Dakarun RSF sun kai hari birin Port Sudan a karon farko

Port Sudan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban fararen hula ne suka tsere zuwa Port Sudan tun farkon fara yaƙin basasa.
Lokacin karatu: Minti 3

Sojojin Sudan sun ce dakarun RSF sun kai wa filin jiragen sama na sojoji a birnin Port Sudan hari da jirgi marasa matuƙi ranar Lahadi.

Wannan shi ne karon farko da hare-haren RSF suka kai babban birnin gwamnatin mulkin soji ta Sudan tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna shekaru biyu da suka gabata.

Kakakin sojojin Sudan Nabil Abdullah, ya ce dakarun RSF sun kai hare-hare da jirage marasa matuƙa a gabashin birnin Port Sudan a Bahar Maliya da sansanin sojojin sama na Osman Digna da kuma "ma'ajiyar kayayyaki da wasu yankunan farar hula".

Ya ce ba a samu rahoton waɗanda suka jikkata ba, amma harin ya ''lalata wasu kayayyaki''.

Dakarun RSF ba su ce uffan ba.

Sudan ta tsunduma tashin hankali a watan Afrilun 2023 lokacin da rikicin mulki ya ɓalle tsakanin sojoji da dakarun RSF gabanin shirin miƙa mulki ga fararen hula.

An yi ƙiyasin cewa aƙalla mutum 150,000 ne suka mutu a yaƙin basasar, yayin da aka tilastawa wasu miliyan 12 tserewa daga muhallansu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana halin da ake ciki a Sudan a matsayin mummunan rikicin da ya yi ƙamari a duniya, inda sama da mutane miliyan 30 ke buƙatar agaji yayin da miliyoyin ke fama da matsanancin ƙarancin abinci.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gabanin harin na ranar Lahadi, birnin Port Sudan ya ɗauki matakan kariya har ana yi masa kallon yankin da ya fi kowanne tsaro a yaƙin da ya addabi ƙasar.

Bayan sojojin Sudan sun rasa ikon Khartoum babban birnin ƙasar a farkon yaƙin, Port Sudan ne ya zama hedikwatar gwamnatin soji ƙarƙashin Janar Abdel Fattah-al Burhan.

Hukumomin MDD sun mayar da ofisoshi da ma'aikatansu birnin da ke gaɓar teku, inda dubban fararen hula suka mayar da wurin a matsayin zaman mafaka lokacin yaƙin.

"Muna kan hanyar zuwa shiga jirgin sama, aka kwashe mu cikin gaggawa," kamar yadda wani matafiyi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta, waɗanda BBC ba ta tantance ba, sun nuna wata fashewa da kuma yadda baƙin hayaƙi ya ke tashi sama.

Wani jami'in gwamnati ya shaida wa AFP cewa an rufe filin jirgin saman kuma an dakatar da jigilar fasinjoji.

Rikicin na shekaru biyu ya haifar da rabuwar kai a ƙasar.

Dakarun RSF waɗanda Janar Mohamed Dagalo wanda aka fi sani da Hemedti ke jagoranta, na iko da yankuna da dama na yankin Darfur a Yammacin Sudan da kuma wasu yankuna a Kudanci.

Gwamnatin da sojoji ke goyon baya na iko da Arewacin Sudan da yankunan da suka haɗa da muhimman wurare a birnin Port Sudan da ke Bahar Maliya

Harin na ranar Lahadi shi ne hari na baya-baya cikin hare-haren da dakarun RSF suke kai wa da jirage marasa matuƙa kan sojoji da gine-ginen fararen hula a yankin da ke ƙarƙashin ikon sojoji.

Ranar Asabar sojoji sun bayar da rahoton cewa an kai hari Kassala da ke gabashin iyakar Sudan da jirgi marasa matuƙi, kusan mil 250 daga sansanin dakarun RSF.

Sojojin Sudan sun karɓe wasu yankuna a watannin baya-bayan nan, sun kuma yi nasarar karɓe iko da fadar shugaban ƙasa a Khartoum cikin watan Maris.

Ana kallon ƙwato babban birnin a matsayin nasara a yaƙin basasar da aka kwashe shekaru biyu ana gwabzawa, amma yayin da sojojin Sudan ke kan gaba a yanzu, zai yi wahala ɓangarorin biyu su samu nasarar da za ta bayar da damar shugabancin Sudan gaba-ɗaya kamar yadda wani rahoton ƙungiyar Kungiyar International Crisis Group (ICG) mai fafutukar hana tashe-tashen hankula a duniya.

Wannan ne yaƙin basasa na uku a Sudan a cikin shekaru 70, amma ana ayyana shi a matsayin wanda ya fi sauran tsanani sakamakon yadda ya lalata ƙasar.

Bayan juyin mulki a shekara ta 2021, majalisar manyan sojoji ta ƙarbi ragamar jagoranci a Sudan ƙarƙashin mutane biyu a tsakiyar rikicin da ke gudana a yanzu.

Al-Burhan shi ne shugaban sojojin Sudan kuma a matsayin shugaban ƙasar, yayin da Hemedti ya kasance mataimakinsa kuma shugaban RSF.

Sun samu rashin fahimta kan yadda harkokin ƙasar ke tafiya da shirin miƙa mulki ga farar hula da kuma musamman wani shiri na mayar da jajirtattun dakarun RSF cikin sojoji.

An fara yi wa juna kallon hadarin kaji ne lokacin da ake dab da ƙirƙirar gwamnatin farar hula kafin rikici tsakanin ɓangarorin biyu kan ikon Sudan ya ɓarke.

Duk yunƙurin da ƙasashen ƙetare suka yi don samar da zaman lafiya bai yi nasara ba, duk ɓangarorin biyu na samun goyon baya daga wasu ƙasashen ƙetare waɗanda ke shigar da makamai cikin ƙasar.