BBC ta samu bayanan sirri na azabar da jama'a ke ciki a yaƙin Sudan

Asalin hoton, Hafiza
- Marubuci, Heba Bitar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
- Aiko rahoto daga, Darfur, Sudan
- Lokacin karatu: Minti 10
"Ba ta samu damar barin wasiyya ba. Lokacin da aka ɗauke ta har ta riga ta mutu," in ji Hafiza, lokacin da take bayanin yadda aka kashe mahaifiyarta a birnin da ke ƙarƙashin mamaye a yankin Darfur, sa'ilin da yaƙin basasar ƙasar ya ɓarke, shekaru biyu da suka wuce.
Matashiyar mai shekara 21 a duniya ta naɗi yadda rayuwarta da ta iyalinta ta faɗa cikin garari sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsu, ta yi hakan ne ta hanyar amfani da ɗaya daga cikin wayoyin hannu da BBC ta tura a asirce, ga mutanen da yaƙi sanya su tsakiya a el-Fasher.
Ruwan wuta da ake wa birnin a kai a kai ya sanya an kaste birnin el-Fasher daga sauran yankunan duniya na tsawon shekara ɗaya, lamarin da ya sanya ƴan jarida suka gaza shiga birnin.
Bisa dalilai na tsaro, za mu yi amfani da sunaye ɗaɗɗaya ne kawai na mutanen da suka amince za su naɗi rayuwar tasu ta amfani da wayar salula domin nuna wa BBC abin da ya faru.
Hafiza ta bayyana yadda ba a cikin shiri ta zama wadda za ta kula da ƴan'uwanta mata biyu masu sama da shekara 10 da kuma ƙaninta mai shekara biyar a duniya.
Dama mahaifinsu ya mutu gabanin ɓarkewar yaƙin, wanda ya haifar da gaba tsakanin dakarun RSF da sojojin gwamnati, lamarin da ya jefa mutane cikin mawuyacin hali mafi muni a doron ƙasa.

Asalin hoton, Hafiza
Bangarorin biyu da suke yaki da juna a baya sun kashe tare - inda suka kwace mulki ta hanyar hambarar da gwamnatin da ke kan gado a lokacin - amma kuma sun farraka saboda wani shiri na kasashen duniya na mayar da kasar kan mulkin dumukuradiyya.
Babban birni na karshe da ya kasance a hannun rundunar sojin kasar a Arewacin Darfur a yamacin Sudan nan ne ya kasance garin su Hafiza - kuma mayakan RSF sun yi ta masa ruwan makamai tsawon wata 12 da ya gabata.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Agusta na 2024 wani makami da aka harba ya fada kasuwar da mahaifiyarta take zuwa domin sayar da kayayyakin amfani a gida.
"Abin jimami ne da damuwa, har yanzu ba na iya zuwa inda take kasuwancin," in ji Hafiza a daya daga cikin sakonnin bidiyo na farko da ta yi ta wayarta jim kadan bayan rasuwar mahaifiyarta.
''Na zauna ina ta rusa kuka ni kadai a gida."
An zarge dukkanin bangarorin biyu da aikata laifukan yaki ta hanyar kai hari da gangan a kan farar hula - zargin da suka musanta.
Mayakan na RSF sun kuma musanta zargin da Amurka da sauran kungiyoyin kare hakkin dan'Adam suka yi cewa mayakan sun rika kai hari kan wadanda ba Larabawa ba a sauran sassan Darfur bayan da suka kwace iko da yankunan.
RSF ce ke da ikon shiga da fita daga birnin inda a wasu lokutan take barin fararen hula fita daga yankin, ta hakan ne Hafiza ta samu damar tura 'yanuwanta zuwa inda ba a yakin. To amma kuma ta ci gaba da zama a birnin domin samun kudin da za ta kula da 'yanuwan nata.
A sakon da ta aika, ta bayyana yadda a lokacin ta rika aikin raba barguna da ruwa ga mutanen da yakin ya raba da muhallinsu a sansanoni da aikin dafawa da raba abinci da kuma taimaka wa a aikin wayar da kai na wata kungiya mai yaki da cutar kansar nono, inda ake biyan 'yan kudi kalilan da take rayuwa da su.
Tana shafe dare ita kadai.
"Ina tuna wuraren da mahaifiyata da 'yanuwana suke zama, abin yana tayar mini da hankali,'' ta ce.

Asalin hoton, Mostafa
Kusan a dukkanin hotunan bidiyo da Mostafa mai shekara 32 ya aiko mana ana iya jin karan ruwan makamai da harbe-harbe a ciki.
Ya ce : "Dare da rana muna fama da ruwan makamai da RSF ke yi."
Wata rana bayan ya dawo daga ziyarar gidan iyayensa, sai ya tarar bam ya fada gidansa da ke kusan da tsakiyar birnin - rufi da bangon gidan duk sun lalace - kuma an yashe dan abin da ya rage na gidan.
"Komai ya salwanta. An wawashe yawancin gidajen da ke unguwarmu," yana mai dora laifin a kan RSF.
A lokacin da Mostafa yake aikin sa-kai a wani sansani na 'yan gudun hijira, sai kawai aka rika yi wa wajen ruwan makamai. To amma ya kunna kyamarar daukar hoto ta wayarsa inda yake ta daukar hoton duk makamin da ya fado wajen.
"Ba wani waje da za ka ce ka tsira a el-Fasher," ya ce. "hatta sansanin 'yan gudun hijira bai tsira daga ruwan makamai ba.
"Kowa zai iya mutuwa a kowane lokaci - ta hanyar harsashi ko makaman da ake harbowa ta sama ko yunwa ko kuma kishirwa.'' In ji shi.

A wani sakon ya yi magana kan rashin tsaftacaccen ruwa, inda ya bayyana yadda mutane ke shan gurbataccen ruwath sewage.
Mostafa da Manahel, mai shekara 26, wadda ita ma BBC ta ba ta waya, suna aikin sa-kai ne a wani wajen dafa abinci na agaji, wanda ake yi da taimakon kudaden da 'yan Sudan da ke kasashen waje suke aikawa taimako.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yunwa za ta iya barkewa a birnin -lamarin da tuni ma ya riga ya faru a sansanin Zamzam da ke kusa - sansanin da mutum sama da dubu 500 ke tsugune a ciki.
Manahel, ta ce mutane da yawa ba sa iya zuwa kasuwa su sayi kaya, idan ma sun je kayan sun yi tsada sosai.
Ta kara da cewa, ''A yanzu duk iyalai sun zama daidai da juna ba talaka ba mai kudi - mutane ba sa iya sayen muhimman kayan masarufi kamar abinci."

Asalin hoton, Manahel
Bayan dafa abincin - shinkafa da miya, sai su rarraba wa 'yan gudun hijira da ke sansanin - ga yawancin mutane abincin da za su iya samu kenan su ci duk tsawon rana.
Lokacin da aka fara yakin Manahel ta kammala karatunta na jami'a kenan, inda ta karanta fannin Shari'ar Musulunci da kuma aikin lauya.
Lokacin da fadan ya isa el-Fasher, sai ita da mahaifiyarta da kuma 'yanuwanta shida suka tsere zuwa wani yankin nesa da inda ake fafata yakin.
Ta ce: "Ka rasa muhallinka da kuma komai da ka mallaka - ka tsinci kanka a wani sabon waje da ba ka da komai."
Duk da wannan hali da aka tsinci kai a ciki, mahaifinta ya ki yarda ya bar gidan nasu, har ma wasu makwabta suka bar abubuwansu karkashin kulawarsa - kuma ya ci gaba da zama domin kare su - matakin da ya kai ga rasuwarsa.
Manahel ta ce, mahaifin nata ya rasu ne a sanadiyyar wani makami da RSF suka harba a watan Satumba na 2024.

Asalin hoton, Manahel
Tun bayan da aka fara yakin, shekara daya da ta wuce kusan an kashe ko jikkata kusan mutum 2,000 a el-Fasher, a kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.
Ba kasafai mutane ke barin gidajensu, su fita ba idan rana ta fadi.
Rashin wutar lantarki na jefa tsoro a zukatan yawancin al'ummar birnin na el-Fasher su miliyan daya.
After sunset, people rarely leave their homes. The lack of electricity can make night-time frightening for many of el-Fasher's one million residents.
Manahel, ta ce, mutanen da suke da wutar lantark ta hasken rana ko batir suna tsoron kunna fitilunsu domin za a iya kai musu hari da kananan jiragen sama marassa matuka.
Akwai lokacin da ba ma iya samun ita Manahel ko sauran tsawon kwanaki saboda ba su da hanyoyin intanet.
To amma babban abin fargaba da tashin hankali ga Manahel da Hafiza shi ne, fadawar birnin hannun RSF.
''A matsayina na yarinya za a iya yi min fyade,'' in ji Hafiza a cikin wani sako da ta aiko.
Ita da Manahel da Mostafa, dukkaninsu, ba Larabawa ba ne, saboda haka suna jin tsoron kada abin ya da ya faru a wasu biranen da RSF suka kama, musamman el-Geneina, su faru a kansu.

A 2023 kasar ta ga kisan-kiyashi na tsabagen rashin imani da tayar da hankali na kabilanci, wanda Amurka da sauran kasashe da hukumomi suka ce tabbataccen laifi ne na kisan-kiyashi.
Ana zargin mayakan RSF da gamayyar kungiyoyin 'yanbindiga na Laraba da kai hari kan al'ummomin da ba Larabawa ba kamar su Massalit - zargin da RSF ta musanta.
Wata mata 'yar kablar Massalit da na hadu da ita a wani sansanin 'yan gudun hijira a kan iyakar Chadi ta bayyana yadda gungun mayakan RSF suka yi mana fyade, har ba ya iya tafiya ba kusan mako biyu.
Haka ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta ce an rika yi wa mata 'yan shekara 14 fyade a lokacin.
Shi ma wani mutum ya gaya min yadda ya ga kisan-kiyashi da mayakan RSF suka aikata - inda ya tsira bayan da aka dauka ya mutu bayan an raunata shi.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa an kashe tsakanin mutum 10,000 da 15,000 a el-Geneina kawai a 2023.
Kuma yanzu sama da kashi daya bisa hudu na al'ummar birnin miliyan daya suna zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Chadi.
'Yanjarida kadan ne suke samun shiga birnin, to amma bayan kai ruwa rana a karshe hukumomin birnin sun bar tawagar BBC ta ziyarci birnin a watan Disamba na 2024.

An hada mu da wasu jami'ai daga ofshin gwamnan birnin, wadanda sai abin da suka yarda za mu gani.
Wannan ya kara tabbatar mana da cewa RSF ke da iko da birnin, inda na ga mayakansu a motoci da manayan makamai suna sintiri a tituna.
Mun samu jin ta bakin wani daga cikin kwamandojinsu wanda ya ce su a wurinsu babu farar hula a birnin irin su Hafiza, da Mostafa da kuma Manahel da ke zaune a el-Fasher.
Ya ce: "Duk mutumin da ya zauna a wajen da ake yaki yana shiga yakin ne shi ma, babu farar hula, dukkansu 'yan bangaren sojoji ne."
Kwamandan ya ce yanzu el-Geneina na cikin zaman lafiya, kuma wai mazauna birnin kusan kashi 90 cikin dari sun dawo gidajensu.
To amma a saninmu dubban mazauna birnin 'yan gudun hijira da ke zaune a sansani a Chadi. Kuma na ga gidaje da dama da ba kowa a cikinsu lokacin da muke kewayawa birnin.

Yadda wadannan jami'ai da hukumomin birnin suka hada mu da su ke binmu ku da kut abu ne mawuyaci ka samu ainahin labarin yadda rayuwa take a birnin.
Mun kammala ziyararmu da tattaunawar da muka yi da gwamnan Darfur ta Yamma, Tijani Karshoum, wanda aka kashe gwamnan da ya gabace shi a watan Mayu na 2023 bayan da ya zargi mayakan RSF da laifin kisan-kiyashi.
Wannan ita ce hira da shi ta farko tun 2023, kuma ya ce shi farar hula ne da ba shi da bangare a lokacin rikicin el-Geneina.

Gwamnan ya ce a yanzu sun manta da abin da ya faru - suna zaman lafiya da lumana da junansu, kuma alkaluman yawan mutanen da aka kashe da jikkatawa a rikicin wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, an zuzuta su.
A dakin da muke wannan tattaunawa mun lura cewa akwai wani wakilin RSF a zaune yana sauraron duk hirar tamu.
Amsar da gwamnan yake ba ni a kan dukkanin tambayoyi kan zargin kisan-kiyashi da sauran munanan abubuwan da aka yi a rikicin birnin da kuma abin da ya faru da tsohon gwamnan, Khamis Abakar, kusan iri daya ce.
KUsan mako biyu bayan na tattauna da Karshoum, Kungiyar tarayyar Turai ta sanya takunkumi a kansa, da cewa yana da alhaki a kan harin da aka kai aka kashe tsohon gwamnan, kuma ta ce yana da hannu a ciki, har ma da sauran laifuka da aka aikata a birnin.
Na nemi jin ta bakinsa kan wannan zargi na Tarayyar Turai, to amma ya ce tun da ana zarginsa a wannan lamari to duk wani bayani da zai yi ba za a dauke shi da sahihanci ba.
Amma kuma duk da haka ya ce shi ba wani bangare da ya mara wa baya a duk tsawon rikicin hasali ma shi yana zaune a gidan a duk tsawon lokacin.

Asalin hoton, Mostafa
Idan aka yi la'akari da bambancin da ake da a tsakanin bayanan da hukumomin da ke da iko da el-Geneina ke bayarwa da kuma tarin bayanan da jama'a ke yi a kan rikicin, abu ne mawuyaci a yi tunanin cewa mutane za su taba komawa gidajensu.
Haka lamarin yake ma game da 'yan kasar ta Sudan miliyan 12, wadanda ko dai sun tsere daga gidajensu suna gudun hijira a waje ko kuma suna zaune a sansanin gudun hijira daban-daban a cikin kasar ta Sudan.
A karshe dai, Hafiza, da Mostafa da Manahel sun kasa jure wa rayuwa a el-Fasher, inda a watan Nuwamba na 2024, dukkansu suka bar birnin suka koma wasu garuruwa na kusa da birnin.
Yadda rundunar sojin Sudan ta sake kame iko da babban birnin kasar Khartoum a watan Maris, yanzu Darfur ta ci gaba da kasancewa wani yanki na karshe inda kungiyar RSF har yanzu take da iko, wannan kuma ya sa el-Fasher ta zama wani babban fagen-daga, inda Manahel ta ce sun fice daga birnin ba su san makomarsu ba - ba su san ko za su taba komawa birnin ba.












