Gaza: Wace illa yunwa ke yi wa jikin ɗan'adam?

Hanayen Falasɗinawa riƙe da tukane suna jira a raba musu abinci

Asalin hoton, Anadolu/Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasashen duniya na ƙara nuna damuwa game da halin rashin jin ƙai da ake ciki a Gaza.
    • Marubuci, Rebecca Thorn and Angela Henshall
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC WS Health
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shirin bayar da agajin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi cewa kusan kashi ɗaya cikin uku na mutanen da ke zaune a Zirin Gaza na fama da yunwa inda suke shafe kwanaki ba tare da cin abinci ba.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce akwai "yunwar gaske" a Gaza, duk da cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya musanta hakan.

A cikin 'yan kwanakin nan, Isra'ila – wadda ke musanta cewa akwai yunwa a Gaza – ta sanar da "dakatar da kai hare-kare a Gaza ta ɗan lokaci" domin bayar da damar shigar da kayan agaji zuwa yankin.

Amma babban jami'in kula da jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya ce ana buƙatar "dimbin abinci" domin daƙile yunwa mai tsanani.

Hukumar UNRWA, wacce ke kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa a Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce kashi ɗaya cikin biyar na yara a birnin Gaza na fama da ƙarancin abincin mai gina jiki, kuma adadin na ƙaruwa kullum.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ruwaito cewa asibitoci na karɓar mutane cikin mawuyacin hali mai tsanani sakamakon rashin abinci, wasu ma suna faɗuwa a tituna saboda tsananin yunwa.

Duk da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta bayyana cewa akwai tsananin yunwa a Gaza ba tukuna, hukumar IPC ta yi gargaɗi cewa yankin na fuskantar barazanar matsanaciyar yunwa sosai.

Mece ce matsanaciyar yunwa kuma yaushe ake ayyana ta a matsayin dokar ta ɓaci?

Hukumar tabbatar da samar da abinci ta duniya – wata ƙa'ida ce da ake amfani da ita wajen bayyana wahalar da jama'a ke fuskanta wajen samun abinci mai arha da gina jiki.

Mataki mafi tsanani a tsarin shine mataki na 5 wanda shine yunwa – yana nufin wani yanayi da ke cika waɗannan sharudda:

  • Kashi 20 cikin 100 na gidaje na fuskantar matsananciyar rashin abinci,
  • Kashi 30 cikin 100 na yara na fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki,
  • Aƙalla manya biyu ko yara huɗu daga cikin mutane 10,000 na mutuwa a kullum sakamakon yunwa.

A rahoton da IPC ta fitar a kan Gaza a ranar 12 ga Mayu, an bayyana cewa gaba ɗayan al'ummar yankin na rayuwa a cikin halin na tsananin yunwa – daga Mataki na 3 zuwa sama.

Rahoton ya yi hasashen cewa daga watan Mayu zuwa Satumba na 2025, kusan mutum 469,500 za su fuskanci matsanancin rashin abinci wato mataki na 5 kenan wanda shine yunwa.

Idan waɗannan yanayi sun cika, Majalisar Ɗinkin Duniya kan ayyana dokar ta ɓaci kan yunwa. Wannan na iya zuwa tare da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasar da abin ya shafa, da kuma wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ko na jinƙai.

Falasɗinawa na ɗaukar buhunan fulawa daga motoci masu ɗauke da agaji da suka shigo ta mashigar Zikim a arewacin Gaza.

Asalin hoton, Majdi Fathi/NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, Falasɗinawa na ɗaukar buhunan fulawa daga motoci masu ɗauke da agaji da suka shigo ta mashigar Zikim a arewacin Gaza.

Me ke faruwa da jikin ɗan'adam a lokacin tsananin yunwa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsananin yunwa na faruwa ne idan mutum ya daɗe ba ya samun abinci, wanda ke nufin jiki ba ya samun isasshen kuzari da zai ba shi damar gudanar da ayyukansa na yau da kullum.

A ɗabi'ance, jiki na narkar da abinci ya koma sinadarin 'glucose' domin samun kuzari. Amma idan babu abinci, jiki zai fara amfani da sinadarin 'glycogen' da ke ajiye a hanta da tsokoki, domin sakin 'glucose' zuwa jini.

Idan waɗannan abubuwan da ke ajiye a hanta da tsokar jiki sun ƙare, jiki zai koma amfani da mai da ke ajiye a jikinsa. Idan wannan ma ya ƙare, sai ya fara cinye tsokoki domin samar da kuzari.

Yunwa na iya sa wasu sassa na jiki kamar huhu da ciki da sassan ɓangaren haihuwa su ragu. Haka kuma, tana iya shafar ƙwaƙwalwa, inda mutum zai iya fama da ruɗani da damuwa da kuma fargaba.

Duk da cewa wasu mutane na mutuwa kai tsaye saboda yunwa, yawancin masu fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki kan mutu ne sakamakon cututtuka da suka haɗa da na huhu ko hanji saboda rauni a garkuwar jiki.

Yunwa kuma tana shafar mutane ta hanyoyi daban-daban.

"Ba wai yaro zai shiga cikin yanayi na rashin abinci ma gina jiki nan take ba. Wataƙila ya taɓa fama da cututtuka kamar cutar cizon sauro da tarin fuka ko gudawa a baya," in ji Farfesa Charlotte Wright, babban mai bincike a fannin abinci na dan'adam a Jami'ar Glasgow da ke Birtaniya.

"Yara da suka kasance cikin ƙoshin lafiya kafin yunwa, za su iya samun ƙarfin ci da narkar da abinci idan aka samu. Amma wasu kuwa ba haka ba ne."

Yunwa a Gaza

Ta ya ya ƙarancin abinci mai gina jiki ke shafar jarirai da yara?

Rashin abinci mai kyau tun daga ƙuruciya na iya haifar da matsaloli da za su daɗe har mutum ya girma. Wannan na iya jawo cikas ga ci gaba da lafiyar kwakwalwa da kuma hana yara girma yadda ya kamata.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta alaƙanta rashin girma yadda ya kamata da yara ke fuskanta da rashin cin abinci mai gina jiki da yawan kamuwa da cututtuka, da kuma rashin kulawa lafiyar ƙwaƙalwa. Yawanci yaran da hakan ya shafa sukan kasance ba sa girma fiye da yadda ya dace da shekarunsu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce iyaye mata da suka sha fama da tsananin rashin abinci na iya haifar yara da za su fuskanci wannan matsalar.

UNICEF ta bayyana cewa rashin cin abinci mai kyau a lokacin da mace ke da ciki na iya haifar da cutar 'anaemia' (rashin jini) da 'pre-eclampsia' wato zubar jini sosai bayan haihuwa, da mutuwar uwa ko jariri.

Hakanan yana iya haifar da mace-macen jarirai kafin haihuwa da rage nauyin jarirai ƙasa da yadda ya kamata.

Mata da ke fama da rashin abinci mai gina jiki na iya samun matsala wajen samar da isasshen ruwan nono mai gina jiki ga jariransu.

Dr. Nuradeen Alibaba daga Médecins Sans Frontières, ƙwararre a kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki, ya ce wannan matsala tana iya riƙe mutum har tsawon rayuwarsa.

Ya ƙara da cewa wasu mutane da suka taso da rashin abinci mai gina jiki na iya samun 'osteoporosis' – cutar raunin ƙashi.

Falasɗinawa ciki har da yara na amfani da gwangwani da kwanowajen ɗibar abinci mai zafi daga babban tukunya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana raba abinci mai zafi ga Falasɗinawa a Gaza.

Ta ya ya za a maganace matsalar rashin abinci mai gina jiki?

Farfesa Wright ya ce, "Domin magance wannan matsalar ta rashin abinci mai gina jiki, akwai hanyoyi guda biyu da ake buƙata wanda suka haɗa da ƙara shigar da abinci zuwa Gaza, da kuma kawo abinci masu gina jiki kuma masu tsada."

"Ana buƙatar a bai wa yara abinci mai kyau cikin gaggawa da kuma iyayensu mata."

"Shayar da jarirai da nonon uwa ita ce hanya mafi lafiya da tsafta, amma dole ne a ciyar da uwa da abinci mai kyau domin ita ma ta iya shayar da jaririnta amma kuma wannan hi ne babban ƙalubale." in ji Farfesan.

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne a fi bai wa yara da iyayensu mata fifiko."

Smitha Mundasad, mai rahoto kan lafiya daga BBC Arabic wadda ita ma likita ce, ta ce rashin cin binci mai gina jiki yana da mummunan illa – musamman ga yara – kuma maganin ba koyaushe ake samun su ba.

A lokuta masu tsanani, idan mutum ba zai iya hadiyar abinci ba, sai a kai shi asibiti ko cibiyar lafiya don samun abincin da aka tanada musamman da kuma magani don cututtuka ko matsalolin da ka iya tasowa.

Saboda haka, ba kawai a samu abinci ake buƙata ba – ana buƙatar samar da abincin da ya dace da kuma ingantaccen tsarin kiwon lafiya don tallafa wa waɗanda ke buƙatar kulawa.