Jefa wa al'ummar Gaza abinci ta jiragen sama ya janyo cece ku ce

Asalin hoton, Reuters
A daidai lokacin da ƙasashen duniya ke tofa albarkacin bakinsu kan rashin abinci a Gaza, Isra'ila ta fara aika kayan agaji zuwa zirin a ƙarshen makon jiya, tare da haɗin gwiwar Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Sai dai matakin ya bar baya da ƙura, inda hukumomin agaji na duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya suka ce salon da aka ɗauka na jefa kayan agajin ta sama ya fi tsada, sannan ba zai zama daidai da shigar da kayan agajin ta ƙasa ba.
An fara jefa kayan agajin ta sama ne bayan gargaɗin cewa zirin na fama da matsananciyar yunwa. Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce aƙalla mutum 14 ne suka rasu a cikin kwana ɗaya saboda yunwa.
An sanar da rasuwar ne a daidai lokacin da Isra'ila ta ɗan tsagaita da kai hare-hare a Gaza, inda ta ce kullum za ta riƙa bayar da awa 10 daga ranar Lahadi domin a riƙa shigar da kayan agaji.
Sama da tireloli 120 ne na kayan agaji daga Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙungiyoyin agaji ne suka isa zirin, kamar yadda hukumomin Isra'ila suka bayyana.
'Ga tsada, ga rashin isarwa'

Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta jefa aƙalla ɗauri huɗu na fulawa da sukari a Gaza. Jordan da Haɗaɗɗiyar Larabawa ne suka bayar da tan 25 na abincin agajin da sauran kayan buƙata.
A ranar Litinin, ƙasashen Larabawan biyu sun fara tattaunawa game da jefa abincin ta sama. BBC ta samu shiga cikin wani jirgin da ya jefa abincin daga Jordan.
An fara amfani da salon jefa abincin agaji ta sama ne a Yaƙin Duniya II domin aika wa dakaru abinci, amma yanzu salon ya ƙara samun karɓuwa wajen isar da kayan agaji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara amfani da salon ne domin kai kayan agaji a shekarar 1973.
Amma ana ganin salon ne a matsayin "zaɓi na ƙarshe" idan babu wata hanyar da za a bi wajen kai kayan agajin, kamar yadda shirin samar da abinci na duniya World Food Programme (WFP) ya bayyana a shekarar 2021.
A wani rubutu a shafin X, jagoran ayyukan agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza Unrwa, Philippe Lazzarini ya ce amfani da salon jefa kayan agaji ta sama "yana da tsada, kuma ba ya isarwa, sannan kayayyakin za su iya kashe fararen hula idan aka samu tangarɗa."
Ya yi kira ga Isra'ila da ta ɗage takunkumin hana shigar da kayan agaji zuwa zirin maimakon wannan salon na shigar da kayan agaji.
Ciarán Donnelly na cibiyar aikin ceto ta International Rescue Committee ya ce jefa kayan agaji ta sama ba zai taɓa wadatarwa ba.
Wani jami'in Jordan ya shaida wa Reuters cewa jefa kayan agaji ta sama ba zai taɓa maye gurbin na ƙasa ba.
A irin salon, jirgin C-130 ya isar da abinci kimanin kwano 12,500 a duk tafiya ne. Ke nan a irin haka, ana buƙatar aƙalla jirage guda 160 kafin kowane mutum daga cikin mutane miliyan biyu na zirin ya samu abincin kwano ɗaya a rana, kamar yadda wakilin BBC Joe Inwood, ya ƙididdige.
Wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abualouf — wanda ke aiko rahoto daga Istanbul — ya ce jefa kayan agajin ya haifar da turmutsutsu.
Wani ɗanjarida a Gaza, Imad Kudaya, ya bayyana wa BBC cewa wasu kayan agajin sun faɗa ne a wurare masu haɗarin gaske, inda ba za a iya zuwa a ɗauko ba.
'Abin da aka fi buƙata'

Asalin hoton, Reuters
Kakakin Unrwa, Juliette Touma ta ce ba zai yiwu a shigar tare da raba kayan agaji a zirin ba, ba tare da sa hannunsu ba, sannan ta soki salon jefa wa mutanen zirin abinci ta sama.
WFP ma ta ce akwai buƙatar kayan agajin da ake turawa su isa ga waɗanda suka fi buƙata ne ba tare da jinkiri ba.
Ƙungiyar likitoci ta MSF ta yi gargaɗin cewa ɗan tsagaita wuta na wani ɗan lokaci a jefa abinci ta sama ba zai magance komai ba.
Ta ce kamata ya yi a rubuta suna, sannan a tsara rabon kayan agajin cikin tsanaki.
'Babu matsananciyar yunwa'

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ba ta da burin kisan mummuƙe ta hanyar yunwa, inda ya ce zargin da ake mata batu ne na ƙanzon kurege.
Ya ce Isra'ila ta bayar da dama "a shigar da kayan agaji kamar yadda dokokin duniya suka tanada," sannan ya ƙara da cewa Hamas "ne ke sace kayan agajin, sannan sai ta zargi Isra'ila da hana shigar da kayan."
Sai dai Hamas ɗin ta musanta zargin yin sama ta faɗi da kayan agajin.











