An yi ruwan bama-bamai a birnin Port Sudan

Asalin hoton, Reuters
An kai harin jirage marasa matuka a rana ta uku a jere a birnin Port Sudan na kasar Sudan.
Kafafen watsa labaran kasar sun bayyana cewa an samu munanan fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin saman birnin, lamarin da ya sa aka soke tashi da saukar jiragen sama.
Kafafen watsa labaran cikin gida sun ba da rahoton kai hari tashar jiragen ruwa da wasu gine-ginen gwamnati.
An ji tare da ganin fashewar bama-bamai da wuta nan da can a birnin na Port Sudan tun a cikin daren da ya gabata, wanda wannan shi ne kwana na uku a jere da birnin ke shan ruwan bama-bamai da ake kai harin ta hanyar kananan jiragen sama marassa matuka, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai na kasar ke bayyanawa.
Sai dai kuma wasu na cewa ba a san sanadin fashewar da tashin wutar ba da kuma ainahin wuraren da hakan ke faruwa a kai, yayin da yakin basasar kasar ya tunkari birnin wanda a da yake shiru daga balahirar yakin.
Rahotannin na cewa an ga hadarin bakin hayaki na tashi daga yankin babbar tashar jirgin ruwan birnin inda dubban mutanen da yakin ya raba da garuruwa da gidajensu suka fake.
Yakin na tsakanin mayakan kungiyar RSF da kuma rundunar sojin kasarta Sudan ya haddasa bala'i mafi muni na jama'a, wanda kuma ake ganin zai ma kara munana a sanadiyyar wadannan hare-hare na birnin na Port Sudan.
Birnin da majalisar dinkin duniya da hukumomi da kungiyoyin agaji har ma da ma'aikatun gwamnatin rundunar sojin kasar suka kafa hedikwatocinsu.
Wannan hari da aka fara kai wa birnin a ranar Lahadi na nuni da kara tsanantar yakin, kasancewar birnin na gabar tekun maliya bai gamu da hare-hare ta kasa ko ma ta sama ba, in banda a wannan makon.
A ranar Lahadi aka kai wani hari da jiragen sama marassa matuka kan wani sansanin soji da ke kusa da babban filin jirgin sama daya kacal da ke aiki a a kasar, bayan wannan harin kuma sai aka kai wasu inda aka hari manyan rumbuna da cibiyoyin adana mai na birnin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A dukkanin wadannan hare-hare sojojin kasar ta Sudan sun dora alhakin a kan kungiyar RSF.
An kuwa fara kai wadannan hare-hare birnin ne bayan da wata majiya ta tabbatar da cewa sojojin sun tarwatsa wani jirgin sama da kuma wani rumbun makamai a filin jirgin saman Nyala da ke karkashin ikon kungiyar RSF.
To amma kungiyar ta RSF ba ta dauki alhakin hare-haren na yanzu ba.
Makwabtan kasar ta Sudan – Masar da Saudiyya sun yi Alllwadarai da hare haren , ita ma majaliasar dinkin duniya ta nuna damuwa a kai.
Tun watan Afirilu na 2023 Sudan ta fada wannan mummuna yakin basasa tsakanin kungiyar ta RSF da kuma rundunar sojin kasar wadanda a da suke tare – rikici kann sabanin mayar da mulki tsarin farar hula ya raba kansu.
Rikicin ya raba mutum ,iliyan 12 da muhallinsu kuma ya jefa rabin yawan alummar kasar cikin matsananciyar yunwa, kamar yadda majalaisar dinkin duniya ta ce.
Bayan shekara biyu da yakin rundunar sojin ta yi nasara korara mayakan RSf daga galibi sassan tsakiyar kasar ta Sudan, kuma mayakan na RSF yanzu sun karkata ga kai hare-hare ta hanyar jirage marassa matukan, daga hare-hare ta kasa.
Inda suke harar tashoshin lantarki da sauran wuraren abubuwan jin dadin rayuwar jama'a a yankunan da ke hannun sojojin.
Gwamnatin soji ta Abdulfatah Alburhan ta zargi kungiyar RSF da kai hare haren baya kan birnin.
Birnin ne cibiyar gwamnatin sojan Sudan kuma babbar cibiyar taimakon jin kai.










