Masu cewa babu kuɗi a Najeriya sai an ciyo bashi karya suke, in ji Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban kasa kuma jagoran sabuwar jam’iyyar hamayya ta NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce babu kanshin gaskiya a batutuwan da masu mulki da gwamnatoci ke yi cewa babu kuɗi a Najeriya har sai an ciyo basussuka domin gudanar da ayyuka.

A wata hira da ya yi da BBC, sanata Kwankwaso ya ce shi ya sa ni kuma ba zai daina faɗin cewa akwai isassun kuɗaɗe a Najeriya ba, duk wani bashin da ake zuwa a ciyo na karya ne.

Sanata ya ce lokacin da ya samu dama ya nunawa al’ummar jihar Kano irin wadannan misalai, domin a koda yaushe mutane ne ke wacaka da dukiyar kasa.

'Na gaji bashi kuma na biya'

Sanata ya bada misali da lokacin mulkinsa na farko a matsayin gwamnan Kano a 1999, inda ya ke cewa ya gaji bashi kuma ya biya, kuma bai bar kowanne bashi ba lokacin da ya sauka daga mulki, sannan ko a 2011 ya tarar da manyan basuka, kuma suma ya biya.

Ya ce mutanen ba sa son gaskiya ne, musamman idan ana riƙe da muƙaman gwamnati.

Ɗan takarar ya ce shi ba zai iya cewa ga makin da zai bai wa gwamnati da ke ci ba, amma sanin kowa ne cewa Najeriya na cikin tasku da rashin tsaro.

“Kullum ana kashe mutane, Kullum mutane na tserewa, Kullum ana raba mutane da muhallansu.

“Ina dai ci gaba da jan hankalin gwamnatin Najeriya domin ta duba ta ga ta wani fanin za ta kawo wa ‘yan kasar nan sauki.

“Talauci ya yi wa mutane yawa, ga malaman makaranta ga marasa galihu da kowa na cikin mumunan yanayi, in ji Kwankwaso.

Babu batun zan marawa wani ɗan takarar baya

Sanata Kwankwaso ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yi cewa babu mamaki ya marawa ɗaya daga cikin ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar Najeriya ta APC ko PDP baya.

Kwankwaso ya ce karerayin mutane ne kawai da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, marasa daraja.

Ya ce “ana dauko tsofaffin hotuna ana haɗawa, wasu kuma na rubuce-rubuce batar da mutane, da sunan yaudara.

“Dama a harkar siyasa mutane ba sa kunya kuma sun iya yaɗa farfaganda da nuna rashin daraja da rashin tsoron Allah.

“Amma abin jin dadin shi ne masu zaɓenmu babu ruwansu da irin waɗannan abubuwan da ake yaɗawa, kuma muna da karfin gwiwar za a zaɓe mu.

Ya ce ya na samun goyon-baya, saboda kowa ya nuna fuskarsa da kuskuransu a baya kuma mutane na fahimta.

Sanata ya ce duk da tunanin mutane kan yadda ake sauya sheka, su babban abin da suka sanya a gaba shi ne batun akida, wanda a baya babu irin wadannan tunanin.

Tsohon gwamnan na Kano ya bada misalai irin na baya lokacin da aka kafa koma mulkin dimokuraɗiya a 1999, yana mai cewa batu da aka rinƙa yi shi ne na yada za a kori mulki soja, ba wai tunanin kafa kasa domin sama mata ci gaba ba.

Sanata Kwankwaso na fatan samun nasara a zabukan 2023, domin kawo na shi sauyin.