Me ayyana gwamnatin ƴan adawa da RSF ta yi a Sudan ke nufi?

Asalin hoton, Hemedti's Telegram account
Ayyana gwamnatin tawaye da dakarun RSF suka yi a Sudan, ya zo a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke cika shekara biyu, abin da ya ƙara saka shakku kan ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya.
Ayyana gwamnatin na haɗin-kai da zaman lafiya da jagoran RSF Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya nuna yadda ƙasar ta rabu kashi biyu.
Sojojin Sudan da ƙungiyoyin haɗaka ne ke iko da gabashi da arewaci da kuma yawancin tsakiyar ƙasar, yayin da RSF da dakarun ƙawance ke iko da kusan ɗaukacin yammacin yankin Darfur da kuma yanki mai girma a kudancin Sudan.
Ana sa ran RSF da sojojin ƙawance za su ayyana yadda za a tafiyar da gwamnatin a cikin makonni masu zuwa. Birnin Nyala na yankin Darfur zai kasance wurin da za su zauna.
Wane tasiri ayyana gwamnatin zai yi?
Ayyana gwamnatin ya ƙara janyo rarrabuwar kawuna a Sudan da kuma saka fargabar cewa ƙasar za ta faɗa cikin mawuyacin hali musamman irin abin da ya faru a Libya.
Yawancin ƙungiyoyi da ke riƙe da makamai da kuma na siyasa sun rattaɓa hannu a watan Fabrairun 2025 da RSF kan kafa gwamnatin ƴan tawaye da za ta fito daga yankunan Darfur da Kordofan.
Wannan ya janyo fargabar cewa waɗannan yankuna za su iya buƙatar ɓallewa daga Sudan.
RSF da ƙawancen ƙungiyoyi sun bayyana shirin fito da "sabuwar takardar kuɗi da kuma takardun zama ɗan ƙasa", wanda masana suka ce yunkurin ɓallewa ne.
Sai dai, Hemedti ya yi watsi da zargin neman ɓallewa daga Sudan. A maimakon haka, ya zargi gwamnatin sojin ƙasar da yin wasu abubuwa da za su kai ga rabewa... da kuma dawo da irin kuskuren da ya janyo rabewar Sudan ta Kudu.
Ta yaya aka tsara tafiyar da gwamnatin?

Asalin hoton, Tasses alliance Facebook page
Ana sa ran gwamnatin ƴan tawayen zai yi amfani da tsarin tarayya na rarraba iko, a cewar "tsarin mulki" da aka rattaɓa wa hannu a Nairobi, babban birnin Kenya a watan Maris. Tsarin ya ƙasa Sudan zuwa yankuna takwas da kuma samar da ɓangarori uku: tarayya, yanki da kuma matakin karamar hukuma.
Ana sa ran mambobin ƙawance na Tasses su za su mamaye gwamnatin ƴan tawayen. Gwamnatin zai kunshi mutum 15 na kwamitin shugaban ƙasa, mambobi 16 na majalisar ministoci da kuma mutum 201 na ƴan majalisa.
Kwamitin shugaban ƙasa shi zai naɗa Firaiminista, mambobin shari'a, attoni-janar, akanta-janar da sauransu.
Firaiministan zai naɗa mambobin majalisar ministoci ta hanyar tattaunawa da ƙungiyoyin ƙawance.
Mata za su samu mukamai da ya kai kashi 40 a majalisar dokoki.
Gwamnatin ƴan adawar za ta samar da sojoji da kuma ƴan sanda iri ɗaya, yayin da RSF da ƙungiyoyin ƙawance na ƴan bindiga za su kasance jigon dakarun.
Wane martani lamarin ya janyo?
Mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric ya yi gargaɗin cewa matakin zai "ƙara janyo rashin tabbas a ƙasar", yayin da Tarayyar Afirka ta yi watsi da gwamnatin ƴan tawayen da nanata goyon bayanta ga haɗin-kan Sudan.
Mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya Walid bin Abdul Karim Al-Khuraiji ya kwatanta matakin Hemedti da "yunkurin kafa haramtacciyar gwamnati".
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ya ce "kafa gwamnatin ƴan adawa ba ita ce mafita ba", yayin da ma'aikatar harkokin wajen Australiya ta ce ta yi "watsi da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ƴan adawa" a Sudan.
Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Tarayyar Turai da kuma Amurka sun nuna adawa a baya da batun kafa gwamnatin ƴan tawaye da kuma nuna goyon baya ga haɗin-kan Sudan.
Waɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan RSF?
Ƙasashe da ake ganin za su tattauna da gwamnatin ƴan adawar sun kunshi babban mai taimakawa RSF daga waje, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma waɗanda ake ganin suna goyon bayan RSF ɗin a siyasance kamar Kenya da Chadi da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Habasha da kuma Uganda. Akwai kuma wani ɓangare na Sojojin Libya da suka ɓalle.
A lokacin da yake ayyana kafa gwamnatin adawar ranar 15 ga watan Afrilu, Hemedti ya gode wa Ethiopia da Chadi da Uganda da kuma Kenya saboda karɓar ƴan gudun hijirar Sudan da suka shiga ƙasar.
A watan Fabrairu, Al-Hadi Idris Yahya, babban jigon ƙungiyar Tasses ya yi iƙirarin cewa "suna da yakinin za su samu goyon baya daga ƙasashe da dama" kan kafa gwamnatin.
Hemedti ya yi kira ga Tarayyar Afirka da ta "amince da zaɓin al'ummar Sudan", wani mataki na amincewa da gwamnatin da suka kafa.
Ta yaya hakan zai shafi ƙoƙarin samar da zaman lafiya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kafa gwamnatin ƴan adawa zai ƙara dagula ko janyo cikas a ƙoƙarin da ake yi na kawo karshen rikicin yayin da RSF ke son tattaunawa da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta Sudan a matsayin masu iko iri ɗaya, maimakon ƙungiyar ƴan tawaye.
Gwamnatin sojin ta Sudan da wuya ta amince da hakan. Tana ɗaukar RSF a matsayin "ƴan ta'adda da kuma masu "kisan kare dangi".
Wasu ƙungiyoyi karkashin Tasses na hankoron neman ɓallewa, kamar ƙungiyar ƴan tawayen Sudan ta People's Liberation Movement/Army-North (SPLM/A-N al-Hilu), wadda ke faɗa don samun iko da kansu a kudancin Kordofan da kuma jihohin Blue Nile.
Yunkurin RSF na son shugabanci da kuma samun damar shiga kasuwar makamai ta ƙasa da ƙasa, zai ƙara tsawaita faɗan da ake yi da kuma janyo cikas a koƙarin samar da zaman lafiya.
Kafa gwamnatin ƴan adawa zai kuma ƙara bai wa wasu ƙasashe damar yin abin da suke so irinsu Haɗaɗɗiyar Daular Laraba da Chadi da Sudan ta Kudu da Kenya da kuma Habasha, waɗanda ake zargi da marawa RSF baya.
Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta karɓe dukkan iko a wata bata-kashi da zubar da jini a juyin mulki da aka yi a watan Oktoban 2021, abin da ya janyo Tarayyar Afirka ta dakatar da Sudan a matsayin mamban ƙungiyar.
Sai dai, ta yi iƙirarin cewa tana yin komai a kan doka kuma tana wakiltar Sudan a matakin ƙasa daƙasa.






