar.