Waɗanne ƙasashe ne suka amince da kafa ƙasar Falasɗinawa?

Asalin hoton, Getty Images
A watan Satumba ne Faransa za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa a hukumance, kamar yadda Shugaba Emmanuel Macron ya sanar, hakan kuma ya sa Faransa ta zama ƙasar G7 ta farko da ta yi hakan.
A wani sako a shafin X, Macron ya bayyana cewa a wani zama da za a yi a zauren Majalisar da ke New York ne za a ayyana hakan a hukumance .
"Bukatar gaggawa a yau ita ce a kawo karshen yakin Gaza a kuma samu kubutar da farar hular da ke zirin. Zaman lafiya abu ne mai yiwuwa. Muna bukatar a gaggauta tsagaita wuta, a saki mutanen da ke tsare a kuma kai wa mutanen Gaza gagarumin agajin jin kai," kamar yadda ya rubuta.
Jami'an Falasɗinawa sun yi maraba da matakin Macron yayin da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce matakin kamar nuna goyon baya ne ga masu ta'addanci sakamakon hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da Hamas ta kai kan Isra'ila.
Amurka, da kakkausar murya ita ma ta yi fatali da sanarwar Macron, in ji Sakatare harkokin wajenta Marco Rubio, yana bayyana matakin a matsayin "ganganci".
G7 kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki wadda ta kunshi Faransa da Amurka da Birtaniya da Italiya da Jamus da Canada da kuma Japan.
Isra'ila ba ta amince da samar da kasar Falasdinawa ba a Gabar yamma da Kogin Jordan da Gaza, saboda a tunaninta, kasar za ta zama barazana ga kasantuwar Isra'ila.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya rubuta wani sakon X cewa: "Samar da kasar Falasdinawa a irin wannan yanayi zai samar da wata kafar ruguza Isra'ila - ta kasance cikin tashin hankali. Mu gane wani abu: Falasdinawa ba kasa suke so ba kusa da Isra'ila, suna neman kasa ne a maimakon Isra'ila."
Suwa ne suka amince a samar da kasar Falasɗinu?

Asalin hoton, Reuters
A yanzu, fiye da kasashe 140 cikin mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 ne suka amince a samar da kasar Falasdinawa. ciki har da mambobin kungiyar kasashe Larabawa da ke Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kuma kungiyar yan ba-ruwanmu wadanda ba su nuna matsayarsu ba.
Wasu kasashen Turai na daga cikinsu har da Sifaniya da Ireland da Norway wadda ta amince da Falasdinu a matsayin kasa a Mayun 2024. Gabanin haka, kasashen Turai kalilan ne suka yi haka - galibinsu a 1988.
Sai dai babbar mai mara wa Isra'ila baya, Amurka da kawayenta har da Birtaniya da Australiya ba su amince da yankin Falasɗinawa a matsayin kasa ba. Australiya ta nuna cewa watakila za ta yi haka ne domin ita ma ta shiga sahun masu goyon bayan maslahar kasa biyu.

Asalin hoton, Reuters
Me ya sa wasu kasashen suka ki aminta da kafa ƙasar Falasɗinawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kasashen da suka ki amincewa da ƙasar Falasdinawa galibi ba sun yi haka ba ne saboda rashin samun yarjejejiya game da matsugunni wanda Isra'ila ta amince da shi ba.
"Duk da cewa a baki tana nuna bukatar a kafa kasar Falasdinawa, Amurka ta dage kan batun tattaunawar gaba da gaba tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, abin da ke nufin bai wa isra'ila damar hawa kujerar na ƙi kan bukatun Falasdinawa," in ji Fawaz Gerges, farfesa a bangaren diflomasiyya tsakanin kasashe da siyasar Gabas ta Tsakiya a jami'ar London School of Economics.
An soma tattaunawar zaman lafiya a shekarun 1990 daga bisani burin samar da kasa biyu, inda Falasdinawa da Isra'ila za su iya zama gefe da gefe da juna a kasashe daban-daban.
Sai dai tattaunawar zaman lafiyar ta fuskanci cikas daga farkon shekarun 2000 tun kafin ma 2014, lokacin da tattaunawar ta rushe tsakanin Isra'ila da Faslasdinawa a Washington.
Ba a warware batutuwan da ake taƙaddama a kai ba, har da batun iyakoki da kuma yadda kasar Falasdinawa za ta kasance, birnin Kudus da kuma makomar yan gudun hijirar Falasdinawa daga yakin da aka gwabza tsakanin 1948 zuwa 1949 da ya biyo bayan ayyana samar da ƙasar Isra'ila.
Isra'ila ta nuna adawa da buƙatar yankin Falasɗinawa ya zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
AFP ta ruwaito jakadan Isra'ila Gilad Erdan a Afrilun 2024 yana cewa kasancewar ana tattaunawar ma nasara ce ga kisan kiyashin da ake yi, yana mai cewa bai wa Falasdinawa damar zama mamba na iya janyo tashin hankali bayan hare-haren Hamas na 7 ga watan Oktoba.
Kasashen da ke son ci gaba da kyakkyawar mua'amala da Isra'ila za su san da cewar amincewa da kafa ƙasar Falasdinawa zai iya fusata kawayensu.
Wasu, ciki har da masu goyon bayan Isra'ila sun ce Falasdinawa ba su cika ka'idojin samun kasa ba kamar yadda yake a yarjejeniyar Montevideo ta 1933.
Mene ne matsayin yankunan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya?

Asalin hoton, SHAHZAIB AKBER/EPA-EFE/REX/Shutterstock
Falasdinawa na rike da matsayin yan kallo wadda ma mamba ba a Majalisar Dinkin Duniya, kamar cocin katolika.
A 2011, Falasdinu ta gabatar da bukatarta ta neman zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya sai dai bukatar ba ta samu shiga ba saboda rashin samun goyon baya a kwamktin tsaro na Majalisar, ba a ma kai ga kada kuri'a ba.
A 2012, zauren Majalisar ya kada kuri'a na daga matsayin Falasdinawa zuwa yan kallo wanda zai ba su damar shiga muhawara a zauren duk da cewa ba za su iya kada kuri'a ba kan batutuwa.
Matakin 2012 - wanda ya samu goyon baya a Gabar Yamma da Kogin Jordan da yankin Gaza amma ya fuskanci caccaka daga Amurka da Isra'ila - shi ma ya bai wa Falasdinawa damar shiga kungiyoyin kasa da kasa ciki har da kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya, kotun duniya da suka shiga a 2015.
A Mayun 2024, zauren Majalisar Dinkin Duniyar ya inganta hakkokin Falasdinawa da ke cikin kungiyar inda ya yi kira da a amince da Falasdinu a matsayin mamba sakamakon zazzafar muharawar da aka tafka.
Matakin ya bai wa Falasdinu damar shiga muhawara da gabatar da bukatu da kuma samun wakilci a zababbun kwamatoci amma ba ta da ikon kada kuri'a.
Kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ne kadai ke da ikon bayar da damar zama mamba.
A Afrilun wannan shekarar, Amurka, a matsayin daya daga cikin kasa biyar cikakkun mambobi, ta hau kujerar naki game da kudirin da Aljeriya ke goyon baya na neman a mayar da Falasdinu ta zama kasa inda ta kira matakin a matsayin ya yi wuri.
"Zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya zai bai wa Falasdinawa dama ta diflomasiyya har da ikon daukar nauyin kudurori da yin zabe a zauren majalisar sannan daga bisani ta samu yiwuwar samun kujera ko kuri'a a kwamitin tsaro," in ji Khaled Elgindy, daraktan shirye-shirye kan al'amuran Falasdinu da Isra'ila a cibiyar nazari ta Gabas ta Tsakiya da ke Wshington.
"Sai dai babu guda cikin wadannan da zai haifar da samar da kasa biyu a matsayin maslaha - abin da kawai zai iya faruwa a karshen mamayar Isra'ila," ya kara da cewa.
Sai dai Gilbert Achcar, farfesa kan nazarin ci gaba da hulda tsakanin kasashe a makarantar School of Oriental and African Studies in London na ganin hukumar Falasdinawa ba za ta karu da abubuwa ba idan ta zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya.






